Ranar Juma'a Bashir ya dawo Gombe kuma ranar aka sallamo baby Iman, Bashir da kansa ya dakkota bayan da ya dawo dan daman shi ya hana likitan sallamar su akan se yadawo saboda matsawar da Addah tai masa akan zancen shagalin suna.
Amiran bata daddara ba washe garin randa sukayi maganar seda ta sake kira ya kuwa yi mata tatas dan dama sunyi waya da Dada ta gaya masa yanda suka kwashe da Addahn dan haka ya qara tabbatar mata da wallahi ko sisin sa baze bayar ayi wani suna ba idan bata gode rai da lafiyar da Allah ya basu ita da yar ba ta godewa Azabarsa. Ai kuwa itama Addah batayi sanya ba ta karbe waya ta masa wankan tsaf ta kuma sake tabbatar masa fa taron sun ba fashi.
Shekara da shekaru tana rabar da kudin Barka da biki, haka auran Amiran kaman na munafukai basu barta tayi shagali ba yanzu ma a haifar mata jika suce Aa, to kuwa bazata sabu ba shidai ya mata shiru harta qaraci kumfar bakinta ta kashe ya kuwa rangadawa Amirah text din gargadi tunda ga ranar ma be sake kiranta ba idan ma ta kirashi baya dauka se yau Juma'a daya dawo garin suka hadu.
Yaso ma da ya tafi ya karbo yarinyar shi kadai sedai kuma ya tuna Amiran na buqatar a karanta mata yanda zata kula da yarinyar yasa yace ta shirya su tafi se gata ita da Hajia Addah aka shige mota.
Sau goma suka hada ido da Addah se sun jefi juna da harara ita da Bashir can dai da abin ya isheta tace "Bani kake harara ba Bashir Uwarka Nafi da Amadu su kake harara mara mutunchin kawai, kuma duk baqin cikinka suna ne se munyi se dai kayi bindiga ka mutu".
Kici kanki be ce mata ba har suka je Asibitin, sosai likita yaja kunnensu akan kula da Iman, Banda wanka a tsundumata a ruwa, suna tsaye ya saka Nurse ta kwatanta musu yanda za'a ringa wanke mata jikin shima ba kullum ba musamman yanayin garin sanyi ya kankama.
Sannan ya dora musu da bayanin in so samu ne mamanta kadai zata ringa daukarta kar a jagwalgwalata su tabbatar kuma ko yaushe tana cikin dumi kar ake fitar da ita cikin iska ko sanyi a kula da kayan da za'a ringa saka mata kuma.
Sallama sukayi suka tafi bayan ya basu ranar da zasu dawo ganin likita.Bashir be yadda ma an dauke ta a hannu ba cikin Baby carrier daya siyo tundaga lagos ya sakata ya dauka Addah ta hau salati da salallami wai ya saka ya a kwando to duk bala'in sa dai ko mayu ne su se ya basu yar in sunje gida tunda ba da ita ze ringa yawo ba,
shida be tankata ba. Seda ya ajiyeta dakyau ya maqala belt din ko ina sannan ya shige ya tada mota har sukaje gida kuwa Addah bata saduda ba se sababi takeyi.
A gidan ma suna zuwa da kansa ya bata feeder ta fara sha dan bottle feeding suke yi kafin ya bawa Amirah taci gaba da bata yana tsaye, seda ya tabbatar tasha yanda ya kamata ya dagata kamar kwan da baya so ya fashe ya sakata a kafada tayi gyatsa kafin ya kwantar da ita a dan gadonta. Seda ya dauketa hoto a wayar sa sannan ya juya.
Kallo daya yayiwa Amirah dake doka uban Murmushi saboda ganin irin tattali da kulawar da yake nunawa yarinyar, ta san yanzu ko Albarkacin Iman seta qara matsayi a zuciyarsa shi kuwa gogan tsaki ya buga ya fice daga dakin dan haushinta yake ji.
Yana fita Addah da jama'arta suka duru daki ganin Baby, kamar me tattaro kaya ta zura hannu zata cukumota Amirah kuwa tayi caraf ta riqe tana cewa "Haba Addah bakiji me likita yace bane shine zaki kawo mata wannan cafkar ai seki ballata".
Suka kwashi salati ita da jama'arta kafin ta fara masifa tana cewa "Eh lallai yanzu na yarda ba iya Bashir ne tanbadaddenba harda ke, yo in banda tanbada ni uwarki zaki hana na dauketa har ni zaki gayawa kar a karya miki ya, to da ban haihu ba yau se nayi kuka kiji da jinki seda na haifi Goma na binne takwas gaku nan biyu a raye harke ma kinyi yar kanki zaki nunamun sanabe da iyayi".
Inna Gaji ce ta ceci Amirah tace "Ba haka bane Fattu yanzu dai barta mu kalla daga haka dan Allah abunda in muna da tsahon rai watarana da qafarta zata taka ta hau jikin duk wanda take so" haka aka lallaba Addah kowa ya leqa yarinya dake baccinta masha Allah kyakykyawa da ita kowa se yace ta kwaso kaman nin yayan Ma'u.
YOU ARE READING
WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)
RomanceLabarin Soyayya, Sadaukarwa, Yaudara, Tuggu da Makirci.