Se bayan dana kai yaran na dawo sannan na kunna wayata, kiran Dada ne ya fara shigowa na daga na gaishe ta daga yanda ta amsa nasan labari ya isarmata kenan.
"Akan me zaki kori Amirah daga gidan Bashir Ma'u" ta fada bayan da muka gaisa.
Lallai wato gidan Bashir tana gaya mun ba gidana bane kenan, murmushi nayi, babu kunya tiryan tiryan na karanta mata abinda ya faru da duk abinda Amiran ta fada mun dama sauran abubuwan da takeyi a cikin gidantsaf seda na tsara mata.
Seda tayi jum da na tabbatar na kunya ne kafin tace "To ai koma menene be kamata ki koreta ba haka da se kija mata kunne ko ki kawo mana qararta mu se mu tsawatar mata, yanzu dai se kuyi haquri ta dawo kuci gaba da zama Allah ya kiyaye gaba".
"Wallahi Dada bazan sake zama da Amirah a gidan nan ba, ta koma gidansu idan auranta ya tashi bazan fasa yi mata duk abinda idan a hannuna take zanyi ba amma fa ba dai gidan nan ba" na fada kai tsaye dan ganin ana nema ayi mun fin qarfi, ita bataga illar abinda tayi ba kenan har ake cewa nayi haquri ta dawo to kuwa baze sabu ba.
Muna gama waya na kira Bashir na kora masa jawabi dan tun a jiya da daren nake ta neman wayar sa ban samu ba se text message na bar masa. Yanzun kuwa yana amsawa na kora masa abinda yasa nace ta tafin, zuwan Addah harma da wayar da mukayi da Dada.
"Wallahi bazan sake zama da yarinyar nan ba kama gaya musu"
"Daman ai ke kika gayyato ta gidan tun farko ai ni meye nawa a ciki?" Bashir ya fada.
Bansan dai ya suka qarke ba a batun Amirah kwanaki kadan tsakani ya tayar da maganar komawar mu Lagos dan ya samu gida babba da ze wadace mu. Nayi zaton za'a samu matsala dasu Dada saboda kes din Amiraj da mukayi amma se naji shiru haka muka fara shirye shiryen dan a lokacin ana Third term ne har yara sun fara shirin jarabawa, daga sun gama zamu tafi se a saka su sabuwar makaranta su koma sabon session.
Lokacin da zamu tafi gida gida nabi duk nayiwa kowa Sallama har gidan Addah naje muka rabu faran faran tana cewa se sunzo dan tana son zuwa Lagos in muka nutsu zata zo tayi mana sati har bakin ruwa se an kaita nace Allah ya nuna mana lokacin ta hada mana tsarabar kayan qamshi da su daddawa harda man Shanu ga dambun nama da tayiwa Jafar dan shine mutumin ta.
Haka muka tattara muka koma Ikko, gidan da Bashir ya samu babban gida ne me kyau yana cikin rukunin gidajen manyan ma'aikatan su.
Flat ne me dauke da manyan dakuna guda biyu se madaidaita suma biyu ko wanne kuma da Bandaki a cikin sa, ga qaton palour da Gurin Dining, Kitchen, store sannan ta bayan gidan da akwai babban fili da akayiwa shuke shuke daga gefe akayi garden.Gida dai masha Allah kuma Bashir ya saka komai na buqata a ciki. Se da nayi dagaske kafin na iya daure kewar gida na saba da garin, dan ma nayi sa'ar maqociya wadda take matar Ogan Bashir ce Anty Halima mutuniyar kirki, ita ta qara wayar mun kai da zaman Lagos na gane kan kasuwa ya zaman ina sarar kaya na turo dasu ko ina kake so a fadin Nigeria.
Kamar wasa naga tallan daukar ma'aikata na wani kamfani da suke hadahadar ma'adanan qasa anan Lagos, a lokacin na cewa Bashir zan cike ya kuma bani goyon baya na nemi aiki cikin ikon Allah se kuwa na samu suka daukeni matsayin meyi musu tallace tallace.
Na kama aiki ba dadewa wata rana kwasam muka samu baquncin Addah, Dada harda Amirah. Sosai mukaji dadin zuwan su dan baka gane dadin gida se randa kayi nesa da yan uwanka kwanan su hudu Addah da Dada suka juya aka bar Amirah da alokacin wai an saka ranar auranta da wani yaro Bashir shima sunansa dan Abokin babban su Bayan sallahr Azumi da sati daya.
Dalilin kawota kuwa saboda acewarsu na koya mata yan abubuwan da ya kamata ta iya, nayi dariya kuwa nace duk abinda bata koya ba a zaman kusan shekara goma da mukayi tare banajin zata iyashi a watanni biyu kacal, haka dai suka tafi suka barmu na kuwa dage tsakani na da Allah ina dora yarinyar nan akan hanya ta hanyar nusar da ita komai.
ESTÁS LEYENDO
WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)
RomanceLabarin Soyayya, Sadaukarwa, Yaudara, Tuggu da Makirci.