A bangaren Hajia Balaraba kuwa cike da farin ciki ta bude gida ta shiga ganin har sannan Kishiyarta bata dawo daga gurin aiki ba, cikin sauri ta fito da rubutu ta huda leda tareda guntsa ta feshe kofar dakin Amarya tana cewa "Shegiya maza ki dawo ki taka ni Alhaji yaiyo waya daga kasuwar ma yace ya sake ki base ya jira ya dawo ba" ta qulle ragowar gudun kar ya zube ta qarasa qofar ta.
Mayafinta kadai ta ajiye ta shiga kitchen ta hau kicikicin dora girki qarin farin cikinta ita ce da girki dama kai yau koda ba itace da girki ba ai dole tasan yanda za'ayi ta aiwatar da aikin nan tanayi tana tuna irin cin mitunchin da Alhaji yai mata dazu da safe kafin ya fita kuma ta tabbata duk Amarya ce ta zugoshi har yana iqirarin tabar ganin sun tara yaya da jikoki tsaf seya yanka mata tikitin zawarci.
Itadai tunda Malam na kan Tudu ya kwanta dama kamar ya tafi da duk ayyukan da Tayi akan Alhaji ne komai ya karye shekara da shekaru tana cin duniyarta da tsinke se yanzu da tsufa ya kusa cin mata ne zata fara karbar taskun namiji ina bazeyuwu ba ai.
Tsaf ta gama hada lafiyayyar Miyar taushenta kafin ta dakko qaramar tukunya ta sare wata wadda zata ci, nan da nan dakko ragowar rubutun Malam Wizy ta kurbe tas ta kuskuro dattin bakinta da komai ta watsa musu a miya ta sake kurbe ragowar ta zuba ta juyata dakyau ta rage wuta ranta fes dan gani take kamar ma aikin gama ya gama.
Tana cikin malmala tuwan autarta me suna Ruqayya ta shigo ta dawo daga makaranta dan tana shekarar ta ta qarshe ne a GSU da mamaki ta kalli maman tata kafin tace "Hajia kece dakanki yau a kitchen ina Baba Zulai din"
Bata ko dago ta kalleta ba tace "Taje gida Sa'adenta batada lafiya ina ga se gobe zata dawo"
"Kai dukda haka da mamaki ace Hajia kina girki lallai yau zamu kwashi dabge bari nayi sauri nayi wanka nayi Sallah muzo mu kwashi ganima"
"Zaki kwashi ganima dan uwarki duk zan kulle bakinku ai na ga ta inda zaki ringa kaiwa uban naki gulma idan na taba kudinsa" ta fada bayan Ruqayyan ta fita daga kitchen din
Oho bata ma san tanayi ba dakin ta ta nufa a ranta tana ayyana tabbas akwai wata a qasa dan ita dai tafi shekara Goma rabonda taga Hajia tayi girki da kanta Baba Zulai ce take yi musu ko kuma ita idan taba gida. Ita zata iya cewa ma idan kaga Hajia a kitchen to an gama Abinci ne idan harda na Baban zatayi barbade daga baya ma daya gane yai Allah ya isa yama zo kuma ya dena cin abincin kwatakwata se baya bayan nan taga ya dawo yana ci.
Ita kuwa Hajia tana sauke tuwo ruwan Tea ta mayar ta saka lipton dinta da kayan qanshi sannan ta zuba jiqon Wizy, bata matsa ko ina ba seda ta kammala tsaf ta hada komai ta kai kan Dining sannan tashi ga dakinta tai wanka ta fara jero Qara'in salloli.
Seda akayi Isha Alhaji ya shigo, kai tsaye part din Amarya ya shiga dan akwai kayan daya manta da safe da ze tafi kasuwa yana so ya dauka kar gobe ya sake mantawa. da mamaki ya kalleta dan ya zata ta tafi aiki tunda tace masa Night Duty ne da ita. tana ganinsa ta miqe"Yawwa Alhaji dama kai nake jira tun dazu"
"Lafiya Abida baki tafi aikin ba? Jiran me kike mun?" Ya fada yana kallonta. Seta miqa masa wayarta kawai ba tareda tace komai ba, karba yayi yana duba screen din sega video Hajia Balaraba tana kici kicin zuge jaka, baya jin me take cewa amma fes yaga sanda ta ciro leda ta guntsi rubutun ta feshe kofar dakin Amarya ta tafi"
Se ya miqa mata wayar dason jin qarin bayani."Wallahi Alhaji yanda ka gani dinnan kasan ka fita ka barni kaina yana ciwo dan haka sena kwanta dan ban ma samu zuwa Barkar Haula da nace maka zan fita ba, se bayan La'asar na ma idar da sallah na tashi zan leqa na karbo Kati se naji motsin a bude qofa, in duba ta window fa shine naga Maman Suhaila na wannan ta tsaya tana maganganu tareda bude jaka wayata na hannuna ni kuma shine na kunna video saboda kar a maimaita irin ta wancan karan data zuba magani akace qarya nakeyi yanzu dai ga Hujja ka gani da idonka, nidai ban fita ba koma na menene kai kadai ka tsallaka shi se kasan yanda zaayi azo a karya dan bazan yi ta zama a daki ba kona fita a sabautani a banza".
BINABASA MO ANG
WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)
RomanceLabarin Soyayya, Sadaukarwa, Yaudara, Tuggu da Makirci.