Asma'u
Alhamdulillah shine abinda zance dan yanda komai yake tafiyar mun lafiya lau ba tareda wata matsala ba. Dukda aikina na office ya dan qaru dan yanzu har tafiye tafiye zuwa sauran states na Nigeria nake yi amma saboda goyon baya dana samu daga Bashir se abin yazo mun da sauqi musamman da tafiyar tawa bata wuce kwana daya a mun dade ne mu kwana biyu.Tuni Amna sun gama sun gama SSCE tana zaune a gida se jiran sakamako kuma abinda ya qara sauqaqamun abubuwa kenan dan kona dade a waje bani da tunanin na dawo gida na tarar da wani aiki.
Baban Ali da Amaryarsa kuwa se sam barka dan naga wani shiri sukeyi yanzu bini bini yana hanya an tafi Gombe, ina yawan kama shi yana waya da daddare dukda yanzu ya denayi a daki sedai ya fita ko kuma naga Text dinta idan ta turo har mamaki da dariya abin ya ke bani na tabbatar wannan ba dabarar ta bace ta samu wani da yake dorata a hanya ne.
Ni kuwa sosai hakan yayi mun dadi ko babu komai hankalin na ya kwanta yanzu ne zamuyi kishi na hankali kowa ta iya Allonta ta wanke dan haka bana wasa babu daga qafa idan ya tafi kafin ya dawo nayiwa kaina Gyara gangariya yanda zan kwance masa kai na shafe duk wani gigi daya taho dashi.
Sannu sannu rayuwa na shudawa kusan wata biyar kenan rabon mu da Gombe, tuni akayiwa Yara register da School Bus zata dauke su ta dawo dasu abinda ya sake sauqaqamun zirga zirga ma kenan tunda idan Bashir ya kaisu ni nake dawo wa dasu toh yanzu kuwa suna rigani dawowa ma tunda daman kullum se sunyi jira bayan an tashi kafin a dauko su.
Jikin Goggon mu ne ya sake tashi da har seda aka kawo ta nan Lagos Asibiti wanda Alhaji Qarami Babban Yayan mu ne ya dauki nauyi dukda yanda muka so ya barmu muyi amma yaqi harya nuna bacin ransa akan mun banbanta tsakani kenan.
Satin ta hudu a Lagos shima dakyar dan kwananta uku a Asibitin aka sallameta amma zata ci gaba da zuwa ganin likita na tsahon sati hudu dakyar da ban baki ta yarda zata zauna a gida na wai ita bazata je godai godai ta zaunawa siriki a gida ba seda Bashir din yasa baki sannan fa ai kuwa ranar zuwanta na qarshe washe gari ta koma Yola tareda Amnah da Faridah zasu yi kwana biyu dan su Faridan sunyi hutun Term.
Tafiyarsu da kwana biyu Bashir ya tsiromun da wani sabon hali, a da duk dadewa baya wuce sallar Magriba a waje shima se ta qure kenan ko da zeje wani guri seya dawo gidan dai ya shirya sannan ya tafi amma a kwanakin nan se ya kai Tara Goma be shigo gida ba.
Ranar farko qarfe Tara ya dawo a gajiye na tare shi, seda yayi wanka na kai masa abinci yana ci nake cewa "yau kayi dare Baban Ali ina ta kiran wayar ka kuma bata shiga ba".
"Eh aiki ne yayi mun yawa shiyasa na tsaya na dan rage wasu abubuwan" ya fada yana ci gaba da cin abincinsa. Har ga Allah na yarda saboda ya samu qarin girma kwananan dan haka nasan ayyukan zasu fi nada dalilin daya saka washe gari ma daya kai goma ban damu ba da yake ma ina dan fama da ciwon kai ka fin ya shigo nayi bacci seda Asuba Aliyu ya ke cemin jiya se 10 Abbi ya dawo.
Abinda ya fara jan hankalina da dadewar tasa yanda abin ya zamar masa jiki dan seda ya jera kwana hudu kullum kuma a maimakon ya rage lokaci qarawa yakeyi, a ranar na hudun data kama Asabar, tun Daya na rana yayi wanka ya fice wai zeje gurin Musa abokinsa akwai wani aiki da sukeyi tare beyi awa biyu da fita ba nayi baquwa.
Maman Shukra maqociyar muce a Estate din da muka fara zama kafin mu dawo nan rabon da mu hadu har na manta ma ina zaune se gata.
Bayan na gabatar mata da kayan ciye ciye na zauna ina sake yi mata sannu da zuwa. Yanda take kallona tunda ta shigo ya tabbatar mun bakinta akwai magana dan Maman Shukra akwai gulma sedai na tabbatar da bata qarya, duk labarin data fada maka to kodai ba gaba daya bane idan kabi diddigi seka gano gaskiyar.
Kallonta nayi da yar dariya nace "Maman Shukra wace jarida muka samu dan tunda kika shigo naga bakin nan naki yana motsi".
Seda ta kora ruwa me sanyi kafin ta kalleni tace Maman Farida Engineer yana gida kuwa?"
YOU ARE READING
WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)
RomanceLabarin Soyayya, Sadaukarwa, Yaudara, Tuggu da Makirci.