Washe Gari Asabar tunda nayi sallar Asuba na koma bacci ban farka ba se goma na safe. Ko yaya Bashir ya qare jiya oho dan tunda na gaya masa babu abinci naji ya fara jan kwafa da tsaki na kwashi qafafuna na bar musu gurin, dan karma a biyo ni a dameni seda na murzawa qofata key sannan na kwanta.
Tsaf na shirya cikin wani Material baqi doguwar riga bayan nayi wanka, tundaga dakin nake jiyo kaya kaya alamar Game suke ko ana musu akan wani abun ina bude qofata Yan biyu na suka taso da gudu suka riqe ni.
"Kai ni yunwa nake ji karku kadani me kuka ci ne" na fada ina kama hannayensu, se Ahmad yace "Indomie Yah Amna tayi mana da Tea Abbi kuma gashi can yanzu aka soya masa Irish".
Kallon inda yake nuna mun nayi muka hada ido da Bashir daya watso mun wata harara kamar idonsa ze fado, duk yanda naso na basar seda dariya ta kufce mun dan haka na wayance ina nufar inda yake nace "Baban Ali barka da safiya, kace kaima yanzu ka tashi? Bari nazo muci dan Allah yunwa nake ji idan bamu qoshi ba se a qaro wani" nayi maganar ina jan kujerar da take kallonsa na zauna.
Ban damu da shirun daya mun ba na fara hada Tea na ina masa surutun da na tabbatar sake qular dashi nakeyi, na gama naja kwanon dankalin, sena bude baki ina kallonsa nace
"Kai Duk wannan da kai kadai zaka cinye shi?"
Can qasa kaman an fuzgo maganar daga bakinsa naji yace "Banci abinci da daddare ba jiya da yunwa na tashi".Kallonsa nayi, naji tausayinsa kadan dan nasan Bashir da abinci ci ne dashi kamar dan kwallo, cikin jimamai nace "Ayya meyasa ka kwanta da yunwa da ka saka Amna ko Spaghetti ce ta dafa maka ai".
Shiru ya sake yi mun, nima ban sake magana ba na fara cin abinci na, ya rigani gamawa, seya miqe ya shiga dakinsa ba dadewa ya fito ya chanza kaya ya saka Caftan na Yadi kansa babu hula. Key din motarsa ya dauka, be mun magana ba ya fice yara suna masa a dawo lafiya.
Harya tada motar se gashi ya shigo, ko me ya tuna oho se ji nayi yana cewa "zan fita amma ba jimawa zanyi ba saura yauma karku ajiye mun lunch".
"Wa ya isa yaqi ajiye maka, jiyan ma aka si aka samu baka ce zaka dawo ba, amma yanzu tunda munsan kana nan ai zamu girka da kai" na fada ina dan murmushi. A raina nace "da bakayi magana ba wallahi yau ma dakaga Akuya sedai ka siyo ko kayi wunin yunwa.
Jellop rice nayi da pepper soup din tarwada, sena yiwa Bashir pepper meat dan baya cin Tarwada shi se gasashshiya.
Muna cikin yin lunch Amna ta kalleni tace "Mami idan mun gama muje gidan Baba?"
"Za kuje ku dame su ko kunsan dai yau Weekend Baba yana nan zaku hana shi hutawa".
Bashir ne yace "Baya nan Ya tafi Zamfara tun jiya, idan kun gama kuje dama yau baza mu fita ba sedai ko gobe".
Muna gama cin abincin kuwa bayan sun tattare kwanukan suka tafi ita da Farida dasu Ahmad, Aliyu da sauran kuwa Ball suka dauka suka tafi Filin da suke bugawa gidan ya rage daga ni se Bashir.
Qin zama nayi na shiga qaqale qaqalen ayyuka dukda na fahimci nufin Bashir, ganin da yayi bani da niyyar saurar sa, ina tsaye ina goge show glass din farantai a Gurin Dining kawai naji anyi sama dani, duk yanda naso nayi tawaye a dole fushi nake amma yaqi bani dama, daman abin be kai zuci ba kuma nima nayi kewar sa nan da nan nima na bada kai bori ya hau sosai kuwa na gigita Bashir.
Ina zaune a gaban mirrow ina Busar da kaina bayan nayi wanka ya shigo dakin yana waya, ta cikin mudubin muka kalli juna murmushi me kyau da narkar da zuciya ya sakar mun kafin ya qaraso ta bayana yana taba Gashina yaci gaba da maganar sa be jima ba ya kammala seya ajiye wayar akan mirrow ya karbi Dryer yana cewa "Dama baki wahalar da kanki ba dan ba'a gama ba"
YOU ARE READING
WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)
RomanceLabarin Soyayya, Sadaukarwa, Yaudara, Tuggu da Makirci.