Part 57

2K 216 47
                                    

BASHIR
Iya bakin qoqarinsa yakeyi gurin aiwatar da abinda Musa ya gaya masa, duk yanda yasan ze shawo kan Ma'u yi yake amma kamar wadda yake qarawa wuta fetur daman baya samun ta a waya duk ubannin saqonnin da yake tura mata kuwa bata taba maido masa da ko guda daya ba.

Ya rasata ina ze sameta suyi maganata fahimta, baya son zuwa gidan ta tunda tace masa bata so amma dole ya zama me gadin qarfi da yaji, da wuri yanzu yake baro office yazo kanlayi ya kasa ya tsare amma ko sun hadu ma wani shashasha take mayar dashi dan daga gaisuwa bata ma bashi damar magana zata wuce abinta.

Abun na bala'in ci masa tuwo a qwarya, ga azumi yana gaba towa baya so suyi azumi a wannan yanayin. Gidansa daman tuni yafi qarfin sa in har yana son nutsuwa to fa sedaiya fita waje dan karadi da surutun Addah kadai ya ishe shi. Shi bata barshi ba ita Amiran da take fama da kanta itama bata tsira ba ga jaye jayen magana da take dakko masa haka kawai seta wanke qafa ta shiga gidan maqota kuma in dai taje seta takalo wani abun haka za'ayi ta tararsa ana kawo qararta sedai yai ta aikin bada haquri.

Kusan sati ana wannan yanayi ranar yana zaune da daddare a dakinsa haka kawai zuciyarsa ta ayyana masa kiran Goggon su Ma'u.

"Nasan tana sona da Ma'u kuma ita kadai ce zata fahimceni a yanzu in Allah ya taimaka seta shawo mun kanta a sanyi komai ya daidaita" ya fada a fili yana janyo waya cike da kwarin guiwa ya shiga kiran Goggo.

Seda ta dan jima tana ringin kafin ta daga da sallamarta suka gaisa yanda suka saba yana tambayarta jikin Baffa tace da sauqi kafin itama ta tambayeshi su Amirah da yara yace duk suna lafiya se sukayi shiru gaba daya.

"Lafiya dai ko Bashir naji kayi shiru" Goggon ta katse masa shiru, seda ya hadiyi wani yawu kafin ya gyara zaman sa ya sunkuyar da kai kamar yana gabanta yace

"Daman Goggo kira nayi in bada haquri, wallahi nauyi da kunyarki ta saka tun lokacin da abin ya faru na kasa kiranki se yanzu dai na daure nace bari na kira".

"In banda abinka Bashir meye abin bada haquri kuma kamar wanda ya aikata wani laifi, shi zaman aure ai raine dashi idan lokacin mutuwar sa yayi kuma ba yanda aka iya ko da dalili ko babu haka ana so ba'a so za'a rabu, karka ji komai wallahi Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri a gare mu baki daya" Goggo ta fada a sake babu damuwar komai tattare da ita.

Cike da qarfin guiwa Bashir ya shafa kai yace
"Hakane wallahi duk abinda ma ya faru Goggo laifi na ne kuma dai sharrin shaidan ne amma yanzu na gane kuskurena kuma in Allah ya yarda haka bazata sake faruwa ba"

"Ai ita rayuwa daman haquri akeyi amma babu komai ai koma dai laifin waye a cikin ku Ai abubya wuce Allah yayi wa kowa zabin Alkahiri a gaba"

"Ai Goggo Alkahiri dai yana nan tare damu dan in sha Allah zamu koma kuma babu abinda ze sake faruwa a gaba se Alkahiri, badan ma wancan tsautsayin daya faru ba ai da yanzu ma ta dawo dakinta qila tana shirin haihuwa koma ta haihu amma yanzun ma muna saka rai in Allah ya yarda kafin Azumi komai ze daidaita." Bashir ya sake fada da qarfin guiwa.

"Toh haka da sauri har kun daidaita kenan?" Goggo ta tambaya cikin mamaki, se ya shafa kai kamar yana gabanta yace

"Aa dai tukunna, kinsan mutuniyar ne akwai rikici itama wani lokacin to har yanzu dai inata ban baki ne amma taqi ta bani dama amma nasan dai in aka ci gaba zata haqura shi yasa ma na kira yanzu ko za'a dan taimaka a saka baki tunda tana jin maganar ku qila tafi saurin sakkowa".

Seda Goggo taja ajiyar zuciya tana jinjina qarfin halin Bashir kafin ta iya ce masa

"Eh to ai duk da na gari da yake so yaga daidai dole yaji maganar iyayensa. Zancen mu saka baki kuma ai bata taso ba Bashir dan a yanzu Addini da kansa ya bata damar zabar abinda take so dan ta wuce Budurwa bare ace za'a fada mata yanda zatayi.

WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin