1

489 17 5
                                    

*AMARYAR ZAYYAD*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 1

*Ƙagaggen labari ne, in kinga yayi iri ɗaya da labarinki ko wata 'yar uwarki to arashi ne, amma banyi ko dan kowa ba sai dan in isar da saƙo da faɗakarwa cikin nishaɗi.*

*Gargaɗi*
_Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin ko kuma satar fasaha, ko a mayar mini da shi Audio a ɗaura min shi a wata kafa na media ba tare da izini na ba, sannan ina gargaɗi ga masu cire sunana a cikin labarina su saka nasu tare da sakinsa a shafinsu, ban hanaku ɗaura labarina ba amma a barmin sunana tare da barin rubutuna yadda yake, da fatan za a kiyaye_

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

ZAINAB (Safna).

Tunda aurenta ya gabato ta samu kanta cikin yanayi na fargaba da tunanin abinda zai je ya dawo, samakon faruwar wasu al'amura a shekarun baya da suka gabata. A lokacin da aka saka ranar aurenta da Sadiq biki ya rage saura kwana goma Allah yayi masa rasuwa, Safna ta samu kanta cikin mawuyacin halin da ba zata iya misaltashi ba, da kyar aka samu kanta dalilin tsananta addu'a da mayar da lamuranta ga Allah, a haka har ta samu ta dawo dai dai ta dangana tare da karɓan ƙaddarar ta. Bayan wani lokaci ta kuma haɗuwa da Lukman tun tana ƙin bashi dama har ta sake masa suka fara soyayya, cikin ƙanƙanin lokaci suka shaƙu daga bisani kuma ya turo manyansa aka fara maganar aure, an kawo sadaki da komai na aure saka rana ya rage wanda iyayensa ne suka ce a basu lokaci su gama shiri kan a saka, kwatsam Lukman da kanshi yazo yace ya fasa aurenta sannan ya yace ya yafe komai da suka kawo, Safna a lokacin kamar zata yi hauka domin ta kamu da tsananin son Lukman fiye da yadda taso Sadiq, babban tashin hankalinta yadda yaƙi faɗar meye dalilin janyewarsa. Safna gata da kyau, ilimi, nasaba, natsuwa da tarbiyya bata da makusa amma kuma ƙaddararta yana ga aure, da kyar ta iya haƙuri da rashin Lukman wanda har hakan yaso jefata cikin wani hali, ta kusa kamuwa da ciwon zuciya, ga hawan jini ya yayi mata dirar mikiya da ƙanƙanin shekarunta, ga rashin barci da ciwon ulcer da yayi mata mummunar kamu saboda rashin cin abinci, haka suka dinga zaryar asibiti da kyar aka samu aka shawo kanta ta dangana, tun daga wannan lokacin ta haƙura da zancen soyayya bata kula kowa duk nacin mutum sai dai yayi haƙuri ya rabu da ita, gata da farin jinin samari amma haka ta shafe shawon shekara biyu bata saurarensu.

Wani lokaci da yayarta Anty Maryam ta haihuwa a taron sunanta, sai rikici ya ɓarke a tsakanin dangin mijinta da danginta wanda hakan ya jawo tashin hankali har aljanu suka dinga zubar da mata a ƙasa, ciki har da Safna ta zube numfashinta ya ɗauke tamkar babu rai, hankula sun tashi sosai dan kyar aka shawo kan matsalar, amma ita Safna sai da ta kwana biyu a sanƙare bata san inda kanta yake ba anata aikin ruƙiyya da hayaƙi, a hakane har aka samu aljanin yayi magana wanda ya tabbatar da shine ya ke haifar da matsala a maganar aurenta, duk da Sadiq lamarin yazo da ƙarar kwana, sannan ba wai ya auri Safna bane kawai bai yarda wani namiji ya raɓeta ba, da kyar aka samu ya tafi ta dawo hayyacinta, tunda aka fahimci ga inda matsalar ta take kuma itama ta fahimci lallai tana da matsala duba da yawan mafarkin ruwa ko tana tashi sama da mafarkin macizai ko tana faɗa da wasu halittu, tunda ta yiwa malamin da yayi mata ruƙiyya bayani yace In Sha Allah zata samu lafiya, ya bayar da magani wanda za ta soma amfani dasu. Alhamdulillahi wannan shine hanyar warakar matsalar Safnah dan an kwashe shekara biyu ana aikin magani kuma an samu nasara dan har Allah ya sa ta fara kula samari a lokacin shekarunta ashirin da huɗu a duniya, ganin suna niman su hanata sukuni yasa ta tsaida Zayyad a matsayin wanda zata aura duk da bata ƙaunar mai mata, amma soyayyarsa tayi mata dirar mikiya wanda ba zata iya haƙura dashi ba duba da shima yadda yake mugun ƙaunarta.

Ba zata mance haɗuwarsu ta farko ba lokacin taje shagonsa dake kan babban hanya tsakanin Gomna Road da kuma Badikko, taje siyo fulawa da kayan haɗin donot, da ta gama siyayyarta an saka mata a leda ta tsaya bakin shagon zata tare napep ta wuce gidansu dake ɓangaren Abakwa GRA, sai ga wani yaro ɗan makaranta akan keke yazo zai wuce, tsautsayi yasa shi raɓar gefenta saboda gosilon daya haɗu a gurin, nan ya fasa mata ledar fulawa ya fashe ya soma zuba a ƙasa, da azama Safna ta kamo rigar yaron wanda ya sashi dole ya tsaya, ta shiga yi masa masifa akan lallai sai ya biyata, yaron ya soma bata haƙuri amma taƙi saurarensa dan abin yayi matuƙar ƙona mata rai, haka mutane suka fara taruwa a gurin masu bata haƙuri nayi masu bawa yaro laifi suna yi, Zayyad dake shago yaji haniyar tayi yawa sai ya fito yana tambayar yaran shagonsa meke faruwa? suka sanar dashi sai ya ƙaraso inda su Safna suke ya shiga bata haƙuri yace shi zai biyata, ya amsa ledar ya bawa ɗaya daga cikin yaransa akan su sake yi mata awo, nan taro ya watse sannan Zayyad ya gargaɗi yaron akan ya riƙa kula da hanya yayi masa godiya ya tafi. Zayyad ya koma shago ya zauna yana hango Safna har aka gama zuba mata ta amsa ta wuce, wannan dalilin yasa tasan shine asalin mai shagon da take yawan siya kaya a gurinsu, shima kuma dalilin daya saka shi riƙe fuskarta kenan, da ta zo siyan abu yana jin muryanta yake ganewa zai fito ya tsaya har a sallameta ta wuce, a hankali ya fara jin wani abu yana ɗarsuwa a zuciyarsa game da ita, tun yana ƙaryata kansa har ya yarda da ya kamu da sonta, ita kuma tana yawan zuwa shagonsa ne tayi siyayyar kayan fulawa saboda sana'arta kenan harkan snacks, donot da samosa tafi yi dan ta iya sosai tana yin na taron suna ko biki ko wani sha'ani, bata yarda da zaman banza ba dan har a gida tana yin na sayarwa, in tayi da yawa takan ɗiba ta tafi dashi makarantar bokon da take koyarwa ta bayar a shagon makarantar ana saida mata, in ya ƙare a bata kuɗin shima mai shagon ya cire ribarsa. Wannan shine sanadin haɗuwarta da Zayyad wanda baiyi ƙasa a guiwa ba har sai da ya kafa gomnatinsa a zuciyarta ya samu gurbi, tun tana ƙi har saida ta amince masa har suka shafe shekara guda da watanni kafin aka saka lokacin bikinsu, gashi yanzu saura wata ɗaya a ɗaura auren. Kiran daya shigo wayar Safna shine ya dawo da ita daga duniyar tunani data shiga, ta sauke numfashi ta ɗaga kiran da sauri dan har ya kusa tsinkewa ta kara a kunne.

AMARYAR ZAYYADWhere stories live. Discover now