14

273 11 1
                                    

*AMARYAR ZAYYAD*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 14.

Suna isa asibiti suka zauna a reception suna jiran likita da aka ce yana ward round, tuni aka tura file ɗinsu zuwa system ɗin doctor. Bayan kamar minti goma sha biyar sai gashi likitan ya ƙaraso, yana ganin Zayyad ya isa gareshi shima ya miƙe cike da fara'a suka yi musabaha.

Alhaji Zayyad Barka da safiya, kai ne da iyalin duka waye ba lafiya.?

Amarya muka rako.

To madallah Bisimillah.

Likita ya ambata ya juya zuwa office ɗinsa, Zayyad ya kalli Safna yace mata su shiga sai Rashida ta miƙe da nufin binsu.

Maman Ilham ki jiramu mu fito.

Cewar Zayyad daya katse mata hanzarinta, ya rasa wannan wani irin binbini take yi musu ko wace mace tana buƙatar sirri amma yaga Rashida sam bata da wannan tunanin. Da suka shiga likita ya tambayi Safna meke damunta, sai ta faɗa masa daga nan ya ɗaura da tambayarta yadda take ji a jikinta harma da yaushe rabon data ga jinin al'adarta, duk ta faɗa masa dan bikinsu saura sati ɗaya tayi wanka kuma bata ƙara ganinsa ba dan har ta soma ɓace lissafi, likita yayi rubuce rubucensa kana ya miƙa musu wata takarda yace suje lab za a ɗiba jininta ayi gwaji da kuma fitsari, Zayyad ya amsa kana suka fito yana gaba Safna tana binsa a baya har suka isa lab, ba ɓata lokaci aka ɗiba jininta tare da bata wata ƙaramar roba akan taje tayi fitsari, suka nuna mata bayi ta shiga ba jimawa ta fito ta basu suka amsa tare da cewa suje su jira zasu kawo result office ɗin likita. Bayan sun dawo suka zauna zuna jiran sakamako, Safna hankalinta yana kan tv Rashida kuma tana ta danne danne a waya haka shima Zayyad. Bayan wani ɗan lokaci sai ga nurse tace su shiga ɗakin likira dan har an kawo result ɗin, suka miƙe suka shiga tare da zama suna fuskantar likita.

Alhaji Zayyad ina tayaka murna da samun ƙaruwa dan sakamako ya tabbatar da Amaryarka tana ɗauke da juna biyu, dan haka zuwa nan da sati biyu zaku dawo dan tabbatar da kwanaki nawa yake. Wannan ciwon kunnen alamu ne na laulayi yazo mata a haka, Allah ya raba lafiya.

Ameen nagode likita sai a ɗaurata akan magani dan samun sauƙin ciwon kunnen.

In Sha Allah gasu zan rubuta sai kuje gurin biyan Kudi ka biya sai ku amsa magungunan a pharmacy.

Zayyad yayi godiya sosai, Safna kuwa taji daɗi sai dai abin yazo mata a ba zata bata taɓa kawo ciki yanzu ba, balle babu wani laulayi kamar amai zazzaɓi kamar yadda sauran wasu mata ke yi. Bayan sun fito Zayyad yace su jirashi a mota ya wuce gurin biyan kudi, daya gama dasu ya amsa magani kana ya fito suka kama hanyar gida.

Bayan sun ƙaraso gida Rashida kamar abin arziki ta juya tana cewa Safna.

Allah ya ƙara sauƙi yasa kaffara ce, zaki iya ɗiga Zaitun a kunnen shima yana maganinsa sosai.

Ameen ya rabbi nagode maman Ilham In Sha Allah zan saka.

Malama ba abinda zaki saka tunda likita yace ciwon kunnen da akwai dalili, ga maganinki ki tabbatar kin karya kin shasu, ina zuwa.

Ya ambata tare da miƙa mata ledar maganin, Safna ta amsa ta wuce, shi kuma suka jera da Rashida tana cewa.

Ya zaka ce kar ta ɗiga bayan kaima kasan yana maganin ciwon kunne, ko ba kaine ka taɓa siyowa ba lokacin da Aslam yayi fama da shi kace Hajiya tace a saka masa.

Hakane amma ita fa laulayi ne yazo mata a haka.

Dumm Rashida taji akanta kamar an buga mata guduma, nan take taji wani gumi ya soma damunta amma haka ta shanye yanayin da take ciki ta ƙaƙalo murmushi.

AMARYAR ZAYYADWhere stories live. Discover now