*AMARYAR ZAYYAD*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 3
Safna ta aje tiren a gabansa kana ta zauna nesa kaɗan da shi tana cewa.
Amincin Allah ya tabbata a gareka Sirrin Zainab.
Ameen Wa Iyyaki. Ya mutanen gidan.
Alhamdulillah duk kalau suke.
Masha Allah! Amma kafin mu kai ga hira, ki fara gabatar mini da abinda kika tanadar mini cikina ya ɗauka tukuna.
Murmushi tayi wanda yasa kumatunta lotsawa dimple, tare da matsawa gabansa ta buɗe plate ɗin Samosa data soya shi ɗazun, Zayyad tun kafin tace masa gashi yayi saurin zura hannu a ciki ya ɗauka ya kai bakinsa ya fara ci, yana irin santin nan da mirgina kai dan yayi masa matuƙar daɗi, Safna dai murmushi kawai take zuba masa kana ta ɗauki kofi ɗaya ta shiga tsiyaya masa kunun madara, Zayyad ya yi saurin katse ta da cewa.
Meye wannan kuma ko yoghurt ne?
Sha dai kaji?
Ta faɗa tana miƙa masa, Zayyad ya amsa tare da kai kofin bakinsa ya kurɓa, wani irin garɗin daɗi ne ya shammaci maƙogoronsa bai san sanda ya kafa kofin a bakinsa ba ya shiga kwankwaɗa, sai da ya shanye kafin ya cire kofin yana sauke ajiyar zuciya mai ɗumi, ya kalli Safna cike da tsantsar ƙauna.
Allah yayi miki albarka, yadda kika faranta mini ubangiji ya faranta miki sannan ya cika miki burinki na mallakar Zayyad.
Wannan karan dariya ne ya kubce mata ta shiga yinsa a hankali sautin yana fita.
Ya baki ce Amin ba kina min dariya.
To ai gani nayi kamar sai an sanya maka waigi, wannan irin santi kamar ance maka ga Safna a cikin gidanka an baka halak malak.
To me ya rage nan da wasu 'yan kwanaki ƙalilan ne komai zai tabbata har abada. Amma batun gaskiya ko miye wannan abun ya mini zallar faɗi, na dai san an saka madara dan ƙamshinsa ke dukan hancina, amma me kyau ki faɗa mini me kika bani ne haka mai daɗi?
Wannan shi ake kira da kunun madara, kuma shi kasha.
Wow amma gaskiya ya kayatar da ni, ban taɓa shansa ba amma ki tabbatar in kinje gidana zaki cikani da salo salon girkinki Ruhieee.
Ya yi maganar yana jan ƙarshen tare da lumshe ido yana saka hannu a gefen zuciyarsa, sosai Safna ta saki dariya, nan dai suka cigaba da hirarsu gwanin sha'awa har misalin ƙarfe tara da rabi kafin suka yi sallama, amma fa saida Safna ta kakkaɓe masa duk wani damuwar da yazo dashi kafin suka rabu ya nufi gidansa cike da bege da ƙosawar son kasancewa da ita.
Ko da Zayyad ya isa gida ya tadda kayan kallo a kunne kitchen a buɗe amma ba kowa a falon, ga plate ɗin abinci da suka ci suka barshi a falon banda ƙamshin taliyar manja babu ƙamshin dake tashi, haka ya kashe soket ya jawo ƙofar kitchen kana ya wuce ɗakinsa, ya cire jallabiyar ya rage ƙananun kaya ke jikinsa ya kwanta tare da jan bargo ya rufe ƙafafunsa, Safna ta riga ta cika masa ciki baida buƙatar abinci, kuma da yake yasan halin matarsa bata girka masa komai ba, da zai kirata ya tambayeta zata ce ta manta, guntun tsaki yaja ya kunna data ya fara duba WhatsApp domin ganin saƙonninsa, dama time ɗin chart ɗinsa kenan dan inya fita aiki ba yida lokacin waya saboda hidima da mutane, nan saƙon Safna ya shigo tana cewa.
Allah yasa mijina ya sauka gida lafiya.
Sai da ya saki murmushi kafin ya bata amsa da lafiya lau sai dai yaga bata online, nan ya fito ya shiga duba saƙonni nan ya samu Seema tana online, sai suka fara chart daga nan kuma suka cigaba da hirarsu na sakin layi, haka ya shagala har kusan sha ɗaya da rabi, ya ce mata zai sauka barci zai yi suka yi sallama tana yi masa mitar itafa ta gaji da ja mata rai da yake yi ya kamata yazo su haɗu su jiyar da juna farin ciki, bai bata amsa ba ya sauka dan yasan ba zata taɓa samun wannan damar ba yana matuƙar kyamar aikata zina, wannana chart ɗin da suke yi shima so yake ya yakice shi ya huta tunda Safna tana gabda shigowa gidansa, Zayyad barci yake ji amma kuma cike yake da buƙatar mace a wannan lokacin musamman yadda yasha kunun madara ya tada masa da maitarsa, dan shi da zarar yasha madara da dare ko yogot to tabbas sai ya motsa masa buƙatarsa, ya duba agogon wayarsa sha biyu saura nan ya shiga wajen kira ya lalubo number ɗin Rashida ya soma kiranta sai dai kash tasa wayar a silent ta saka a jikin chargy a wuta, sannan ma barcinta take yi hankalinta kwance dan tuni tayi nisa dan koda ya dawo tayi barci Anisa ce keta danne danne a waya tana chart, Zayyad sauke ajiyar zuciya yayi mai ɗumi ga mace har mace amma sam hoto ce bata damu da buƙatarsa ba sai nata, dan in abin ya motsa mata tasan ta jira shi ya dawo duk inda yaje, kota dinga kiransa a waya tana jiransa. Zayyad ji yayi kamar ya fashe da kuka ko hakan zai sama masa kwanciyar hankali amma koda yayi kukan ba zai yi masa maganin halin da yake ciki ba, sai ya sauka daga gado ya ɗiba ruwan flaks a marfinsa ya shiga shansa yana kurɓa a hankali har ya shanye farin ruwan ya rufe ya koma ya zauna yana mayarda gumi, daga haka kuma yaji sauƙin ƙullewar marar, sai miƙe ya kashe wuta ya koma ya kwanta ya rufa da bargo ba jimawa barci da ɗauke shi.
![](https://img.wattpad.com/cover/375693523-288-k733294.jpg)
YOU ARE READING
AMARYAR ZAYYAD
General FictionSanin abinda ke cikin labarin sai an bini daki daki amma akwai sarkakiya.