10

253 11 2
                                    

*AMARYAR ZAYYAD*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 10.

Rashida da kyar barci ya ɗauketa a wannan ranar sosai ta kuma ƙullatar Safna da zayyad ɗin, hakan yasa ta yi fushi dashi bata kula shi iya gaisuwa kawai ke shiga tsakaninsu, har Safna ta gama kwana bakwai na amarcinta, a ranar Safna da kyar ta bari Zayyad ya fita aiki dan sosai ta langwaɓe masa akan kewarsa da zata yi, koda ya fito sai ya wuce side ɗin Rashida ya samesu a falo, ya zauna yana amsa gaisuwar su Zaliha suka miƙe suna cewa in zai wuce ya rage musu hanya zasu wuce gida, yace to kana suka wuce ɗakin yara dan fito da jakar kayansu. Zayyad ya kalli Rashida fuskarsa sake.

Uwargida har yanzu fushin ake da Zayyad ne? Ya kamata a sausauta masa haka tunda yau kece da shi, da fatan zai samu kyakkyawar tarba.

Kai da kace duk abinda nayi ba burgeka zanyi ba ai babu wata tarba da zaka samu.

Nifa ba haka nake nufi ba, meyasa kike da nacin magana ne da yawan ƙorafi, to kiyi haƙuri komai ya wuce, ki rubuta mini abinda babu ta text anjima zan aiko Jamilu ya kawo miki.

To adawo lafiya dama naso zan je gida kafin yamma na dawo.

A'a ba zaki ko ina ba ki bari sai wani satin.

Dan Allah ka barni na tafi kusan wata kenan ban leƙa ba, bazan jima ba zan dawo.

Amma ki rasa ranar da zaki fita sai ranar girkinki, meyasa haka ne? sannan yara in sun dawo fa.

To baga antynsu ba sai su zauna a gunta kan na dawo.

Hmmmm ba zaki je yau ba, ki yiwa su Zaliha magana su fito mu wuce.

Ya ƙare maganar yana miƙewa ya fice zuwa waje, Rashida cike da takaici ta kwalawa Anisa kira suka fito sai ta rakasu har mota tana cewa.

In Sha Allah ina nan zuwa gobe in Allah ya kaimu ku gaida su mama.

Suka amsa da to kana Zayyad ta tayar da mota ya wuce. Ta koma ɗaki ta zauna tana jin ba daɗi saboda ba kowa sai ita kaɗai, su Ilham sun tafi hadda sai wajen biyu na rana zasu dawo ga duk baƙinta sun tafi, a wannan lokacin ne taji sha'awar son ta ƙara wani haihuwa, dan tun bayan data haifi Aslam ta saka implant na shekara biyar, to gashi Zayyad ya ƙara aure ya kamata ace ta cigaba da haihuwa kafin amarya tazo ta fara nata, burinta ace tafita yawan yara, dan haka tunanin ya tsaya mata a rai da nufin dole ma taje gida gobe daga nan ta wuce asibiti a cire mata implant ba tare da ta sanar da Zayyad ba, dan tasan in ta sanar dashi bazai bari ta cire ba tunda ba son haihuwar yake sosai ba, in kuma ta biye masa itace zata kwan ciki har amarya tazo ta fita haihuwa gwara ace nata yaran sun fi yawa, da wannan tunanin ta miƙe ta nufi ɗakinta ta zauna ta ɗauki waya ta kira ƙawarta Kubura, koda ta ɗauka suka gaisa take ce mata.

Nayi baƙin cikin bikin nan bana nan, amma da zarar na diro gari zaki ganni, wai Rashida kina miye ne har kika bari auren nan ya tabbata?

Ya zanyi to Kubura ƙaddara ta riga fata, gashi ba aje ko ina ba Zayyad yana son nuna mini halinsu na maza saboda yaji sabon guri.

Hmmm ai wlh kece kika yarda amma kin ganni babu wata ɗiya da zan bari ta shigo mini gida wai sunan kishiya, ga Aliyu nan yasha gwada yin auren da magana ta taso za kiji ta kwaranye to an gaya miki zama zanyi, ai ba zan bari ma magana tai kwari ba balle ayi aure, kema tuntuni naga kinyi sakwa sakwa ne amma ko yanzu bata ɓaci ba.

Ni gwara dai ki dawo muji ta ina zamu ɗaura, dan wlh inna cigaba da ganin Zayyad da wata za'a wayi gari aji nayi mushe zuciyata tayi bunga.

Hmmm kisha kuruminki, akwai wani magani ɓata gaban kishiya zan haɗo miki su ki tsuma kanki, ta yadda idan ya kusanceki wlh ita da shi sai rabo in ya tsaga, sannan batun sauran mallakan suma zan sa yayana ya haɗa miki, kin san mu gidanmu yayi ƙaurin suna da malinta.

AMARYAR ZAYYADWhere stories live. Discover now