18

324 12 1
                                    

*AMARYAR ZAYYAD*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 18.

Ght products me Maida Bora mowa💃🏻💃🏻💃🏻 Mai maida mazaje jarumai uwar gida da Amarya suyi ta alfahari da shi shima na alfahari da su🙈😂

Wai haryanzu kina zaune baki gwada ba? Kaima kana zaune baka gwada ba? mata da Maza nata k'ara martaba da kima adalilin ght products, wai kun tsaya kallo? Shin ko sai gwad'o yayi muku k'afa ne?🤔🤥

Yar uwa da d'an uwa ku garzayo in hada muku kayan gyara iya kudinku iya shagalinku.

Mrsjmoon bata tsauwalawa ku dai ku zo musa labule in gyaraku ciki dawaje kuyi tsaf tsaf kuyi cif cif kuyi zaqwai zaqwai kunsan dai zaki na zuma baya illah😋 hakkun duk wanda bai tab'a amfani da kayan GHT ba anbarshi a baya Maza da Mata kada ku bari a barku a baya dan dan Allahb👏🏻 ku ka sance a kan gaba wurin mallakan naku ba jiran ana baku labari ba😍🏃‍♀️🏃‍♀️ Mai so zai iya tuntubar wannan number 08132166848 a Whatsapp ko kira. Nagode sosai.👏🏻👏🏻 Indiawa suka ce bahut bahut shukhriya🥰🥰

Safna koda ta shiga ɗaki ruwan wanka ta fara sakawa domin ta samu ta watsa ko zata ji daɗin jikinta, sai ta ɗauko maganinta a ɗaki ta fito falo ta zauna a cushing ta sha, a lokacin ne Zayyad ya shigo falon dan ta barshi a buɗe, yace ta fito suje part ɗin Rashida Mahaifiyarsa tazo tana ciki, daga haka ya fice sai ta miƙe ta mayar da hijab ɗin data cire ta fito ta nufi sashin Rashida. Da sallama ta shiga wanda idonsu Zaliha ya dawo kanta harta ƙaraso ciki ta zauna a carpet tana gaishe da Ammi, a lokacin Rashida ta farka ta soma zaro ido tana nuna inda Safna ke zaune tana fuzzar da miyau, su Anisa suka yi kanta suna salati, haka shima Zayyad miƙewa yayi ya isa gareta yana tambayarta lafiya, bata iya cewa komai ba sai nuna Safna, wanda ita kuma kallonsu kawai take yi tana jin wani hayaƙi yana yawo a kanta, sarai ta fahimci meke maruwa amma har cikin ranta bata yarda da Rashida ba sharri kawai take so ta yi mata, Ammi ma tana zaune tace su kawo ruwa su shafa mata a fuska dan itama kallon lamarin take yi kamar a drama, bayan sun shafawa fuskarta ruwa sai ta shiga sauke ajiyar zuciya ta dawo hayyacinta, Anisa ta miƙe cikin faɗa.

Gaskiya Safna ki tashi ki fita mun samu ta fara dawowa hayyacinta karki ɓata mana maganin da muka fara yi mata, kuma In Sha Allah aniyarki zata biki.

In Sha Allah aniyar kowa kuwa zata bishi, kuma Allah baya barci.

Cewar Safna cikin kwarin guiwa dan sosai taji zuciyarta a dake babu fargaba ko tsoro. Zayyad ya dubeta rai ɓace.

Tashi ki fita bana son tashi hankali.

Babu inda zata je ta zauna zanyi magana daku duka.

Cewar Ammi cikin haɗe rai, ba wanda ta ƙara magana ta cigaba da cewa.

Anisa da Zaliha dole zasu bar gidan nan a samo wata wacce zata yi jinyar Rashida, dan na kula in dai kuna gidan nan ba zaku bari a zauna lafiya ba, ko kuma su ɗauki Rashidar su koma gida ta yi jinya a can bana son tashin hankali. Sannan wannan ciwon nata alamu ya nuna Aljanun dake jikin Rashida basa shiri dana Safna dan haka sai an tsaya tsayin daka wajen yin maganinta, itama Safna a dage mata, na rasa wannan abu ace girki ba ɗaya ba ko wacce da side ɗinta ba ruwan wani da wani amma ku kasa sakawa zuciyarku salama akan kishi, to gaskiya ba zai yuwu ba duk wacce ba zata zauna lafiya ba to zata tafi gidansu.

Amma Hajiya ita Safna da Anisa tayi magana meyasa zata biye mata, ba sai tayi shuru taga hukuncin da zan ɗauka ba.

Tunda na zo gidan nan mutanen nan suke bina da rigima, na kawar da kai nayi haƙuri amma ba zasu fasa ba, yayarsu tayi mini suma suyi mini, ina ce a ranar da aka kawo ni cikin gidan nan bayan 'yan uwana sun watse sai da suka haɗani faɗa da kai, buga ƙofa da sassafe bani da sukuni a cikin gidan nan, Rashida ta takura mini bayan ni bana shiga lamarinta, yarinya ta fasa mini kwanon dana saka maka yaji jiya ta kawo sai naja mata kunne akan karta ƙara, saboda sau biyu kenan suna fasa mini kwano, amma ba halin na yiwa yaran nan faɗa Rashisa zata zo har ɗakina tana gaya mini maganar da yayi mata, ya kake so nayi.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 25 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AMARYAR ZAYYADWhere stories live. Discover now