*AMARYAR ZAYYAD*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 17.
Bayan sun shiga falo kowa ya zauna kukan Safna ne ke tashi a ciki, babu wanda yace tayi shuru ko ya tambayeta abinda take yiwa kuka, har ta gaji dan kanta ta yi shuru tana ajiyar numfashi, a lokacin ne Yusuf ya shigo ya miƙawa Umma sugar ta amsa ta saka a cikin kunun tsamiyar data dama musu, data gama juyawa ta zubawa babansu a kofin jug tasa Yusuf ya miƙa masa tare da kular ƙosai data zuba masa, daga nan ta sakawa Mudan sai Yusuf, a lokacin ne ta kalli Safna da take zaune a takure a carpet.
Kin karya?
U-um ta bata amsa haɗe sa girgiza kai, umma ta zuba mata a wani kofi da ƙosai a plate tasa Yusuf ya miƙa mata sannan ya koma ya cigaba da karyawa, falon ya ɗauki shuru sai cin abincinsu suke yi sai dai ko wanne zuciyarsa cike yake da damuwar ganin Safna, amma da yake sun san dokar Abbansu yasa kowa yayi shuru har sai shi ya buɗe baki ya fara magana, Umma ma dauriya kawai take yi tana tusa abin karin ba dan tana jin daɗinsa ba, ace yarinya ko wata biyu bata cika a gidan aurenta ba amma matsaloli suna biyowa baya irin haka, duk ta ƙosa taji meke faruwa, ɓangaren Abba kuwa yana sane yaƙi cewa kowa har sai ya karya tukuna, shiyasa daya kammala ya miƙe ya shige ɗakinsa ya shirya cikin manyan kaya har da malum malum kafin ya fito yana gyara zaman hularsa ya samu guri ya zauna, wanda a lokacin duk sun gama karyawa Safna ce dai data kasa cin komai tana wasa da yatsunta babu kuma wanda yace taci dole, Abba yayi gyaran murya yana dubanta wanda yasa Safna tattaro duk natsuwarta.
Mamana meya kawo ki gida a irin wannan yanayin? Bana so kiyi mini karya ki faɗi duk abinda ke faruwa muna saurarenki.
Safna bata taɓa zaton Mahaifinsu zai tambayeta cikin sassauci haka ba, hakan yasa ta samu damar sauke ajiyar zuciya abinda take ji ya tokare mata a wuya ya sauka, sai ta shiga basu labarin irin matsalar data fara fuskanta da Rashida har kawo abinda ya faru yau, sai ta ja fasali tare da sauraren me zasu ce, umma tace cikin damuwa.
Ban zaci haka daga gareki ba Safna ina yabonki da haƙuri ashe ba kida shi, meyasa zaki biye mata? Kenan duk jan kunne da faɗar da muka yi miki ya tashi a banza ko, wannan ba shine tarbiyyar da muka baki ba, sai ki biye mata kunyi faɗa keda nasan aljanunki bama sa tashi. Me yasa sai yanzu zasu yi haka kuma anata magani.
To mugunta suka shirya mata mana, ace anyi maganinsu sai da aka yi aure zasu riƙa tashi, ashe maganin ya zama aikin banza. Sannan Safna meye dan sun fasa miki plate, saiki rabu dasu in ma kina buƙatar wasu ne saiki kira ki faɗa a siya miki, kuma bai dace ki hukunta yarinya ba tunda har uwarsu tanuna ki daina takurawa yaranta, wataƙila da su zata riƙa amfani dan ganin tana tunzuraki aljanunki na tashi, kinga in hakane to ta samu nasara akanki tunda gashi tayi sanadin da Mijinku ya koro ki gida kuma ko wata biyu baki rufa da aure ba, wannan kinga ya zama kin zubar mana da mutunci da ƙima, dan haka daga yau wannan ya zama na farko da ƙarshe, na rantse da Allah idan har kika sake biye mata kuka yi faɗa koda ta baki ne Zayyad ya koroki gida to ki sani sai na yi miki dukan da tunda kika zo duniya ba ayi miki irinsa ba. Idan ma tayi miki wani abu ki jira ya dawo ki faɗa masa shi ya ɗauki mataki, amma zanfi so karki zama mai kai ƙara ki zama mai haƙuri juriya da kawar da kai, ki tashi cikin dare ki faɗawa Allah ki sata a addu'a akan Allah yayi miki ganinta ya kawar da saɓani a tsakaninku, in kinyi haka In Sha Allah zaki ga kyakkyawar sakamako, dan haka yanzu zan fita bazan jima ba zan dawo ki shirya zan mayar dake gidan mijinki. Ke kuma sai ki ƙara ja mata kunne dan wlh bazan ɗauki wannan shegentakar ba.
Abba ya ƙare maganar akan umma, to tace masa kana ta yi masa a dawo lafiya ya wuce ya fita, a lokacin Mudan ya soma magana.
Gaskiya idan kika ƙara faɗa da kishiyarki wlh har gida zan zo in miki shegen duka, haba Safna ya za ki biye mata kuyi abu sai kace a zamanin jahiliyya, karki kuma aikata haka dan ban sanki da rikici ba, yau da Maryam ce aka ce tayi haka bazan musa ba dan ita tana da zafi da gatsali.
YOU ARE READING
AMARYAR ZAYYAD
General FictionSanin abinda ke cikin labarin sai an bini daki daki amma akwai sarkakiya.