*AMARYAR ZAYYAD*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 6.
Safna tana kwance tayi lamo dan har barci ya fara fizgarta sai taji wani irin bugun ƙofa kamar tarar aradu, a razane ta tashi ta zauna dan ƙirjinta saida yayi wani irin bugawa saboda zazzafar tsoro daya dirar mata, jin an cigaba da buga ƙofar ya sata saukowa daga gado ta fito falo, sai ta isa ƙofar ta kara kunnenta dan ji hira sama sama data fito, nan ta tsinkayi muryar wata tana cewa.
Wannan 'yar iskar amaryar 'yar rainin wayo ce, ji yadda muke buga mata ƙofa amma taƙi ta buɗewa.
Anisa muje kawai tunda bata buɗe ba dama sai da nace ki bari mu ganta zuwa gobe amma kika nace sai kin zo.
Na ƙosa ne naga wacce tafi Anty Rashida da Zayyad taketa rawar ƙafa akanta, amma taci bashin wannan wulaƙancin data yi mana.
Safna tana jinsu amma taƙi buɗewa dan hirarsu ya tabbatar mata da 'yan uwan Rashida ne, banda niman fitina taya daga kawota zasu zo suce zasu ganta ai koma miye sabari washe gari tunda yanzu ango ne ya dace ya shigo ɗakin ba wasu ba, imma ganinta ne zasu gaji da ita tunda zamane na dindindin. Sai ta koma cushing ta kwanta tana tunanin su, ashe gwara data rufe ƙofar da Anty maryam ta ce mata, bata san da wanne ma suka zo ba a cikin wannan daren.
Anisa suna shiga falon Rashida ta tsaya tana zagin Safna, Zaliha tana tayata tare da wasu 'yan uwansu da suka je tare, dan zasu kai kusan su biyar waɗanda suka je sashin Safna da niyyar su ganta, Rashida ta kallesu tana cewa.
To kuma uban waye yace kuje, ai gwara data yi muku haka gobe kwa ƙara.
Amma meye laifinmu dan munje muyi mata hira kafin angon yazo. Wannan ai wulaƙanci ne tana ji ana buga ƙofar tayi banza damu.
Rashida ta ƙanƙance idonta tana cizon yatsa ta miƙe tana faɗin.
Aiko saita san ta wulaƙantaku dan daren yau In Sha Allah ba zata kwana cikin farin ciki ba, sai nayi amfani da wannan damar na bar mata tarihin da har ta koma ga Allah ba zata manta da shi ba. Miko mini wayata na kira Zayyad.
Ta faɗa tana nuna inda ta saka chargy, Nan suka saki shewa Anty Wasila tana cewa.
Yauwa 'yar gari gwara ki fara nuna ikonki na uwargida, tasan cewa kece da gida bata isa ta samu yadda take so ba sai in kin so hakan ya faru, komai sai da makirci gwara ki hau kan layin dana ɗauraki shima zai miki amfani sosai matsawar kin iya takunki.
Murmushi Rashida ta saki ta koma ta zauna tana ɗaura ƙafar damanta akan center table.
Ai tunda ta yarda ta auri mijina ita da farin ciki sunyi sallama.
Sai ta amsa wayar da Zaliha ta ɗauko mata, dama falon ba kowa sai su dan duk mutane sun watse wasu baƙin kuma suna can ɗakinta sun kwanta wasu kuma sunje gidansu, sai ta shiga wajen kira a wayarta ta danna number ɗin Zayyad, bugu biyu ya ɗauka zata yi magana ya rigata.
Gani nan na kusa ƙarasowa gida ina hanya.
Cikin yanayi na rauni da sanyin murya tace.
To sai ka ƙaraso.
Rashida lafiya kuwa naji muryanki cikin damuwa.
Ka bari dai ka ƙaraso ɗin.
Tana kaiwa nan ta kashe wayar tana sakin wani shu'umin murmuahi, Zayyad kam kasa haƙuri yayi ya shiga kiranta amma taƙi ɗagawa, hakanan ya samu kansa cikin damuwar yadda yaji muryarta, dan sosai yake tausayinta ba ƙaramin jarumta tayi ba da auren nan nasa yana jinjina mata akan haka. Rashida ta kalli Anisa tana cewa.
YOU ARE READING
AMARYAR ZAYYAD
General FictionSanin abinda ke cikin labarin sai an bini daki daki amma akwai sarkakiya.