#13 in romance hot list. 25/1/2017 Still faring high after months of completion. Thank you.
A duniyar Aneesa babu abinda ya kai mata Innarta muhimmanci, gashi Innarta ta tura ta birni ta zauna da mutumin da bata taba haduwa dashi ba iya rayuwarta...
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
"Aadil, kabi duk abun da ya dace na ka'ida ka tabbatar mun samu farfosal din nan abu na farko da safe, kar ka bari mu rasa wannan kwangilar kafi kowa sanin muhimmancin sa a wurin mu" Ya fada yana rike da wayarsa da bata faye nauyi ba nesa da kunnensa kadan.
"In sha Allah zan tura nan da nan" ya dan yi shiru kafin Aadil yace "yaya wurin su Hajiya?"
Sagir ya ci gaba da goga saman hancin sa da tsakanin idanuwan sa a hankali, wasu lokutan yakan manta cewa Aadil babban abokin sa ne baya ga mai kula da harkar kwangila na kamfaninsa idan harkar kasuwanci ta taso, amma Aadil a ko da yaushe yana tabbatar da cewa ya sauke nauyin abotar su.
"Lafiyar su kalau." ya kusa ajiye wayar kafin nan yace "Aadil, na gode da komai"
Aadil yayi murmushi sannan ya ajiye wayar ya shiga tattara duk abin da zai bukata na taron washegari.
Sagir Mustapha Daggash, dan kasuwa ne mai tashe, mai shekaru talatin da uku a duniya. Kanuri ne da dan ratsin fulani a tare dashi. Mutane da dama sukan ce ya dauko kyaun siffarsa daga mahaifinsa ne, yayin da wasu sukace ya dauko kyaun, nadadden bakin gashin kansa ne da kyaun idanunsa daga bangarren mahaifiyarsa kasancewarta bafulatana. Wannan ya bashi mix din kamanni tamkar wani kyakkyawan dan Morocco. Koma daga ina ya samo kyaun sa, a tsawon sa kafa shida da 'yan kai hade da yanayin ginin jikin sa baza ka kira shi jibgege ba amma kuma a tsaye yake, kana ganin Sagir kasan yana kula sosai da lafiyar jikinsa, abun da yafi bada mamaki a tattare da Sagir shine duk da kasancewar sa mai kyau, mai kudi mai kwarjini bai sa ya iya juya AL'AMURAN da suka shafi ZUCIYARsa ba, sam wannan baya gabanshi.
Bayan maganarsu da Aadil, ya sake yin wayoyi biyu duk dangane da harkar kasuwancin sa, kafin nan ya fara shirin kwanciya. Lokacin da ya sake jin wayar sa na tsuwwa, saura kadan yaki dagawa amma sai ya duba ko Aadil ne yayi mantuwa, ganin lambar kanin sa yasa yayi saurin dagawa.
"Kamaal, kasan da cewa yanzu kusan daya na dare ne ko?"
"Hello," Sagir ya kyafta idanu jin damuwa a muryar kanin nasa yasan ba lafiya ba.
"Hello Kamaal, me ke faruwa?" bayan dakikai muryar kanin nasa ya doki kunnen sa.
"Yaya, Abba na asibiti" a take sagir yaji wata faduwar gaba, sai kuma Kamaal yace "ya samu ciwon zuciya!" kwarai ya razana.
Abin mamaki duk da razanar da yayi sai ya samu nutsuwa yace "Subhaanallah, ina kan hanya yanzu" kashe wayar yayi ya wawuri makullan mota. Yaya hakan ya faru? Me ke damun Abba? ko tunani yakeyi sosai, ko dai abinci ne baya cin mai kyau? Sagir nan da nan yaji komai yana warware masa.
"Likita, yaya jikin nasa?" doctor Ahmad ya kama hannun Sagir da ya miko masa don su gaisa
"Alhamdulillah, yanzu ya fita daga hatsari sai dai yana bukatar hutu"
Sagir ya saki numfashin da bai san yana rike dashi ba. "Zamu iya ganin shi yanzu?"
"Eh zaku iya shiga, sai dai ku shiga da daddaya, saboda yanzu baya bukatar wata hayaniya."