BABI NA GOMA SHA BIYAR

8.8K 679 100
                                    


BABI NA GOMA SHA BIYAR

Iskar dada karfi takeyi, irin ruwa mai nacin nan ne, lokaci daya ya tsuge sai dai karfin shi ya ragu ya karu. Aneesa ta dubi agogon da ke makale kan siririn hannun ta yafi a kirga, yayin da take kokarin gyara jakar da ke hannunta , wanda a yanzu ya kusa zamewa daga jikin ta gaba daya, Saboda tashin hankali.

"Amma ko ina Uncle Aadil ya tsaya? Yasan halin da nake ciki kuwa? Me zai sa yace na jira shi bayan ya san baya kusa?. Ga shi ba inda zan shiga na rabe kafin ruwan nan ya tsagaita! ko dai na koma cikin makarantane?" Tambayoyin da suke cikin kwanyarta kenan.

Ta daga kanta tana duban titin da kusan babu kowa sai motoci jifa-jifa da suke ficewa daga makarantar ko shigar ta. Ga 'yan tasi amma tana jin tsoron shiga, saboda ba wai ta san gari bane sosai. Sannan wane ita ta taka cikin wannan yanayi. Ga uwa uba wani dan karen nauyin da yake dankare a zuciyar ta idan ta tuno abun da ya faru. Kai... tsaya shin ta ma san me ya faru kuwa? Me ake boye mata? Tayi saurin girgiza kan ta sai a lokacin ta kula da safa da marwan da take tayi a kan layi.

Saura kiris ta juya zuwa inda ta fito dai-dai nan ne taji karar tsayuwar mota a gefen ta. Mai tuka motar yayi saurin bude mata kofar gaba, yayin da tayi saurin shigewa ciki. Sai da ta natsa ne ta goge ruwan fuskar ta sannan ta dube shi a cikin kagara amma ganin yanayin fuskarsa yasa ta dan sassauta.

"kiyi hakuri da barin ki da nayi a cikin ruwa, (traffic jam) na samu kan hanyata ta zuwa nan, ina fatan dai bakiyi fushi ba?" Aadil ya fada yana kallonta ta gefen idon shi.

"Uncle Aadil, banyi fushi ba fada min me ya samu  Uncle Sagir dina?"

"Kar ki tada hankalinki, daga can nake yanzu, kuma Alhmadulillah. Saboda haka ki kwantar da hankalinki kinji?" ya fada yana kallonta "Subhaanallah, duk kin jike"

Aneesa sai kada kafafunta takeyi labbanta suna bari, ji takeyi kamar Aadil baya ma tafiya a motar.

"Na sani, me yasa malam Hassan bai zo dauka na ba?"

"Ni nace masa ya tsaya a asibitin, tare da Kamaal koda wani abu zai taso, kuma na fi son na fada miki da kaina."

Cikin kidima ta juyo ta dube shi "Uncle Aadil ba mutuwa Sagir yayi ba kuke boye min ko?" ta dube shi da idanu masu dimbin bada tausayi, da raunana zuciyar mai kallonsu.

"Sagir yana lafiya kalau da ranshi, kaman yanda na fada miki hatsarin mota kawai yayi, ya dan samu rauni amma yanzu haka na bari likitoci suna dubashi ma, sunce anjima zasu shiga dashi dakin tiyata"

Ai Aneesa shiru kawai tayi, ta jingina da kujera tana zubda kwalla, don sai taji bata jin sautin kukan ma, can ta furta "Duk ni na jawo, ni nace masa yayi sauri ina son muyi magana."

Aadil ya dubeta hade da cewa "Aneesa ki daina wannan maganar, kiyi shiru addu'a zakiyi."

Ya sa hannu ya kunna na'urar duma motar, domin ya kula ta fara barin sanyi. Ya san ko ya ce subi gidanta ta canza kaya bazata amince ba don haka kai tsaye ya kaisu asibitin. A filin Adana motoci na shahararren asibitin Aadil ya tsaya.

Yana tsayawa Aneesa ta balle kofar motar ta fita cikin sauri.

"Aneesa!" Aadil ya kirata yana kara sauri, "ga wannan" ya mika mata lema.

"A'a ka barshi"

Tare suka shiga asibitin, suna karasa shiga ciki zuciyar Aneesa na kara bugawa. A bakin kofar ta ja ta tsaya, tana tunanin ko ta shiga ne ko ta juya, wata zuciyar tace mata "Aneesa Sagir ne fa a kwance a ciki."

Nan taji wani karfin gwiwa ta samu ta karasa ciki. Dole ta shiga ta ganshi koda kuwa bayan hakan bata san yanda zata rayu ba, tunda dai itace sanadin abun da ya faru da shi ranar.

Al'amarin ZucciOnde histórias criam vida. Descubra agora