BABI NA SHA SHIDA

10.9K 666 243
                                    

BABI NA GOMA SHA SHIDA

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

BABI NA GOMA SHA SHIDA

Hajiya Juwairiya tana zaune banda ikon Allah ba abun da take gani, ita ta rasa ma da wanne daya zata ji, bakin cikin da ta tsinci kanta bata taba mafarkin zai sameta ba. Wannan tashin hankalin dai ya samo asali ne a safiyar jiya.

Lokacin da Daddy ya tara su yana shirin fita wurin aiki "Abun da yasa na taraku a nan abubuwa uku ne, na farko dai na je nayi magana da makarantar su Sameeha zata koma karatunta amma an mai da ta ajin baya saboda differing da na mata tun a wancan lokacin na session din da ya kare" Nan da nan Sameeha ta hau murna tana godiya, Mummy ma abun yayi mata dadi ba iyaka.

"Na biyu kuma shine kwanaki, akwai wanda ya zo neman izinin ya nemi auren Sameeha, kuma na amince masa don haka Sameeha zaki iya ganin bako a ko wani lokaci" Nan take zuciyar Sameeha ta hau bugawa saboda ta tsorata ganin ita har ga Allah mutum daya da ya kwanta mata a rai ya mata nisa saboda ba yanda za ayi yama fara aurenta, a bangare daya kuma ta samu Daddy ya fara damuwa da al'amarinta, har ya amince da wannan mutumin idan ta kuskura ta nuna kin amincewarta to bazata kwashe lafiya ba, don haka ta qudurta zata samu Aneesa ta nemi shawara a wajenta game da abunyi.

"Abu na karshe kuma ina so na shaida muku, idan Allah ya kaimu wata mai kamawa ina da niyyar kara aure"

Fuskokinsu ne gaba daya ya hasko tsoro da razana hade da mamaki. Zaheeda da Khazeena suka ce "Daddy Aure?"

Hajiya Juwairiyya kam tsabar razana ta gagara magana sai kifkifta idanu takeyi kawai. "Daddy wani abu Mummy tayi maka?"

"A'a Khazeena aure ai ana yin shi ne don bautan Allah, da kuma cika da kamalar rayuwar dan Adam ba sai Mummy ta min wani abu ba, lokaci ne kawai yayi, kuma ina so ku dau maganar nan, cikin natsuwa duka na san kun girma kuma kowacce da tunaninta kowa aure zatayi nan gaba kadan kuma ba laifi bane ku samu wata ko a same ku. Ina son ku dauke ta kamar yanda kuka dauki Mummy."

Jikin su kaf yayi sanyi, ya san tabbasa zai samu matsala wajen bullo da wannan maganar amma kuma ya duba yaga abun da kawai zai yi kenan ya kashe wutar gidan shi.

"shi kenan ku tashi kuje."

Sameeha ce tace "Daddy a ina ka samu matar?"

Ya dubi sashin da Mummy take zaune ba uhm ba a'a yace "kuje zan fada muku daga baya."

"To, Allah ya kaimu"

Haka yaran suka watse daga falon, a hankali ya juyo ya dubeta "Juwairiya..."

Hannu ta sa ta dakatar dashi "Mahmoud, ka cuceni, ka wulaqantani, ka musguna min, abin da za ka min kenan? Duk hukuncin da ka dauka a kaina na dauka na rungume shi amma hakan bai isheka ba shine zaka kara aure a wannan shekarun? Ka tuna fa ka fara aurar da 'ya'ya, so kakeyi kana haihuwa yaranka na haihuwa? kai duk a bar wannan zancen, a gaban yarana zaka bani wannan mummunar labarin ashe haka tsanata da kakeyi yayi zurfi a zuciyarka?"

"Sam babu ko daya, ni ban ki ki ba, ba kuma muzanta ki nayi ba, ina da dalilina na yin wannan maganar a gaban yara. Amma idan hakan bai yi miki ba sai kiyi hakuri. Auren nan da zanyi dukan mu ya fi mana rufin asiri."

Al'amarin ZucciWhere stories live. Discover now