BABI NA GOMA SHA UKU

8.1K 691 166
                                    


BABI NA GOMA SHA UKU

SHEKARU BAKWAI DA SUKA GABATA

Facal! Facal! ta wurga ta sake dauko wani ta jefa "Wallahi ban yarda ba sai kin sake, wancan bai shiga da kyau ba"

"Falmata, ke dai kawai kin faye cogel. Nawa ya riga naki, ko ba haka ba Abulle?"

Abulle tace "Uwani, kullum ke kike ci. Gaskiya a sake."

Uwani tana dariya tace "Hmm, gwamma ku Falmata yau bazaki makaranta bane? Ni kam nayi gida zan shirya kar Inna ta min fada."

Abulle tace "Ai makaranta sai ke, Innar Falmata ta cire ta. Ke ma ban san me zakiyi da bokon nan ba kaman wani jaraba, kin bi kin nannace masa duk sa'o'in mu ke kadai kika nace."

"Ku zauna nan dai baku san dadin iya karatu bane shi yasa. Kuma bazan bari ba. Sai anjima" Tana fada ta juya cikin sauri ta bar bakin rafin.

Tana tafiya taji ana binta a baya don haka ta rage sauri ta dan juya kadan, ai tana ganin shi ta kara sauri.

"Uwani, Uwani ki tsaya mana muyi magana me yasa kike gudu na ne?"

Wayyo, yaya zatayi da wannan sarkin nacin nan ne? "Na ce maka ka daina bi na, bata lokacinka kakeyi."

"Haba Uwani, ki fada min yaushe zan same ki a gida muyi magana."

"Idan na shirya zan neme ka yanzu karatu nakeyi don Allah ka daina bina."

"Naji Allah ya baki hakuri, sai anjima."

Ta wuce tana sauri kaman zata kife ta shiga gida, kai tsaye dakinta ta wuce ta fidda kayan makarantarta sannan ta shiga wanka, tana shiryawa ta samu Inna a madafi.

"Yau ma sai da kika kara lattin ko? Ni na rasa wannan wasa naku na fama da kullum sai an yi shi, sai nayi magana da malam ya sa a rinka wassafa ki a makarantar tukun."

"Inna kiyi hakuri, bazan sake ba."

Nan ta dauki kular abincinta tayi waje da sauri, tana fita ta wuce su Sheyido suna wasa a gindin bishiyar kofar gidan su, "Uwani yanzu ke kadai a cikin maza zaki koma ajinku wannan shekarar?"

Murmushi tayi cikin rashin damuwa tace "Je ki dauko takardunki mu tafi."

"Tab, Baffa zai min duka. Sai kin dawo." Tana juyawa taji sun tafa suna dariyarta, ko a kwalar rigarta ta tafi makaranta. Idan an tashi ma bata tafiya sai da Malam Habu saboda 'yan mazan tsokanarta sukeyi. Don ita kadaice mace a ajinsu, sai gwamma daya ajin ma akwai mata biyu.

"Baba kana gani yau ma sai da su Tukur suka tsokane ni ko?"

Malam Habu ya ce "Ki rabu dasu, abunki da suka tsokane ki ai baki manta me aka koya muku a aji ba ko?"

Kai ta daga masa sannan suka ci gaba da tafiya har suka koma gida.

Tana isa gida ta tarar Inna Halima ta daura sanwa, hakan yasa ta maida kayan gidanta jikinta ta shiga yi mata wanke-wanke.

Hakan ya kasance mata al'adarta kullum, ranar da yamma bayan ta gama ayyukanta ganin ba makarantar Muhammadiyya tace "Inna ina son na je na duba Mama tun shekaranjiya banje ba."

"Ki gaishe su, ki tafi a hankali don Allah. Ba ruwanki kuma da yara daman."

Uwani ta fita sai sauri takeyi, domin duk inda ta wuce gulmarta akeyi wai ta ki barin boko alhali sauran kawayenta duk basuyi. Don Falmata ma aure za a mata da kaaka.

Kaman wani hadin baki tana fitowa daga gidan Mama sai ta tarar da Nata'ala a bakin kofa, "Uwani yau kam don ALlah ki tsaya, ban san me na miki ba kike wulaqanta ni haka."

Al'amarin ZucciМесто, где живут истории. Откройте их для себя