Frankfurt, JAMUS24 YULI, 2010 --- 7:31 PM
"Sannunku, Fasinjoji daga jirgi na 17 zuwa Tel Aviv, an canza kofar tashi zuwa kofa ta 16A. Za a samu jinkirin tashi saboda mummunar yanayin waje.
ƙungiyar da ke kasa na kan aikin cire kankara daga fuka-fukan jirgin domin shirin tashi .
Har ila yau kuma jirgin a dan cike yake don haka muna miƙa kyautar tikitin zagayen tafiya da dawowa zuwa 'yan fasinjojin da a shirye suke da su bi jirgin baya.
Zamu fara bodin nan da minti arba'in. Mun gode da hakurinku." Matar da take magana daga muryar komfuta ta gama jerowa cikin shiryayyen turancinta, kafin ta sake rattabowa cikin wasu fitattun yarukan duniya.
Kwarai ba haka fasinjojin suka so ba kasancewar sun riga sunyi kusan awa guda suna jiran a kirasu.
MASDOOK
"Ya ilaahi yanzu mutum sai ya sake jiran kusan minti arba'in a wannan wurin? Allah dai ya sa kar na makara domin kuwa ba zan iya jure babban asarar da za mu yi ba muddin ban isa a kan lokaci na hadu da Adir ba."
Ganin jiran ba na lokaci kalilan bane yasa ya shiga neman wurin da zai dan rage aikinsa, can ya hango wurin zama. Don baya son zama cikin falon baki na musamman hakan ya sa ya fito wurin jira na jama'a baki daya ba tare da ya shiga wurin hutawar baki na musamman din ba.
MIHJANA
Littafin hannunta ta rufe, duk da bata son waiwayawa taga abun da yake faruwa hatsaniyar ta dameta, agogonta ta kara kallo a karo na uku. Bata san lokacin da zasu tashi ba -yanzu ma an jinkirta jirginsu, dalilin da yasa take zaune a nan kenan a karo na farko sakamakon rasa jirgin da ya dace ta shiga da tayi- Bayan sun tsaya domin shiga jirgin da zai karasa da su Birnin na Tel Aviv.
Ba abunda ta tsana irin wuni a filin jirgi duk da dai ba kullum take tafiya a jirgi ba amma iya tafiyar da tayi ta san cewa akwai 'kularwa da ban haushi ka zauna tsawon awa uku ko ma fi jiran jirgin da zakuyi tafiyar da bata wuci ta awa guda ba, duk da dai yau tafiyar tasu kusan awa hudu ce.
Madubin idanunta ta sake gyarawa da zimmar ci gaba da duba littafinta. Ihun da ta jiyo alamar hatsaniyar tana kara kamari ne yasa ta sake maida hankalinta garesu. Me yasa batayi mamaki ba da taga mutumin da ake rikici dashi?
A fadin filin jirgin kaf! a rasa wanda zai kawo irin wannan tashin hankalin duk gamayyar jama'a na launin fatar bil'adama a wurin sai dan KASARTA? Duk da bata da tabbacin ko shi dan wani kasa ne taga lallai bakin fata ne, sannan kuma daga jin turancinsa dan kasarta ne gashi sai daga murya yakeyi, can dai masu kula da harkan tsaro sukayi gaba dashi.
Mihjana ta girgiza kanta cikin takaici da Allah wadaran irin dabi'armu da ba za mu iya yin abu mai sauki ba kaman bin dokar wuri ko da kuwa wurin bako ne a garemu.
KAMU SEDANG MEMBACA
Al'amarin Zucci
Romansa#13 in romance hot list. 25/1/2017 Still faring high after months of completion. Thank you. A duniyar Aneesa babu abinda ya kai mata Innarta muhimmanci, gashi Innarta ta tura ta birni ta zauna da mutumin da bata taba haduwa dashi ba iya rayuwarta...