"Ni gaskiya bana son wulakanci, yaya za ayi sai zan tafi makaranta sai bazaku ajiye min komai na ba, mummy gaskiya ki kori wannan Hannatun, wai ita meye aikin ta? idan ta gyarawa mutum wuri kullum sai bazata ajiye masa abun sa yanda ya bari ba." Zaheeda ta fada tana huci tamkar tukunyar da ta tafasa
"Yi hakuri Zaheeda, ina Hannatun bari na kirata tazo ta duba miki." Mummy ta fada cikin lallashi.
"Gaskiya mummy ni idan tasake min haka kawai zata koma kauyen su ne," nan fa aka taso keyar Hannatu wai tazo ta nemi rigar saman uniform din Zaheeda (blazer).
Gaba daya gidan sai da ta tada kowa saboda sababin da takeyi wai 'yan aikin gidan sun raina ta'. Suna zaune zasu karya ne, Daddy yace "wai meye ne tun da sassafe nake ta jin hayaniya a gidan nan?" nan da nan kowa tayi tsuru da idanu, "ina magana kuna jina?" ganin daddy ya bata rai sai Khazeena tace "Zaheeda ce bata ga uniform dinta ba shine tace sai mummy ta kori hannatu tunda bata ajiye mata kayanta inda ya dace" Harara Zaheeda ta sakar mata ta doki kafarta ta kasan table.
Daddy yace "Haka akayi zaheeda?" bai jira amsarta ba yace "ashe daman maganar da nake fada muku baya zama a kunnen ku ko? na sha fada muku, mutum komin kashin sa yana da daraja, kuma don kina sama da wani ba wai yana nufin ki musguna masa bane, don yau kunga tarin 'yan aiki a gidan nan saboda ina da ikon daukan su? Watarana idan bani dashi fa wa zai muku komai? Idan kukayi wasa duk sai na sallame su, ku kama ayyukan gidan sai muga ko da dadi. kar na kara jin wani ya sake raina wani dan aiki ko da ma ba na gidan nan bane."
Jikin ta yayi sanyi amma ranta yayi mummunar baci, don me yasa Khazeena zata fada har Daddy yayi mata fada, duk laifin wannan Aneesan ne tun da ta zo gidan ya daina dadi.
Haka ta figi jiki suka tafi makarantar. Sameeha ko ranar bata da lecture tana gida, don haka ita da Aneesa aka bari, mummy kuma ta tafi shagon ta da yake Garki modern market.
Suna fita Aneesa ta tattare kwanukan kan tebur din, don tun ba yau ba mummy ita take sawa ta kwashe daddy na barin wurin, don haka kafin ma tace ta tattara sai ta kwashe. Ta gama kai kwanukan tana goge kan tebur din ne ta ga wayar Sameeha.
Ta daga zata kai mata kenan, sai sako ya shigo mata. Aneesa tace "yawwa ga chatin nan bari yau kam nagani." Ta sa hannu yanda taga Sameehan nayi a kan glass din wayar taga sakon ya budu.
Babe i'm really missing you, can't wait to see you. I miss those soft lips...
Aneesa ta karanta sakon ta nanata, ta fahimci komai na sakon to amma me yasa kawarta zatace mata tana kewan bakin ta? Sai ta kara dubawa Hamza ta ga sunan mai sakon. Nan Aneesa ta kara kidimewa. Yau me ya hada Sameeha da namiji da zata rinka wannan maganar dashi? Carab sai kuwa sukaci karo da ita. Sameeha ta tuna ta bar wayarta a falo ta dawo da wuri don ta dauka ta manta bata kulle wayar ba. Kawai sai ga shi taci karo da Aneesa "wai ku a kauyen ku ba ku tafiya a hankali ne? ko da yake naji ance da tumakan ku da mutanen ku duk daya ne."
Ran Aneesa ya baci sosai amma bata nuna mata ba. Wucewanta kawai tayi daki, ba tare da ta bata wayar ba.
Wuni Sameeha tayi tana neman wayar nan. Aneesa bata ce mata komai ba, wayar na dakin Aneesa sai da aka tashi cin abincin dare Aneesa ta fito da wayar ta cire ta a silent, ta ajiye a gefen ta.
ŞİMDİ OKUDUĞUN
Al'amarin Zucci
Romantizm#13 in romance hot list. 25/1/2017 Still faring high after months of completion. Thank you. A duniyar Aneesa babu abinda ya kai mata Innarta muhimmanci, gashi Innarta ta tura ta birni ta zauna da mutumin da bata taba haduwa dashi ba iya rayuwarta...