Tunda ta bige kan kafet bayan isha'i bata tashi sanin inda take ba sai da lokacin tashinta yayi, ta farka taga kayan jikinta duk sun shashaketa. Da sauri ta shiga bayan gida ta watsa ruwa sannan ta fito ta fara nafilfilu kafin lokacin sallah yayi. Sai da taji shirun yayi yawa ne tsoro ya soma kamata. Ta fara Allah-Allah a kira Sallah tayi sallah, ai kuwa kaman ladan ya jiyo kukanta nan ya shiga kwado kiran sallah a masallacin kusa da su. Tana idarwa ta gyara abun da zata gyara a dakin ta kimtsa cikin wani material mai laushi marar nauyi, dinkin ya mata kyau nan ta nemi mayafin da ya shiga da su ta yafa sannan ta fito falon tana sanda, zata wuce kitchen domin sarrafa abin karyawa, ji tayi kawai yace "kin tashi lafiya?"
Da sauri ta juyo a birkice, kasancewar falon duhu ne kaf ya karade shi, da taimakon wutan lantarkin da suka haska waje tamkar safiya ne yasa ta hango hoton surar shi a zaune kan kujera.
A hankali ta dawo suka gaisa, "yaya naga kin fito da sassafe haka?"
"Daman abinci nake so na hada"
Ya kare mata kallo sannan yace "tun da sassafe?"
"Eh, ban saba baccin safe ba, kuma bani da abun yi"
"To, ba laifi. Amma kiyi shi cikin karanci don naga kunu a flask shi nake bukata kawai"
Nan ta tuna da kununta na jiya ita bata ma sha ba, tace masa "Tun na jiya ne fa?"
"ke ba sha zakiyi ba?"
Ta amsa masa yace "To idan har ke zaki sha me zai hana ni sha?"
Jin hakan yasa ta mike, ta tafi kicin din. Tana bude flask din taga da zafinsa sosai, ita bata taba tunani mutum kaman uncle Sagir ma ya san kunu ba bare ya sha. Kofi mai fadi ta dauko ta ajiye ma'adanin suga akan tire da cokali ta koma falon zata ajiye a dining yace mata ta kawo masa falon. Ta lura wani aiki yakeyi a komfutarsa, sai dai yana kallo ta saka komai kaman bata da jini a jiki. Ita kuma duk tsoronsa kesata hakan don kar ta mishi shirme ya sake ce mata bakauyiya.
"Ga wannan ki yi amfani dashi." ya mika mata takwaran ledar jiya da ya baiwa Aisha, tana budewa taga shigen ta Daddyce ipad taji suna kiranshi.
Ta sa hannu ta karbi kwalin.
"Na gode" ta fada a sanyaye.
"kin san me akeyi dashi?
Cikin jin kunya tace masa "a'a, ina dai ganin irinsa a hannun Daddy"
"To shima kamar komfuta yake, zaki iya shiga yanar gizo sannan yana da abubuwan da aka zuba a ciki don amfanin ki. na sa miki abubuwan karin ilimi a ciki, kasancewa ban cika zama ba zai debe miki kewa idan kika samu wani abunyi. Idan na samu lokaci zan gwada miki yanda zakiyi amfani dashi, an miki setin komai ansa kudi, kafin nan sai ki adana"
"To, na gode"
Zata tashi ne yace "Wai ni Aneesa ni dodon ki ne? Me yasa kike rabe-rabe idan ina wurin?"
Nan da nan idanunta suka raina fata
"Bana son kina yawaita jin tsorona haka, nima mutum ne kamar ki kinji?"
"Eh"
"Shi kenan, ni karfe bakwai zan wuce ofis akwai abubuwan da nake bincike, zan iya dadewa kafin na dawo, idan kina so nayiwa Aisha waya tazo ta tayaki zama, ko kuma ki kira su Khazeena duk wanda ya miki, sai dai bana son yawan surutu kin ji ko?"
"eh, ayiwa Aishan magana idan bata da wani abunyi"
"To ba damuwa. Abu na karshe, idan sun zo su tayaki mayar da kayanki sama daki na hagu daga hawan ki.
"zamuyi in sha Allah."
Bayan fitan shi ne, ta haura sama kofofin nan tabi tana bude su, dakin farko da ta bude komai a kimtse yake kaman sabbin zubi, ga wani kamshi mai kwantar da hankali da ya ta'allaka da dakin, komai mai launin ruwan toka ne, sai dai launin wani abu ya turu fiye da wani abun har ciki ta karasa nan tayi arba da wani makeken ma'adanin kayan sakawa da takalma(walk-in closet), budadde kowanne an jera su a wurin da ya dace, ita Aneesa dai mamakin yawan su da kuma lokacin da aka diba ana jera su takeyi. Nan take ta gane nan ne dakin maigidan, don haka ta juya ta fita ta bude daya dakin shi kuma komai nasa fari ne, ba wani tarukuce a cikin sa nan ma ta fita ta bude dakin da uncle Sagir yace nan ne nata, babban dakine sosai, harda wurin zama mai dauke da kujeru biyu da dan teburi a tsakiyar su, daga bakin wundon dakin kuma wata kujerace ta alfarma wanda mutum za iya kishingida a kai. Komai a ciki ruwan kasa ne mai ratsin ruwan gwal, duk dakunan sun mata kyau sun kuma dace da tsarin mai gidan. A dakin nata ne ta bude har cikin bandaki. Komai gwanin ban sha'awa a cikin bandakin. Tana karewa gidanta kallo ne, taji karar kararrawa a kasa, nan da nan ta sauka ta bude don ta san Aisha ce ta iso.
ESTÁS LEYENDO
Al'amarin Zucci
Romance#13 in romance hot list. 25/1/2017 Still faring high after months of completion. Thank you. A duniyar Aneesa babu abinda ya kai mata Innarta muhimmanci, gashi Innarta ta tura ta birni ta zauna da mutumin da bata taba haduwa dashi ba iya rayuwarta...