BABI NA GOMA

10.1K 648 99
                                    

 BABI NA GOMA

Ups! Gambar ini tidak mengikuti Pedoman Konten kami. Untuk melanjutkan publikasi, hapuslah gambar ini atau unggah gambar lain.

 BABI NA GOMA

Suna zaune a dakin taron da ya kunshi kujerun danyar leda masu jikin karfe mai sulbi wadanda suka zagaye makeken teburi na gilashi mai kwana hudu, teburin ya fiye tsawo maimakon fadi, gaban ko wannen su ruwan sanyi ne da kofuna da kuma lemuna, sannan akwai siraran na'uran magana a gaban kowani mutum da ke da mazauni a wannan teburin, duka mutanen da suke hade a wannan daki su suke murda kambun kamfanin Daggash-Adebayor and sons, wanda yake ciyar da ma'aikata dubbai da suke aiki kasan kamfanonin su da ma'aikatansu a fadin kasar Nijeriya da wajenta.

Idan ka duba fuskokin su gabaki daya zaka fuskanci farin cikin cimma burin su da kuma nasarar warware matsalar da ta sha gaban su. Yayinda zukatansu ke cike da mamakin wanda aka kama da laifin juyar da kudin kamfani da na ma'aikata zuwa wani boyayyen ma'adanar kudi a ketaren kasar.

Bayan taro ya watse kamar kullum Mr. Ahmad da Sagir ne suka saura a dakin taron. "Amma abokina, nayi mamakin gano Dr. Okoli da kayi cikin kankanin lokaci"

"Mr. Ahmad na jinginar da abubuwa da dama kafin na samu gano bakin zaren da taimakon Mr John babban security officer din mu"

"To Amma yaya ka gano shi?"

"Ka tuna lokacin da mukayi shawarar daukar hayar kamfanin binciken kudade da kuma kadarorin sabbin kamfanonin (financial forensics) da duk zamu saya mu dunkule dasu (merger) gudun rikice-rikice?"

"Okay, lallai na tuna"

"Na nemo su ne, muka hada takardunmu da accounts din mu sukayi binciken da zasuyi daga fannin su suna turo min rahoto, bana son na saka mutane da yawa a binciken saboda koma waye ne zai iya yi. Binciken da akayi dai ya nuna mana Dr. okoli yayi amfani da ilimin komfutar sa ne wajen shiga network din mu a matsayin shine akawun wannan kamfani, wato yayi satar hanya (hacking) ta wannan hanya ne a ko wace rana duk kudin cinikin da zasu shiga bankin mu to kason shi suna shiga nashi ma'adanar yayinda a wurin mu zamu ga tamkar kudaden sun shigo mana"

"To amma abun da na gagara ganewa yaya akayi sai yanzu aka fahimci wannan matsalar?"

"Na saka ayi binciken dukka abubuwan da kamfani ta mallakane maimakon nan da wata uku kaman yanda aka saba yi kowani shekara a nan ne Auwal yake shaida min wurin bincike sun gane wata matsala sun samu (glitch) a asusun kamfani."

"To ai Alhamdulillah, tunda Allah ya sa an gane kuma an damka shi a hannun hukuma. congratulations, sai dai na san abokina mun shiga hakkin amarya da yawa, wannan aikin ya taso lokacin da tafi bukatar ka a kusa."

Sagir yayi dariya. Ahmad ya ci gaba "Ai ina ga yanzu kam tunda komai ya zo karshe sai ka dauki hutu haka nan. Daman ka cancanci wannan hutun yanzu na kula wannan shekara ta uku kenan da baka dauki hutu ba ko sau daya"

"Ayyukan ne muna nan ma yaya suka kare..."

Ahmad ya tsayar dashi "wannan karon ba musu, kayi sabon aure, sannan madam ta cancanci ka bata time. Daga gobe ina son naga takardar hutun ka shine magana ta karshe"

Al'amarin ZucciTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang