BABI NA GOMA SHA HUDU
CI GABAN LABARIN
Aneesa dai sun koma makaranta, satin su uku kenan da komawa, amma bata ga wani canji daga Sagir ba. Asalin zancen ma dai wataran sukanyi kwana biyu basu hadu ba, don kafin ta fita daga gida zuwa makaranta ya tashi ko yana wajen motsa jiki ko kuma ya fita. Wataran kuma kafin ya dawo ta riga tayi bacci, tasha ta shirya abinci sai dai ta bawa su Musa a waje. Abun ne ya dameta matuka ta nemi abunyi. Nan ne ta yanke shawarar neman Aadil a waya inda ta nemi ganinshi.
"Amarya bata laifi ko ta kashe dan masu gida." Aadil ya fada yayin da ya zauna a kujerar falon Sagir.
Aneesa tayi kwafa tace "Ni dai ban kashe dan masu gida ba, amma laifina har ya kusa ya karni"
"A'a haba, muna nan wa ya isa ya taba ki?"
"Maganar gaskiya Uncle Aadil akwai abun da nake son na tamabayeka ne ya daure min kai matuka game da abokinka. kuma bani da wanda naga ya dace zai kuma iya warware min wannan tambaya sai kai"
Aadil yayi shiru yana sauraron Aneesa, can ya gyara zama yace "ina jinki kanwata, menene tambayar ki?"
"Don Allah ina son ka fada min tsakanin ka da Allah, shin akwai watace a rayuwar uncle Sagir kafin na shigota?
Tambayar bata bashi mamaki ba tunda ya san taqaddamar da sukayi da Sagir a lokacin da ya fahimci ko Aneesa wacece.
"Sam, babu wannan ni dai a iya sanina ma ya dade bai tunkari wata 'ya mace ba da sunan so tun kafin ya hadu dake ma bare zancen aure"
Tana son ta masa bayanin dalilinta na yi masa wannan tambayar amma bata son tono cikinta don haka tace "To, Amma ba wani abu na rayuwar uncle Sagir da ya dace na sani? A hakikanin gaskiya na san yanda tsakaninka da shi yake kuma hakan yasa na nemi shawararka don haka bazan boye maka ba na janyo wani babban laifi ne, kuma nayi duka iya kokarin naga na shawo kan wannan matsalar na gagara."
Aadil ya gano me take nufi don haka ya amsa mata tambayar da ya sha dambe tsakanin zuciyarsa da kwakwalwarsa wajen furta shi tun ba yau ba.
"Na gane, Aneesa idan har akwai abu guda da yakamata ki sani kuwa to shine Sagir ya taba yin aure!"
A take zuciyar Aneesa ta hau dukan uku-uku, nan take taji tafukan hannunta sunyi zufa, idanunta suka fito ba don kishi ba sai don tsantsan mamakin da amsar Aadil ya haddasa mata.
"Tun yaushe? yaya akayi ba wanda ya sani?"
Aadil ya nisa yace "da dadewa, tun farkon fara aikin sa a matsayin me tsara zane na gine-gine, munje Bauchi dangane da wani aiki a nan suka hadu. Karfin yiwuwar abun ma abokin mu ne ya karfafa shi kasancewar a gidansu Sagir ya ganta. Abu kamar wasa, muna komawa Abuja ba da dadewa ba zance ya kankama, kusan ko wani karshen wata muna Bauchi wurin Ummi. Har Allah yasa akayi auren cikin matukar kaunar junansu"
Aneesa tace "to me ya faru?"
Aadil yace "kin san komai akace da wa'adinsa anyi auren su da wata hudu kowa ya tsinci mummunar labarin mutuwar wannan auren wani abun mamaki shine har yau Sagir bai taba fadawa kowa takamammen dalilin rabuwarsa da Ummi ba. Abun da ya fada kawai shine, bata da lafiya ya bata abin da zata bukata ita da iyayenta don su nema mata magani"
Aneesa tayi shiru cikin alamun damuwa, kafin tace "Na gode uncle Aadil, Allah ya bar zumunci"
"kar ki damu komai zai daidaita in sha Allah, mutumin nawa ne sai a hankali zaman tare da ma sai an hada da hakuri da lallabi, kin san sabon shiga ne, ki bashi lokaci"
Aneesa kwafa tayi a ranta tace wanda ya zauna da matar so na tsawon watanni hudu da wacce bata san meye soyayyar da na miji ba waye sabon shiga a cikin su oho.
YOU ARE READING
Al'amarin Zucci
Romance#13 in romance hot list. 25/1/2017 Still faring high after months of completion. Thank you. A duniyar Aneesa babu abinda ya kai mata Innarta muhimmanci, gashi Innarta ta tura ta birni ta zauna da mutumin da bata taba haduwa dashi ba iya rayuwarta...