Assalamu alaikum, da fatan anyi sallah lafiya. Allah ya karbi ibadunmu ya kuma maimata mana cikin koshin lafiya.
Ga ci caban labarin Aneesa da Sagir, sai dai gwiwana na ta kan sagewa bana jin ra'ayoyinku game da taurarin da ma labarin gabaki daya. 😔
A sha karatu lafiya, ayi tsokaci ni kuma nayi ta turowa akai akai
BABI NA TAKWAS
CIKIN DAKIN TARO A LEGAS
"Amma ta yaya kudade masu tarin yawa haka zasu bata a cikin tsawon watanni biyar kacal, dole a bi duk inda suka shiga a samo su, Auwal ina son ka min magana da John na security office, kowa ya hada duk abun da ya dace bazan bar garin nan ba sai an kaddamar da binciken da za ayi don ganin yanda mukayi wannan sakacin." Sagir ya dubi akawun kamfanin su na kera magani da bada shawarwari kan harkan magunguna, "Kuma ko da wasa bana son hakan ya sake faruwa. Don duk wanda sakacin yake daga gareshi zai iya rasa aikinshi"
Bayan shugaban yayi shiru ne ya bada dama ga sauran daraktocin kamfanin su bada albarkacin bakin su da shawarwari waken shawo kan wannan matsalar.
Sai da suka sallami kowa ne, taro ya watse suka zauna shi da Mr. Ahmed Adebayor suna kara tattauna matsalolin da suka shafi kamfanin nasu.
"Arch. Sagir, wadannan kudadaden ba kanana bane, a tsawon watanni biyar, kana ganin yanda muka bullowa wannan al'amari yayi? Wani amsa zamu bawa investors din mu da kuma wadanda suka amince da aikin mu?"
"Na sani Mr. Ahmad shi yasa nake son nayi maganin wannan abun ta hanyata. duk wanda ya ke wannan aikin (diverting) kudin kamfanin nan, dole yana da wasu hanyoyi na musamman da ya samu hanyar yin hakan, wannan ya nuna min cewa wani mai babban matsayi ne a wannan kamfanin. Don haka wannan mitin da na tara na kira kowa ne saboda duk wanda yake kwashe kudaden nan zai nemi ya rufe takunshi(he will try to cover his moves) wannan zai taimaka mana sosai, da kanshi zai fallasa kanshi zai yi wani dan karamin kuskure, akwai abubuwa uku da nake son na bincika kafin nan".
Suna gama tattaunawa (apartment) dinsa da yake Ikoyi ya koma, sai a lokacin gajiyar ya karasa sauko masa, wanka yayi ya nemi abinci yaci. Sannan ya dauki wayarsa, ya samu missed calls da yawa wasu na kostomomin su ne, wasu kuma abokan sa ne yasan da dama sun kira ne su masa murnar aure. Sai da wannan tunanin ya zo masa ne ya tuna, nan da nan ya nemi lambar wayarta. Amma kaman kullum tana ta ringing ba a dauka ba yaja tsaki "wai me yasa aka kirashi mobile idan ba a tafi da gidanka dashi oho, bakauya kawai." Aisha ya nema ganin suna tare zai fi saukin samunta.
Sun gama shiryawa za a kai Aneesa gidan Sagir ne wayar ta shigo, Aisha ta shigo ta mika mata wayar, tana karba sai da ta tuno sallamar su na jiya, amma kuma sai ta tuno yanda ya tafi ya barta "Yaya hidima? Sun barki kin huta kuwa ko dai suna ta faman miki abubuwan al'adu?"
Duk da tana cikin fushi amma murmushi tayi mai karamin sauti sannan ta toshe bakin wayar ta matsa can kuryar dakin sannan ta ci gaba da magana.
"Ai jama'a rahama ne, yaya aiki?"
A gajiye ya amsa mata "lafiya, don Allah ki tafi ko dakin Hajiya ne ki kulle kiyi bacci idan kika biye musu, haka zaki yi ta fama da ciwon kai"
Taso ta fada masa ran Hajiya ya dan sosu da tafiyar sa amma tayi shiru. shi kuwa a bangarensa tunanin irin artabun da sukayi da Hajiya da taji baya gari yakeyi, akan hakan har tace masa an fasa kai Aneesa sai ya dawo ya dauki matarsa. Da kyar yace tayi hakuri baya son mutane ma su san baya nan wata kila ya juyo washegari da yamma.
"Muna shirin tafiya ne ma yanzu..."
Oh, za a kaita gidan shi ne fa ko? nan take sai yaji wani iri "kuyi hakuri, na kusa kammala abubuwan da suka kawoni, idan akwai wani abu ki nemi Aadil. Me yasa bakwa son rike wayar ku ne a hannu ayi ta neman ku ba a samu?"
VOCÊ ESTÁ LENDO
Al'amarin Zucci
Romance#13 in romance hot list. 25/1/2017 Still faring high after months of completion. Thank you. A duniyar Aneesa babu abinda ya kai mata Innarta muhimmanci, gashi Innarta ta tura ta birni ta zauna da mutumin da bata taba haduwa dashi ba iya rayuwarta...