BABI NA GOMA SHA BIYU
Tana zaune a dakinta idan banda aikin kuka ba abin da takeyi, wanda da shi ta wuni dashi kuma ta kwana, ko kasa bata sauka ba wunin jiya kaf, babban matsalarta daya ba wanda zata iya fadawa kukanta a wannan yanayin. Bugu da kari wanda ya sata a wannan halin bai ma damu da ya san me take ciki ba, wai shi da kanshi ne ma yake fushi da ita. Shin yaya zatayi da rayuwarta ne?
Yana fitowa daga ofis, a mota yake tunanin abunyi, "lallai nayi mata alqawarin shiga cikin wannan magana na kuma warware matsalar Sameeha, saba alqawarin nan kuma ba daidai bane a gareni, idan Aneesa na da aibu ko kuma bata daukeni a matsayin komai ba, hakan ba shi zai sa nima na zama kamarta ba" don haka ne ya dauki hanyar gidan Alhaji Mahmoud, yaci sa'a kuwa ya sameshi a gida.
Mummy ta shigo falo ganin Sagir suna magana da Daddy, kuma bata ga Aneesa ba sai ta raya wa kanta "hmm hali ya auku kenan, ta taba masa wani abun in banda haka me zai kawo shi cikin dare. Indai 'yar Halima ce kam ka kulla da ganin bakin ciki" tayi kwafa ta koma daki.
Suna gama tattaunawa da Daddy ya koma gida, yauma baiga alamar ta sauko ba, don kofar kicin na kulle yanda ya bari da safe. Ranshi a bace ya hau saman, a nan ya sameta a zube a kasan dakinta duk karfinta ya soma karewa.
"Aneesa (you are very stubborn) kin faye taurin kai" dagata yayi ya ajiye a kan gado, idanunta suna neman lumshewa, labbanta duk sun bushe. Da sauri ya koma dakinsa ya hado mata ruwan shayi mai kauri ya dawo dakin. A kan teburin gefen gado ya ajiye sannan ya zuba ruwa a kofi, ya dan sa yatsa ya jika mata labbanta dasu, cikin rashin karfin jiki ta kau da kanta. Haushinta ya kara kama Sagir "ki tashi ki sha tea," ta so yin gardama, don haka ne yace "ki tashi ki sha ko na saba miki, wani irin rashin hankali ne za kiyi kwana biyu ba ci ba sha, so kikeyi ki kashe kanki?"
A hankali ta zauna a kan gadon hawaye na bin fuskarta ta karbi kofin, ita kanta mamaki takeyi da taga har yanzu idanunta suna iya zubda ruwa bayan wanda ta zubar tsakanin jiya da yau.
Yana zaune ta gama sha, ya umurceta da ta shiga tayi wanka ta zo ta kwanta, ba musu haka ta tashi ta shiga. Sannan ya mike ya bar mata dakin, tun daga cikin bandakin sai da taji karar buga kofar. "Yau ni kam nayi babban kuskure na jawo wa kaina damuwa a wurin Uncle Sagir"
**** ***** **** ****
Kwanaki uku da suka wuce ne Sagir yace ta sameshi a dakinsa idan ta kammala, Aneesa ta nufi dakin cikin fargaban laifin da tayi. Amma shigarta ta samu yana bandaki da alama wanka yakeyi don haka ta samu bakin gado ta zauna, can taji karar bude kofa ta ciri kai tace "gani Uncle Sagir" a karo na biyu ta kara cimmashi a yanayin da ta ganshi a Istanbul don haka ta sadda kai da sauri, "Dazu na gama ce miki Uncle ya kare a gidan nan ko?"
"Na manta ne, bazan sake ba" idanunta suna kan yatsun kafarta da suke wasa da kafet . Yana cikin budadden ma'adanar kayan sawan shi ne yace mata "ki cire wannan hijabin ko ki koma dakinki"
A hankali ta cire ta ajiye a gefe, ganinta a zaune, bayan ya juyo ne yasashi murmushi, ba tare da yace mata komai ba ya je gefen gadon shi ya kashe wutar dakin, ya rage guda na gefen gadon. Kallon shi tayi na rashin fahimta ko kuma kin fahimta yace "yanzu kuma kwanciyar ce take saki ciwon jiki ko kuma a zaune kika fi jin dadin bacci?"
"ni bana jin bacci" ta fada a sanyaye,
"Tunda bakya jin bacci je kiyi alwala ki zo muyi nafila. Bata masa gardama ba ta mike ta shiga bandakinsa ta yi kyakkyawar alwala sannan ta fito sukayi sallar. Bayan sun idar ne ya juyo ya rike mata goshi taga yayi addu'a bata ce komai ba har ya kammala, ta mike ta je ta kwanta. Idanunta a rufe ruf, ganin ya kashe wutar dakin sai hankalinta ya kwanta a tunaninta bacci zaiyi amma kuma sai taji Sagir ya shiga yi mata wani salon da yake firgita mata tunani ya hautsina rayuwarta, yake jefa ilahirin jikinta a wani irin tashin hankalin da bai misaltuwa, a nan ta sandare kamar gawa a wannan lokaci idan za a tsaga jikinta kamar baza a samu jini ba don tsabar tsoron da ya shigeta. Tun tana daurewa har ta gagara kore hoton da yake addabarta a kwakwalwarta, hakan yasa ta tattara duk wani karfinta ta hankada Sagir daga jikinta, har sai da yayi baya-baya.
![](https://img.wattpad.com/cover/74226191-288-k101158.jpg)
ESTÁS LEYENDO
Al'amarin Zucci
Romance#13 in romance hot list. 25/1/2017 Still faring high after months of completion. Thank you. A duniyar Aneesa babu abinda ya kai mata Innarta muhimmanci, gashi Innarta ta tura ta birni ta zauna da mutumin da bata taba haduwa dashi ba iya rayuwarta...