BABI NA GOMA SHA TAKWAS
Ana ta shirye-shiryen auren Sameeha da Aadil, don haka Aneesa bata ga ta zama ba, tun da aka shiga satin bikin suke sintirin kasuwa, da shirya kayan da amarya zata yi amfani dasu. Daga ta dawo daga makaranta to aikin kenan, sai da suka gama ne ta samu kanta, saboda amaryar ma kanta ta daina fita. Gashi makarantar ma tayi zafi saboda yanzu saura zango daya su fara zana jarrabawar karshe. Gajiya ce taji tana sauka a jikinta don haka tayi tunanin idan tayi wanka ta dan mike watakila ta warware.
Shigowar Sagir gidan ne ta farka sai dai da wani matsanancin ciwon kai ta tashi don haka ta nemi magani tasha. Tun dawowar shi ya kula da canjin da yake tare da Aneesa
"Lafiya yau na ganki haka? Yau ma kunje kasuwar ne?"
"A'a ai mun gama zuwa kasuwa, kaina ne yake min ciwo tun dazu da na tashi a bacci, amma na sha magani"
"Allah ya sawwaka, kar dai ki sake shan magani haka ba tare da likita ya rubuta miki ba, bari na gama sai muje asibiti a duba ki."
"Nifa lafiyata kalau, ciwon kai kuma ai ba wani ciwo bane face gajiya, da na samu isasshen hutu zai daina, gajiyar sintirin nan ne."
"Tun kafin auren ma kun bi kun daga wa kanku hankali me yasa baza ku gaji ba? ki dai shirya kizo muje ta can zamu je main house mu gaishe su."
Tunda taga ya dage ta san zasu bata ne idan bata shirya ba, saboda haka ta dauko khimar dinta ta sauko.
Asibitin da suke zuwa ya kaita sai da aka dauki temperature dinta aka gwada jininta BP da nauyinta sannan aka mikawa likita file dinta, tare da Sagir suka shiga. Likita ya gama mata tambayoyin da ya kamata sannan yace "Madam zamu rubuta miki gwajin fitsari da na jini gobe sai ki kawo sample a nan lab din mu." Sagir yayi godiya wa likita sannan suka fita "Yanzu me ya sameki da likitan ya ganki, simple abu amma sai kinyi gardama akai" Tana jinsa ya gama fadan sa bata ce masa komai ba, can main house sukayi hira sannan suka koma gida.
Da safe Sagir yace bazata makaranta ba tukun sai ta je gwajin da likita ya rubuta mata don haka asibiti taje da safen. Tana can ne Sameeha ta kirata a waya take shaida mata a ranar za a kai kayan aurenta. Hakan yasa ta nemi Sagir a waya akan tana so ta bi gida idan ta gama da asibiti. "ba damuwa sai ki fadawa malam Hassan din ya kaiki, amma karki dade, kinga ba kya jin dadi"
"to na gode."
Aneesa tana zuwa ta samu Anty Fatima ma ta dawo daga Zaria kenan suka gaisa bai dade ba masu kawo kaya suka iso, sun samu tarba mai kyau, bare Mummy bata son a ga kashinta don haka sosai aka marabce da bakin ranar har 'yan gida nasha-nasha aka wuni, su Khazeena ne kan gaba wajen kallon kaya. Suna tafiya Aneesa ta shiga dakin Sameeha tace "ke kuma kina ina ana ta bidiri, Zaheeda tace ta ga abubuwan da take so duk zata kwashe tunda baki san me aka kawo ba."
"ki rabu da ita, zanyi maganinta."
"A'a me yayi zafi idan nata yazo sai kema ki kwasa. Yaya dai amaryar uncle Aadil abu kamar wasa wai wani sati daurin aure. Da fatan dai yana kula mana dake?"
"Aneesa kenan har sai na fada? ai Uncle Aadil ba daga nan ba"
"Manya iyayen soyayya, Allah ya tabbatar da alheri yasa a yi a gama lafiya"
"Ameen, kinaga Daddy ya soke mana wasu events wai shiri daya kawai za ayi , a tafi Zariya a karasa bikin a can?"
"kema dai dama kina tsamman daddy ne zai yarda da wasu tsirfe tsirfe? a dai yi addu'a koma me za ayi Allah yayi wa auren albarka kawai."
"Ameen, haka Aadil yace."
"Ni kinga zan gudu my dear yace na koma da wuri, kuma kinga gwamma na gama shiri a tsanake kar nayi mantuwa."
YOU ARE READING
Al'amarin Zucci
Romance#13 in romance hot list. 25/1/2017 Still faring high after months of completion. Thank you. A duniyar Aneesa babu abinda ya kai mata Innarta muhimmanci, gashi Innarta ta tura ta birni ta zauna da mutumin da bata taba haduwa dashi ba iya rayuwarta...