BABI NA BAKWAI

9.5K 672 109
                                    

 BABI NA BAKWAI

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

BABI NA BAKWAI

Da yammacin ranar juma'a ne ta sanar da su Mama shirin da baban Uwani yayi na maganar aure.

"Ya tsaida shawarar zai taho da bakin shi nan a daura auren, amma ganin irin bakin nasa bazasu sake ba, yasa nace su daura kawai a can Zaria"

"Ke Halima me ya kaiki shiga maganar, tunda yayi kara saboda a daura a gidan da yarinya ta tashi ai ya gama komai"

"hmm Mama sai kace baki sanshi ba, mutumin da ya kyamaceni da inda na fito me zai sa ya kawo mijin Uwani da dangin sa suzo suma su kyamaceta?"

"Ke dai dadina dake kina da riko, abun da ya wuce ba ya wuce ba?"

Inna Halima jikinta yayi sanyi don Mama ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, saboda haka tayi shiru da manganar, amma ita dai tace tunda ya san 'yarsa yaje can ya daura mata aure, ita addu'arta ma kawai ta wadatar ba sai taje ba.

Malam Habu dai haka suka sata a gaba suna bata baki, daga bisani aka tsaida magana za a zo Kunuwal daurin aure.

"Hajiya, don Allah ki bari haka nan, duk zamu aika musu, su Inna Munira ma sun shirya komai yanda duk wanda aka gayyata bazai samu mishkila ba."

"to ai dole ne mutum ya duba, tunda kinga baza ka tara jama'a kazo kaji kunya ba ko?"

Humaira tace "ho, Hajiya duk farin ciki ne, ni kaman Yaya Sagir ba dan fari ba"

Hajiya bata bata amsa ba, ta nufi falonta inda ta bar wasu baki suna jiranta.

Sagir ne ya shigo dakin yana nemanta Hamdiyya tace "Tana tare da baki a falonta."

"Kai ni fa shi yasa bana son biki-bikin nan, duk a bi a takura mutane mutum da gidansu a hana shi sake"

"Yaya Sagir don kai fa a ka taru a taya ka farin ciki,"

"Naji, ina Azhaan tun shigowata ban gan shi ba na kuma hadu da maman shi a falon Kasa"

"Yaya Kamaal ne ya fita dashi."

Ya nemi bakin gado zai zauna sai yaga kaya "Donn Allah ki kira yaran nan su kwashe kayan nan sai ku bar guri wani iri kaman tashin duniya?"

Hamdiyya ta kula dai kaman akwai abun da yake damun yayan nata don haka ta nemo masa Hajiyar ta samu ya fita ko zasu huta da mita.

Anty Sameera ce ta shigo dakin "lafiya kuwa yau naga Yaya Sagir a birkice, yana tamabayata Azhaan, Kamaal ya dawo dashi amma bai tsaya ta kanshi ba kuma ya fice a gidan"

"oh kema dai kya fada kaman wanda ya zare, haka auren ke razana maza harda irin su Yaya Sagir?" Anty Sameera ta samu kujerar dake gaban gado ta zauna, "kika san ko Antyn naki ce ta razana shi? tunda ai kin san shi ba daga nan ba"

"Anty Sameera kenan, sai kin ganta very innocent, haduwar mu ta farko ta burgeni, bata da wani irin iyayi da eye service, kuma yarinyace wallahi yayi dacen mata tsakaninta da Allah take zama da mutum kuma ta fada maka cikin ta"

Al'amarin ZucciWhere stories live. Discover now