❣❣ ❣❣
❣ ❣👩🏻 *MAYA* 👩🏻
❣❣
❣
3⃣Via O.H.W📚
Neeratlurv.blogspot.co.ke
Wattpad
@ Neerat _lurv
_*ASALINSU*_Alh Aliyu (Daddy) ya kasance asalin d'an,jihar borno a karamar,hukumar(local government)Biu dake gari Maiduguri, su biyu ne rak wajen mahaipansu, wato shi da babban wansa umar, mahaipinsu malam yusuf Manomi sosai, Mahaipiyarsu Zara'u, kuma tana zaman gida Kadai, auren hadin gida akawa malam Yusuf da Zara'u, shekararsu daya da Aure allah ya albarkacesu da samun cikin dansu wato umar, tundaga kan umar kuma,haihuwa ta tsaya musu saida suka d'ebi tsawan shekara 8 kan Allah yasake vasu cikin Aliyu, tun tasowan umar Bai sha'awan makarantar boko yafi sha'awan zuwa gona da mahaipinsu in yadawo kuma yaje makarantar allo, lokacin umar Nada shekara 18yrs shikuma Aliyu Nada,10yrs mahaipinsu ya Rasu sakamakon jinyan da yasha na ciwon kafa, tun bayan rasuwan mahaipinsu umar yakasance shine uba kuma shine Yaya, yana kokari waje baiwa Aliyu tarbiyya uwa uba ilmin boko Dana Arabic, Sam Aliyu baida Matsala irin ta yara tunda yataso, umar yana sa'nar mahaipinsu wato noma, Dan kudin da yake samun inya sayarda kayan su toh dashi yake ciyardasu kuma yake biyan ma Aliyu makarantar boko a Central Yayi primary da nursery while secondary kuma a Day barrack,basu taba kuka dasunan rashiba kullum burin Umar ya farantawa kaninsa da mahaipiyarsu."
"Tun nursery, primary har secondary school Aliyu ya kasance mai kokari da hazaka Sam baida kiwuya yana karatu sosai yasha zuwa quiz (gasa),a makarantu da dama kuma shi yake zuwar musu first position a class ,hakan na matukar burge Yayansa,da mahaipiyarsa, gasada Shiga ran mutane dan yaron akoi natsuwa da hankali."
"Kwanci tashi Ba wuya wajen Allah har Aliyu ya kammala secondary school d'insa da taimakon Allah Dana Yayansa yasami admission a university of Maiduguri (Unimaid) a bangaren public administration shi zai karanta, koda yazo tafiya Umar yahad'amasa kaya irin ta yan gata, Umma mahaipiyarsu ta masa nasihohi sosai kan ya kula da karatunsa yasan mai yaje nema banda abokan banza,banda Neman Mata kuma komin rintsi komin wuya ya kasance kan gaskiyarsa Allah yana tare dashi."sosai nasihan ta shigesa haka ma Ya Umar yatamasa Nasa nasihan, Umar shi yakaisa tashan hawan mota nan yashiga Motan Maiduguri daga nan suka daga sai borno garin shehu, garin kyawawa garin zaman lpy (Home of peace), da sawkarsa Tasha bai wani shawuyaba ya tari taxi yakaisa makaranta wato Unimaid."
"Da isarsa ya wuce hostel nan ya yad'a zango, tun Fara attainding lectures d'insa yan Mata ke kawo Kansu garesa amma shi Sam basa gabansa, haka abokai daga cikin maza ma duk bai kulasu, wasu suce Yana da girman Kai wasu kuma suce dan yanada kyau ne yake yanga,."
"Aliyu ya kasance yana daya daga jerin kyawawan maza yana ajin farko duk da shi (pabir/bura) amma kyaunsa kamar Dan Fulani, akoi tsapta Sam vai son kazanta kullum zaka gansa cikin kayaki masu kyau da haske bai kaskantar da kansa, kuma akoi xuciya,sa'an abin mutum Sam bai burgesa shiyasa kullum yake nisantar kansa da mutane, tunda yaxo akoi wani yaro Mustapha Alibee yake shigemasa Amma Aliyu yaki sakemasa Amma shi mustapha baya damuwa da rashin kulasa da Aliyu yake tun 1st semester yake shigemasa amma sai da zukazo kusan,3rd semester Aliyu ya soma kulashi nan suka kulla abota kullum suna tare har ya kaiga komai nasu yazama daya, Kama daga dressing har sauran abin kamar su natsuwa da halayen Aliyu da mustapha ya koya."
"Shi dai mustapha Alibee ya kasance kanuri ne back and front dinsa, mahaipinsa shararren Dan siyasane kuma sananne a garin Maiduguri da sauran jihohin yana a matakin permanent sectary na gomna a lokacin , mustapha shida kannensa biyu kadai Allah ya mallakawa iyayensu tun tasaowarsu a gidansu suna da tarbiya da son talakawa, mustapha,yayi makarantarsa a FGC Maiduguri,sai kuma yanxu dayake unimaid, shima public admin yake karantawa."
"Rayuwa dai taci gaba da tafiya a kwana a tashi har su Aliyu suka shiga part 2 a university, lokacin ne kuma umar yayi aure ya auri wata Yar biu Itama, hamsatu (Hafsat) sunanta , Aliyu yazo tare da mustapha bikin umar nan ya gabatar da mustapha wa danginsa, sun karramasa sosai kuma yaji dadi, dan koda suka dawo Maiduguri mustapha ya gayawa babansa irin karramawan dasukama dansa shima yaji dadi har yace Aliyu ya dawo gidansa da zama, lokacinda mustapha ya sanar da Aliyu zancen dawo gidansu da farko ya ki saida mustapha yayi da gaske ya yarda hakan ma saida ummansa da Ya umar suka sa baki ya koma".
"Bayan shekaru biyu da auren Umar ya haihu dansa namiji sunan Aliyu yasa ake kiransa da Ali.".
"Lokacin kuma shi Aliyu na part 4 a university suna final year Kansu yadau zafi suna exams".
"A wata laraba ne Aliyu da mustapha suka fita Zuwa coke joint tunda sukaje idon Aliyu yayi tozali da wata kyakyyawan Yar shuwa Arab kallonta ya soma yi har saida ta tsargu da kallon, mustapha yataba yace musty kaga wancan yarinyar ya nunamasa Yar shuwan, Kai wlh Aliyu bakada aiki oya c'mon let's go, kin tafiya yayi yarinka yiwa musty magiya kan yarakasa wajenta, musty ganin abokinsa yanuna damuwa kuma yasan bai taba cewa,yana son mace ba sai yau hakan yasa sa yarda suka je wajenta."
"Da sallamarsu suka je ta amsa musu, bayan sun gabatar da Kansu sukanemi sanin Nata sunan da adreshinta'".
'Fadamusu tayi sunanta Aisha kuma tana karatune anan jami'ar tana karanta business itama tana final year dinta tanazaune da iyayenta a unguwar federal low cost."
"Mustapha ne yasanar da ita mai ke tafe dasu, tayi na'am dasu har tamusu kwatancen gidansu suka rabu kan da dare zasu xo."
"Da dare sun je kuma sun fahimci juna, Tun daga ranan suke zuba soyayya Ba makawa har suka gama makaranta, manya sun shiga maganan su an yanke da zaran sun kammala service za'ayi aure'.
"Bayan shekara daya da gama service baban mustapha yasa momusu aiki mai kyau suna daukan salary mai tsoka, mustapha ma ya hadu da kawar Aisha Nafise yace yana sonta duk an amince."
"Da watansu biyu da dawowa aka daura auren su duka mahaipin mustapha shi ya musu komai har gida ya basu babba kowa danasa part din da mota ya mallakawa kowannensu, Ya Umar ma ba'a barsa a bayava danshima yataka rawar gani "
"Nan kowannensu ya tare gidansa da sabuwar amaryrasa".