8

249 14 0
                                    

❣❣

*_MAYA!🙍🏻‍♀_*

❣❣

1⃣2⃣

Via O.H.W📚
Neeratlurv.blogspot.co.ke
Wattpad
@neerat_lurv

*_Alhamdulillah Tnx for d prayers dearest Naji sauki nakuma ga sakonninku know that Neeratlurv always heart you and she loves y'all ocean and galaxies_*#onelove💞

***
Kashegari da misalin Karfe biyu bayan sallah'n juma'a aka daura auren Aliyu jama'a dayawa ba dama sun hallaci Bikin sabida Aliyu yaron kirkine uwa uba ga Malam Umar shima.

Andan hada walima Wanda yadan kayatar na maza xalla a kofan gida can na hango Nawaz da Makinta Zaune daga dayan bangaren.

Hannu Makinta ya kai yadan taba Nawaz yace "guy what are you staring gabadaya hankalinka is not here. "

Fuskansa ya dauke kamar bada shi Makinta ke maganaba ya wani sha mur cikin ransa kuma yana duba wane ko zai ga small brat dinsa because he wanted to see her again yarinyar tayi tsiwa dayawa kuma kana ganinta kasan shag6abbiya ce shikuma akasari bai son mace mai tsiwa gani yake hauka ke dibansu in suna haka.

Wayar hannunsa yacigaba da dannawa bai ko kula Makinta ba seconds -seconds ya kan dan waiga ko zai yi nasaran ganinta amma da zaran yaga Makinta na kallonsa sai ya wani dauke Kai yana shan kamshi.

Makinta kam ikon Allah yake gani shima banza yayi da Nawaz because inda sabo toh yasaba da Hali irin na Nawaz.

Misalin 8 na dare aka dau amarya zuwa gidan sirikai cikin yan daukar amarya harda Makinta amma banda Nawaz daya kasance cikin mota yana chatting abinsa.

Biki yayi biki kusan kwana uku ana abu daya acikin kwana na hudu ne duk aka watse aka bar yan gida da kadan daga cikin dangi.

Duk cikin kwanakin nan Nawaz na yinsa ne but he really need to be at home and duk iya yinsa nason ganin yasake ganin MAYA bai yiba har yagama hakura.

Yau Monday yakasance misalin Karfe 10 na safe granny dasu Mummy Zaune a falo Maya na daga gefen granny Senator Aliyu suka doka sallama a bakin kofan amsawa akayi nan aka musu izinin shiga.

Shigarsu keda wuya ai Maya na hango Nawaz tayi bayan granny da saurinta tace kaka shine wancan din haka take fada tana sake shigewa jikin granny.

Kallo Kallo kowa yake idan take nunawa su Daddy dasu Malam Umar suka sami waje suka zauna Abban Maya ne yace "Maya ki fita bayan Inna kan na isa wajen."

Kambu! harda kai Umaru Kake son doke ta ko! toh bismillah Inna tafada tana jawo Maya daga bayanta da duk tagama tsorta dan ba kadan ba Marin da Nawaz yamata ya rikitata shiyasa duk take tsoransa.

kusa da Inna ta zauna kamar zata shige jikinta tukun Inna tace "ai ni dama nasan wannan mai jan kunnuwan shi ya doke min jika kuma ai sai na rama mata."

Ba shiri Inna ta Mike tayo kan Nawaz takai masa dundu a baya dan kara ya saki ya Mike nan suka soma xagaye dakin Inna tace dole sai ta sake dukansa shikuma yace A'a su Daddy kam kallonsu suke shikuma Nawaz sai da ya tabbatar ya gama gajar da ita ya kyaleta da kanta ta nemi waje ta zauna tana haki tace "ja'iri yaron "

Tabe baki yayi alamar ko a jikinsa.

Inna tace kai Aliyu yi maza ka dau wannan hege yaron naka ku barmin gida kan ya kasheni da jikata.

Daddy yace toh Inna gobe ma ai sai mu wuce ko.

Da sauri tace ni yau ma ku tafi dariya ta baiwa yan falon yadda ta dage su tafi a yau din.

Nawaz yace "yar tsohuwa kwantar da hankalinki ni ko yanxu ma na iya tafiya."

toh katafi mana dan banza kawai.

Fuskansa ya kwabe yana yatsine wa shi duk ya kagu su bar garinnan Wlh.

Inna kuwa gaisuwa sukayi da ya'yan nata can Daddy yace Maya ba makaranta yau ne ya tambaye ta.

Cike da shagwa6a tace akoi nidai kawai naki zuwa ne yau ta dan turo dan karamin bakinta.

Kajimin 'ya yanxu wasa kike hala baki son karatu infact kina ma jss nawa.

Uhmm ina jss 3 zamuyi junior Waeca term dinnan.

Toh Masha Allah zaki bini birini insaki makarantar yan gayu Daddy ya tambayeta.

ai kuwa da saurinta tace eh kawu zan bika nima nazama irin kulawa ta gidansu ramatu itama can birni taje taxama kamar yar Indian.

Yauwa my daughter zamu tafi tare da ke kinji.

Yeee tafasa ihu tana tsalle cikin jin dadi zata je birni cike da murna ta fice a dakin zata kaiwa su ramatu Labari.

Lalle Aliyu toh fa ba inda xaka kaimin jika Wato Kaje can danka Ya kashemin ita ko.

Mummy da tunda taga Maya yarinyar tashiga mata rai tace "Inna dan Allah kibarmin ita Wlh ba abinda zai samata I promise to take a good care of her."

Tafi can ai bakin ku dayane duk Zakuje ku kashemin jika kawai.

Daddy ne ya sassauta murya yana ta magiya har saida su Malam Umar da Daddy'n Makinta suka sa baki da kyar ta amince nan ma saida Umman Maya tasa baki amma ta gindaya musu sharadi Wlh duk abinda yasami jikarta toh fa basu kwashe da kyau ba suka ce sunji sun amince.

Nawaz da duk haushi yagama cikasa yayi tam kamar zai fashe sai Kallo dayake bin Mummynsa dakuma Daddy dashi zaman falon ne yagama basa haushi Ya fice gaba daya ko ta kansu bai biba.

Maya dai an zaga anata fada kawaye za a tafi Maiduguri gidan kawunta sai murna take ita a dole zata zama yar gayu.

Nawaz ko da yafita gida ya wuce ya kulle kansa a daki da haushi bacci ya daukesa.

Kashegari suka shirya dan tafiya nan fa Inna da Umman Maya suka rungumeta kamar bazasu sake ganin junaba Suna ta kuka
Ali da Abba ba karamin juriya suka yi ba dan yadda suka saba da Maya itama tayi kukan rabuwa da yan uwanta ba kadan ba har saida Mummy tajata jiki ta rinka lallashinta.

Duk wannan abinda ake Nawaz na a mota sai kallonsu yake yana yatsine fuska duk sun cika kunnuwansa da koke2.

Toh fa nan suka dunguma cikin mota suka kama Hanyar borno garin shehu..

*_Vote_*
*_Comment_*
*_Share_*
*_Follow_*
*_Love_*

*_Daga Alkalamin✍_*

*_NEERATLURV😍_*

*_Da_*

*_ABDUL MR SMILE😊_*

MAYAWhere stories live. Discover now