20

438 15 0
                                    

❣❣
  ❣

MAYA!🙍🏻‍♀

❣❣
  ❣

26_28

Via O.H.W📚
neeratlurv.blogspot.com
Wattpad@neerat_lurv

  *Kamar yadda Daddy yafada haka yakasance sabida acikin 3days angama komai kuma suka dawo gidajen sun kayatar masha Allah, Abba baban Maya yarasa wani iri godiya zaima kanisa, Daddy naganin haka yace" karka godemin sabida Kaine silan zamana yadda nake a yau ka sadaukar da farinciknka sabida kamin komai yakai yayana abin sona kuma haryanxu bansan damai zan sakamakaba" rungumesata Abba yayi yana mai farinciki, Inna harda guntun hawayen farinciki, Ali ma yanuna nasa farincikin wajen godewa kawunsa kuma takwaransa...
  
  Daddy yasake bajinta wajen budewa yayan nasa babban masana'antar saida kayan shuka saikuma Ali daya budemasa babban provision shop a milk shop  bayan kyautar motoci dayamusu masu tsada da kyau yabaiwa matarsa da umma jarin dubu Dari uku-uku suyi Sana'a, ba a bar Momi a bayaba domin ta taka rawar gani wajen hadamusu turaruka da humra na mutan borno, ansamo wata dattijuwa daza suna zama da inna anata bangaren. Domin gidane guda biyu saidai kowa da gate dinsa amma zaka iya Shiga ta baya akoi karamin kofa dazai sadaka da gidajen juna...

  Yau tun wuri Daddy yace wa Momi su shirya bayan sallah'n magrib zasu gaida su inna sabida tun zuwansu Maya bata saniba amma yace kar a sanar da ita it's a surprise yake son mata..

7:00pm daidai suka bar gida bayan Maya ansha wanka cikin wani material dinkin dogon riga tayi rolling gyale sai Dan karamin side bag dinta tayi kyau sai kamshin oud na larabawa take Momi akoi kokari wajen kamshi shiyasa Dan zaman Maya da ita Maya tazama mayyar son kamshi itama.

  Da isansu mai gadi ya hanagame musu gate na gidan cikin jerin Inda aka tanadar Dan ajiye motoci Daddy yayi parking suka fita bayan ya gaisa da mai gadi suka nufi ciki, isarsu kowa ya hallara a falon inna ana hira daga sallama Maya bata hango kowa sai inna tayi jikinta da gudu inna tana ta ihu da kiran sunanta nayi kewarki amma naji dadin ganinki ire iren abinda taketa fada kenan saida Ali yayanta yadaka mata tsawa tadawo hayyacinta nan tayi arba da iyayenta ta tafi garesu suma tanata murna, nan aka gaggaisa aka shiga hira anan ne Maya taji abinda Daddy yawa iyayenta itama ta daura nata godiyan, umma taji dadin ganin yarta cikin koshin lpy dakuma Karin wayewa taji dadi matuka har takasa boyewa Momi saida tamata godiya itama sosai bisa yadda take kulamata da tilon yarta..

   Dare sosai suka tafi gida bayan darun da aka sha da Maya kan sai ta xauna anan da kyar da sudin goshi Daddy yashawo kanta bayan yamata alkawarin nan da 3dayz zai kawota su kwana nan ta sake suka dunguma xuwa gida...

Command guest inn....

  Misalin 10 na dare wajen ne da ake club bakajin komai idan ba karan kida dake tashi a wajen ba saikuma idan ka duba wasu gefe ka hango wasu  na zukar taba, wasu wiwi,wasu shisha wasu giya suke sha kowa dai da abinda yake yi wajen wani squad na hango na matasa guda hudu nan natabo Mr smile namasa alaman muje dauko rahoto yadan fidda ido yace" kai neerat anya kuwa" nace muje dai nakega kamar Nawaz ne kasan akoisa da son chasu dariya Mr smile yayi yasoma tafiya ina biye dashi, nan muka garzaya zuwa wajen...

   Nawaz ne sai makinta, Abdul dakuma Sadiq su hudu ke zaune gabansu wani tebur ne cike da nau'in juices kala2  hade dasu chamgpane sai manyan pot na shisha guda biyu Wanda suke anfani dashi.

  Nawaz yace"guys kunji yadda mukayi da Daddy kuma yau almost 4days kenan bamu haduba banama kwana gidan."

  Numfasawa Abdul yayi yace"gaskiya this is a big issue wannan Abu kamar shirin film just imagine kamar ka amaka auren dole gaskiya gaye kafado.

  Mtsww! Nawaz yaja tsaki yace nifa kaga dadina da kai kenan shawara na ke nema musan yadda zamuyi amma kake mana wani surutun damn it yadan zuki hayakin shisha ya fexar".

  Makinta yace"calm down dude ai yanxun we are looking for d solution amma ni fa gaskiya na sare I have no option than nacemaka kabar wannan abun kawai kasan Daddy maganar sa kaifi dayane ba canzawa kuma nima old man dina yace nan da 1months idan ban kawo mataba he's willing ya auramin duk wacce yakeso."

  "Fuck you guys! Dukanku you're no use tunda bakuda solution.."

Sadiq da tunda suka soma magana bai sa bakiba yasoma da cewa" pal! Kasan wani Abu ni a ganina you shud b patience kawai ka karbi auren tunda har yabaka choice na gaba ka auro duk wacce tamaka kaga it's simple ka auri yarinyar kawai kuma beside ba out sider bace she's your cousin sis kasanta kumafa gidankuma daya nasan ba matsala..

  "You shot up kaga yarinyar ne *kwaila* CE fa she's no use batada komai I think idan banyi karyaba yanxune mafa take ss1 a secondary skul meye zanyi da ita ae abun kunyane idan aka ganni da ita matsayin mata da miji mtsww God save me yafada cikin daga murya."

  Sadiq yasake cewa " ita *kwailar* ba mace bace kuma wlh Dan baka sonta ne amma ae na tabbata da kana sonta baxaka ga kwailancin bama, kumafa baka San wani Abu ba wlh auren yaran wani lokaci yanada fa'ida sosai kai zaka tankwarata ta yadda kakeso duk yadda kayi da ita tahaka zaku tafi zakafi more soyewa da ita wlh am telling idan ka auri yarinyar nan watarana da kanka zakabamu lbrn yadda kakesonta harkaxo kanamana kukan dadi yakarasa mganarsa cike da shakiyanci."

  Kaifa Dan rainin sense ne nine zanso wata yarinya har nayi kuka a kanta Allah ya kiyaye wlh."

  Ganin basuda yadda zasuyi a karshe kawai suka hakura ayi auren kawai, amma cikin ran Nawaz kuma ya kudiri zai gasamata aya a hannunta harsaita nemi yasake ta da kanta wani shu'umin murmushi yayi a ransa shi kadai yasan mai ya tanadar mata....

   Washegari....

Misalin 10 na safe Daddy yaxo fita kenan Nawaz yashigo harabar gidan, Daddy na tsaye bai shiga mortar ba, Nawaz na parking yafito ganin kallon da Daddy yakemasa yasasa karasawa yana Sosa keya ya Dan runsuna yace "Daddy good morning", bai amsamasa illa wucewa dayayi yace " follow me", Daddy natafe Nawaz na bayansa har suka shiga falonsa yayi daidai da lokacinda Momi take kokarin saukowa da beni itama zuwa tayi ta xauna tace" my dear baka tafiba Ashe" dan murmushi Daddy yace "eh na hadu da dankine nace bari mushigo zamuyi magana kema ki xauna", kallonsa Daddy yayi mai kyau kusan 2mins kafin yace" wato Nawaz baka daukeni da muhimmaci ba kadaukemu a bakin komai ba bamusamin darajar iyayeba shiyasa naga kusan kwana biyar baka nememuba, kayi kokari nidai ba abinda zan fadamaka kaje kasoma shirye-shirye sati mai zuwa aurenka kuma  daga yau dinnan kasa afara gyran gidan da zaka aje matarka Abu na karshe kaje ka gaida mahaifan yarinyar nan ka iya zuwa wajen mahaifiyarka Tabaka address nasu, yana kaiwa nan yamike yafita..

  Momi ma ko kallon Inda yake batayiba tamike tace zanbada akaima address din idan na rubutamaka daga haka tayi wucewarta itama....

  Kusan suman zaune yayi ganin yadda iyayensa suka sauyamasa ciza Dan lebbensa yayi yace gaskiya da sake dole na nemo mafita...

  Ansa driver yakai Maya gidansu akan zatayi 2 days..

    Nawaz yaje ya gaidasu sunyi murna suka tarbesa cikin mutunci yadan sake jiki dasu shidasu makinta sukaje kuma basu hadu da Maya ba..

  Daddy yaji dadi yadda Nawaz yabi maganarsa Dan hka ne ma yadan sauko yake jen Nawaz jiki.

  Kuma shima Nawaz yabaiwa iyayensa hakuri bisa batamusu dayayi Yakuma Nuna zai krbi auren yabi zabinsu yadan sake dasu shima amma duk wannan abun Maya batada masaniya akai.....

Daga Alkalamin✍

NEERATLURV😍

      Da

Abdul Mr Smile😊

MAYAWhere stories live. Discover now