13

292 17 2
                                    

❣❣

*_MAYA!🙍🏻‍♀_*

❣❣

1⃣7⃣

Via O.H.W📚

neeratlurv.blogspot.co.ke
Wattpad
@neerat__lurv


*After one week*

Komai na tafi daidai, Maya na xuwq skul kuma sosai ta maida hankalinta take fahimtar abinda ake koyar da ita, yanxu har lesson teacher aka samomata har gida yake xuwa byan sallahn isha ya mata gashikuma ansata islamiyya 3 take tafiya idan ta dawo daga makaranta sai 5:30 kuma ta dawo.

Daga dayan gefen kuma Nawaz yana sha'aninsa har yanxu ba wani jituwa tsakaninsa da Maya, Tsakaninsa da Zee kuma sai abinda yayi gaba kusan yanxu kullum suna tare, Zee na matukar sonsa da kishinsa kuma Zee yar barikice sosai shiyasa tasamo kan Nawaz a dan kankanin lokaci amma duk da haka bai sakemata ta rainasa ba yanan miskilinsa har yanxu, kudi kam yana mata barinsu.

Yau kamar kullum karfe 8 da rabi na dare Momi da Maya zaune suna kallon wani indian Film, sosai Maya ta maida hankalinta kan wayarta datake chatting dashi jefa2 takan daga kai ta kalli tv sai ta dauke suna a haka sallamr Nawaz ya daki kunnun wansu, Momi ce kadai ta daga kai ta kallesa shaye da toka ta amsa masa sallamarta sa.

Yana murmushi yakarasa kusa da Mom dintasa yasami wuri ya zauna kansa ya daura cinyarta yace "ina wuni Mom" Momi dake shafa gashin kansa tadan mintsinesa kad'an tace " naki na amsa sai yau ka gadaman xuwa gaidani muna gida daya amma ta karashe maganar tana ture kansa dake cinyarta" dan marairaicewa yayi yan rike da dukka kunnuwansa biyu yace " Mommah am sorry i will never repeat it again" pointed nose dinsa taja tace "kullum haka kake cewa sai kayi abu kace you will never repeat that again but you keep repeating it how on earth do you want me to belief baxaka sake ba.this time around Momi na magan sounding serious" Ganin yadda Mom ta dau zafi yasa sa sassauta murya cikin sweet and husky voice dinsa yace " Mom belief me this time around i mean it zan canza insha Allah just keep praying yakarasa maganar with puppy face" Mom na ganin haka ta ji ta yarda da dan nata amma ta dake tasake cema.

"pls Abuu (Babana) ka canza kafa gani duk ka girma kazama tuzuru ba mace you are now 33 getting to 34 yrs amma ka kasa girma nidai kawai kayi ka yi aure ko zaka canza."

Dariya yasoma yace " Mom nace zan canza amma ki bar maganar auren nan yanxu ban shirya ba yafada yana tamke fuska." Ya zanyi ni Aeeshatu naji Mom ce tayi maganar, sai a sannan Momi ta juya taga Maya dake danna Waya kamar bata san suna wajenba amma kusan duk hiransu taji saidai bata daga ta kallesu ba Momi tace " Mamana baki ga yayanki bane bazaki gaidasa bane.

Dan hade rai tayi sa'annan tayi rau-rau da idonta fuskarta kamar mai shirin kuka da kyar ta ce " ina wuni ba tare da ta kalli direction dinsa ba."

Shima bai damu ba amma cikin ransa ya ce " kutt! Wannan yarinyar da raini take amma xanyi medicine dinta, fakan idon Momi yayi ya watsa Maya kallon zamu hadu dake ne, ciki2 ya masata da "lpy".

Nawaz kallon Momi yayi yana shafa cikinsa yace " Momi am starving fah" harara ta watsamasa tace bamuyi girki da kaiba.

Cikin shagawaba yace "haba Mom son dinkine fa kike cewa baki dafa abinci dashi ba nifa na kula Momi tunda yarinyar nan ta dawo ki soma shareni"

Toh sarkin iya magana na shareka din ai baka abin kirki shiyasa Momi tayi maganar tana wurga masa harara.

Tsam ya mike yace " Momi pls yarki ta kaimin abinci part dina yanagama maganar yayi ficewarsa yanufi part din nasa.

Maya da Momi tace ta hadawa Nawaz abinci ta kaimasa kamar takurma ihu take ji amma ba hali haka ta wuce kitchen ta dauko tray taxo ta hadamasa abincin rice and stew da koslo saikuma kaza da akawa gashi yaji kayan hadi da coconut juice.

A bakin kofan ta tsaya kamar bazata shigaba can ta daure ta tura kofan falon a hankali take tafiya kamar wacce koi yafashe wa a haka har ta kai tsakiyar falon taga ba kowa dinning spacd dinsa ta nufa da saurinta ta jibge abinci tajuya tana sauri ta wuce har ta kai bakin kofa taji ance " ke!" tsaya wa tayi ba tare da tajuyaba dan tagane muryansa.

shikuma kin juya warta bai damesa har ya sami waje ya xauna cikin shigan 3qtr da shirt laptop dinsa daya dire a gabansa yasoma butting dinsa, ta kusan 3 mins a tasaye ganin ba sarki sai Allah yasata juyawa a sanyaye ta iso wajensa tace " gani".

Dauke kai yayi yakuma yi kunnen uwar shegu kmr bai jita ba sun dau minti biyar a haka ganin tagaji da tsayawa tasake cewa "Ya Nawaz ganifa" runtse idanu yayi yabude soma magana cikin voice dinsa dayake tunin fada yake amma wajen mai sauraro sam hakan ya bambanta.

"Ae ai na ganki kuma bance banda ido ba and kuma najiki zo nan yace yana nunamata gabansa"

Ba musu ta karasa hade da tsunkuyawa kanta a kasa, rankwashi taji mai dan karen zafi tsakiyar kanta wanda har sai da idonta yakawo ruwa a sanyaye ta daga idonta karaf cikin nasa idon yana jifanta da wani irin kallo wanda ta tsana, saurin dauke nata idon tayi ta dukar da kanta kasa tana fidgetting fingers dinta. Kallonta yake yana nazari can yace jeki kiyi serving dina abinci, mikewa tayi duk jikinta na rawa takarasa dinning tahada masa komai ta kawomasa ta ajiye a gabansa. Saida yagama yanga ya ja abincin ya soma ci duk abinda yake Haryanxu Maya na a zaune bai bata ixinin tafiyaba ya dau kusan rabin awa yana cin abincin a yanga ce har ya kammala "Ke" yasake cewa dago ido tayi da hannu yama nuni da ta kwashe abin gabansa.

Ba musu tayi yadda yace ta hada kwanukan ta dau tray din tazo tafi yace " who permit you to leave go back my friend" Jikinta a sanyaye ta koma ta xauna can yadan dibi lokaci yasoma magana yace "wato ke gaki kin raina mutane ko kina gaidani kina min kallon raini ko toh zaki gane kurenki oya yanxunan before the blink of an eye ki tashi kisoma sharemin daki ki goge ko ina ki wanke toilet ina daga balcony ina jiranki and wlh idan nazo naga sabanin yadda nake so i swear sai kin sake kazama kawai bacemin daga nan.

Jiki a muce ta mike tanufi bedroom dinsa komai a gyra yake bata san mak zata gyraba kuma gashi yanxu karfe tara na dare kuma yace tayi shara, ta jima a tsaye ganin tsayuwar bazai ficeta ba tasoma kakkabe kan godon tasoma gyra, Maya tasha wahala sosai ta jigata sabida sai da ta kusan lashe 2 hours tana sake tsabtace wajen hatta kitchen Saida tayi gyra tayi goge goge bunner ta dauka tasa turaren wuta takuma feshe ko ina da room freshner.

A balcony ta samesa lokacin har 11:40 na dare yayi, yana aikin danne2 a laptop tana iso sa tace "Yaya na gama" da kamar bazai amsataba yace " naji lemme go and check tukunna yafadi hakan yana mikewa" ko ina ya duba yaga fes ga kamshi ta ko ina can cikn zuciyarsa yace " perfect" amma a fili ya dake yace "ke haka ake gyra daki a garinku stupid next time kisake min irin wannan gyran ki gani yana murde kunnuwanta yake maganar har saida tace "Auchhh! Pls you are hurting me it pain" sake murdewa yayi yasaketa yace "you can go now" da sauri2 tafice tabar part dinsa idonta tab da hawaye cikin ranta kuma ba abinda take inbanda jamasa Allah ya isa da take haka ta zo ta tara da falon tsitt ba Momi dan Momi dataga bata dawo ba tana jin bacci kawai takashe tvn tayi shigewarta daki .

Kitchen ta nufa ta ejiye kwanunkan ta wuce daki direct toilet tafada tayi wanka tazo ta shirya cikin kayan bacci nan ta kwanta nanda nan bacci ya dauketa...... _wannan keanan_

_This is just d beginning ku kasance da mu dan bibbiyar labarin Maya_

*_Daga Alkalamin✍_*

*_NEERATLURV😍_*

*_DA_*

*_ABDUL MR SMILE😊_*

#Vote
#Comment
#Share
#Love

#onelove💞

MAYAWhere stories live. Discover now