16

244 12 0
                                    

2018

❣❣

*MAYA!🙍🏻‍♀*

❣❣

2⃣0⃣

Via O.H.W📚
neeratlurv.blogspot.co.ke

Wattpad
@neerat_lurv

**Kwanaki biyu tayi a asibitin aka sallamota suka dunguma zuwa gida"

Jikinta Alhamdullilah ta mulmule ciwon ciki na nan saidai shima Ba sosai Ba Dan tana shan magunguna ga allura dayake taimakawa wajen danne ciwon cikin"

Saida ta share 1week lokacin jinin ya tafi kan tafara xuwa skul.

Yau ta tashi da murnanta sabida xuwan Inna da ake tsammani a yau, ta daga hankalinta tun sanda Daddy yace Maya bataji dadiba take sababi wai sai ta zo ta duba jikallenta shine Daddy ya akai driver yaje ya daukota .

Tun jiya Maya ke faman kai da komo a kitchen tana hadawa tsohuwa kayan kwadayi daidai Wanda xata iya ci tayi su samosa, meat pie, dasu spring rolls, cokies da Momi ta koyar da ita.

Saida ta hada komai ta shirya xuwa skul har taso tayi letti Dan pass 7 kuma yau Short day 12:30 zasu tashi sabida jumma'a.

Sanye take da uniform dinta Masu kyau da Dan karamin ash hijab dinta iya kafada tayi kyau matuka bayanta rataye da wata tsadaddiyar bag Golden littafaine ta rikesu a hannunta irin dogayen nan, A hankali take takunta mai matukar daukan hankali, yana daga balcony yana zaune waya ne hannunsa yana danne2 kamar ance yadago kansa ya hangota kasa dauke idonsa yayi kanta cikin ransa kuma fadi yake"
_Bai taba ganin mace datake tafiya cikn natsuwa wacce ta iya taku a hankali kamar Maya ba_"

Yana cikin kallonta ta juyo da fuskarta wow! Yafada a hankali she looks cute this morning bai San sanda ya seta camera yasoma daukarta pics ba itakuma tana cikin gaisawa da mai Bawa flower ruwa Saida ya dauka kusan kala biyar ya janye wayar ganin kamar zata juya yacigaba da duba wayansa, sarai ta gansa itama ta maxge kamar bata gansaba ta kwaye ta shige mota driver yaja suka bar gidan sai skul."

Suna tafiya Nawaz ya fiddo wayansa yashiga duba pics din Saida ya duba yaja Dan karamin tsuka yana mai jin haushin kansa na daukanta pics amma on the other side of him ya tsinci Kansa yana mai jin Dadi hade da murmushi Wanda bai San daliliba.

****

12:40 dai dai Maya ta iso gida fully happy to see her Granny ko tsayawa rufe murfin Mota batayiba ta ruga guje tayi cikin gida tana ta faman kiran Innata! Innata!!, a falo ta cimmasu suna zazzaune ana hira Momi,Daddy da Granny banda Nawaz da inkacire sa yana wajen amma kallon kawai yake bai ko kallon direction dinsu, jin irin ihu da take ta faman kwalla na kiran innarta yasasa dakamata wata tsawa yace

"Would you shut up your mouth kin bi kin cikama mutane kunne da ihun ki mara dadin ji."

Ae karab Inna ta karba da cewa

"Yo kaidin muryanka Nada dadin saurarone ae gwamma nata akan naka kuma har yanxu kana nan da mugun halin nan naka kana kuma takura jikalleta ko ae na cinmaka kuma zanyi maganinka"

tana ta sababi shi ko kallonta bayayi har ta gama surutun tsaki yaja yana sake tamke fuska, Inna ta harxuka tace "kayima uwarka Aeesha tsakin kuma idan Baka yi bakinka yayi tsayiba toh Baja kaiba tsaka kawai."

Tun da Maya ta shigo take haki ganin irin tsawa da Nawaz yadakamata yasata rakube gefe guda tana tsoronsa dan tasan muguntarsa.

Daddy da Momi kam ido kawai suka bisu dashi, Inna ne ta tashi ta isa Inda Maya take ta rungumeta jikinta tana fadin daman nasan wannan bakin mugun yana nan da bakin halinsa baxai canxaba tajata zuwa inda take zaune ta zaunar da ita lafewa Maya tayi jikin inna tana gaidata cikin shagwa6a itakuma inna sai biyemata take Sundau tsawon lokaci haka kafin ta tashi tashige daki tayo wanka ta sauya kayanta xuwa Riga da wando na jeans da wata doguwar Riga kirar Indian dress iyaka guiwarta.

Tundaxu Nawaz yabar falon dama Daddy kuma yafita zuwa sallah'n jumma'a sai karfe biyu suka shigo Daddy da Nawaz din suna zama bada jimawaba Makinta da iyayensa suka shigo nan waje ya kaure da hira inna abin nema ya samu sai xuba hira anci ansha sai kusan maghriba iyayen Makinta suka wuce gida bayan inna tace ran Sunday zataje gidan Nasu su yini itama.....

*_Daga Alkalamin ✍_*

NEERATLURV😍

*DA*

ABDUL MR SMILE😊

#vote

#Share

#Comment
#Love

# *One Love💞*

MAYAWhere stories live. Discover now