❣❣
❣MAYA!🙍🏻♀
❣❣
❣29_30
Via O.H.W📚
Neeratlurv.blogspot. com
Wattpad @neerat_lurv*_Here is a page of honour to you Mhiz Hajjorh all though I don't dedicated a page boh you deserve to have this babe kinfi kowa son littafin Maya a duniyar WhatsApp tnx xo much durling, comments dinki da kaunar Maya nakaramana karfin guiwa wajen typing heart❤ you babe..._*
Dan bata fuska tayi tana yamutsa sa tace."Momi ni wlh bana son wannan abun da kike bani bayida wani dadi duk yabi yabatamin test na bakina tafada tana sake yamutsa fuska."
Dariya Momi tayi tace"ae dole nabaki sabida inason gyra 'yata ne kuma wlh idan kika ki sha saina miki dure ehen tafada in a serious tongue."
Daukan cup dinda aka ajemata kayan tsimin aciki tayi takafa a bakinta harda runtse ido ta shanye tana yarfa hannu ita dole taji abin namata bauri lol.
Good of you Momi tace sannan tasake cewa sai ki tashi kiwuce can wajen mai gyran jiki tasoma nata aikin daga haka Momi tafice ta barta..
Baki ta Chuna shi gaba tana gunguni itafa tarasa ganewa tun shekaran jiya daga dawowanta gidansu aka soma dirkamata kayan tsimi gakuma wata shuwa Arab dakemata dilka d gyran jiki koma meye ne ita zata fadawa Momi tadaina bata wannan abin gaskiya da haka tafice ta wuce zuwa Inda aka ware don gyran jikinta...
Karfe uku daidai yayiwa Momi da kawayenta saikuma yan uwanta sunkai su goma a gidansu Maya, akwatuna ne aketa faman Shiga dasu saidai aka shigar da side 24 a tsakiyar falon inna kamin daga bisani suka zazzauna aka soma budewa kayane nagani nafada aka zuba a cikin kowani akwatin mussaman Momi ta aika Dubai akamat sayyayen tsayawa fayyacemuku abinda ke cikin akwatin bata lokacine amma Kaya alhamdullilah ko yar governor albarka, antarbesu cikin mutunci nan aka basu tukuici mai tsoka umma harda kukan farinciki saida tayi anan aka bar kayan Momi taki tafiya dasu acewarta wajen mahaifanta yakamata kayan su zauna..
Koda Abba yaga kayan yayi matukar farinciki amma duk da haka saida yakira Momi yamata surutun bata kudi datayi wajen zabga kayayyaki haka tanunamasa ai yiwa kaine kuma karyamanta auren tilon danta ne dole tanuna bajinta bugu da kari gakuma 'yarta..
Washegari da wuri sadiya taxo Dan Momi har gidansu taje taroki abarmata sadiya harzuwa bayan auren dan debewa Maya kewa,kuma alhamdulillah iyayenta sun amince, nan Momi tabata anko rabawa sauran frnds dinsu su hudu da ita Biyar tarabamusu...
Maya na kwance bisa lallausan gadonta sadiya tashigo ta hangota kudundume cikin blanket tana sharan barci abinta hannunta rike da cup da Momi tabata ta kaiwa Maya ta shanye abin ciki, duka ta nadamata da sauri Maya tabude idonta tana kaikaya wajen da dukan yataba Dan yashiga, ganin sadiya tayi saurin cewa"You" ta dira daga gadon tana kokarin kaimata duka ajiye cupin hannunta tayi suka soma guje2 da
Kyar Maya ta cinmata takaimata duka daya nan suka zube suna haki, saida suka Dan huta Maya tace."Babe yaushe kikaxo ne?"
"Bansaniba sadiya tafada tana murkuda baki"." maida wukar kiyi hkr tawan kinji tafada cikin sigar lallami."
"Hmmm kinwani zo kina bacci har sha dayan rana ina zakisan xuwana any way na hkra and ga wancan cup din Momi tace inbaki and I should make sure kinshanye abin ciki."
"Ido Maya tadan waro waje tace haba tawan kidai rufamin asiri naxubar saikice na shanye."
"La! Yarinyar nan bakida hankali ni zanwani rufamiki asiri toh badaniba is better ki shanye kafin nakira Momi."
Tana hararan sadiya tashige ta wanko bakinta ta dawo ta shanye tana yamutsa face kamar yadda tasaba...
Nifa narasa meyasa ake tamin abubuwa strange Maya tafada tana kallon sadiya ko zatasami amsa,uhmmm wayasan dalili sadiya tafada in an I don't care tongue takara da cewa kitashi kishirya Momi tace Abbanki nakiranki a falon Daddy, tana mita ta Shiga ta shirya tafito tacemata sai ta dawo.
Da da fadinwan gaba tashiga tayi sallama ta hango Daddy da Abbanta sai Momi,Ummanta da Nawaz dake gefe gakuma inna, gabadaya aka amsamata sallaman banda Nawaz da ko dago kai baiyiba, hartasamin waje ta zauna Daddy yayi gyran murya ya bude taro da addu'a yasoma magana kamar haka.
"Yace gabadaya munsan mai ya taramu anan mussaman kai Nawaz kasan komai saidai ita mamata dabata da masaniya yajuyo da kallonsa zuwa wajen Maya yace.
" Fadimatu Zarah!"
Gabanta ne yafadi jin yadda Daddy yakira sunanta gabadaya abinda ba a cika kiranta da sunan ba,tattaro natsuwanta tayi tace "Na'am Daddy"
Yasake cewa"kinsan muna sonki ko? Kuma kinsan bazamu so abinda zai cutar dakeba ko?".
Nanma courage tayi gathering tace "eh Daddy".
"Yace alhamdulillah da kika san haka"Kallon su inna yayi gaba daya Abba ya girgiza masa kai alamun yafada yace .
"Daughter nasan baxaki watsamana kasa a idoba kuma nasan ke mai biyayyace duk abinda muka yanke hukunci akai nasan ke mai karbane kuma kin yarda da kaddara ko"
"Eh insha Allah ni mai karban kaddara CE aduk yadda zai zomin kuma zan kasance mai muku biyayya."
"Madallah Daddy yace daga bisani yace wannan taron dominki akayi daughter badon komaiba sai sabida aurenki da Nawaz yayanki da aka yanke ranar juma'a insha Allah nasan ba dadi saidai bisa wani dalilin ne mukayi haka bawai don son zuciyaba saidan inganta rayuwarku ke dashi ina fatan kin karba hannun bibbiyu."
Tunda akace aurenta da Nawaz komai na jikinta yadaina aiki sankarewa tayi a zuciyarta tace chab wannan Wanda na tsanesa shima ya tsaneni shine za'a wani yimana aure gaskiya da sake tana cikin wannan tunanin ne taji hawaye yasoma wanke mata fuska dago fuskarta tayi takalli saitin mahaifanta saitaga idanunsu yana mata nuni da sunyi na'am da zance tasake waigawa taga Momi da Daddy suma tatuna irin hallacinsu gareta muryanta narawa tana hawaye tace" Daddy Allah yasa hakan shine nafi alhairi" tana fadin haka ta tashi da gudu tabar falon tana sheshekan kuka daki tawuce tafada gado tana kuka mai tsuma zuciya sadiya kuma sai akin rarrashi tunda tasan baxaiwuce maganar aurentaba.
Can kuma falon hamdallah sukayi Daddy yace su Momi suje du rarrasheta, suna fita inna ta kalli Nawaz tace.
"Toh sarkin yan girman kai ko nace tsaka dan kafi karfi tanan wlh karkaga anbaka jikalleta a bulus kace zaka wulakantamin ita Dan rufamaka asiri tayi kasan tafi karfinka kuma wlh wani Abu yasameta kayi kuka da kanka dan kotu kadai zai rabamuku dakai mugu kawai mai zuciyar fir'auna mutum kullum cikin daure fuska da girman kai nidan anfi karfina ne inbahakaba bakai ba jikata haka tayita mita daga karshe ta tashi tayi wucewarta...Nasiha sosai su Daddy sukawa Nawaz nagame da rike amanar Maya Dana aurensu kamar da gaske ya amsa yana godiya yamike yafita cikin ransa kuma yasake kallubalantar Maya dasake shiri kan irin bakar wuyanda zaibata...
Duk su inna da su Momi sun dukufa wajen ganin Maya tayi hkr dakuma tsagaita kukanta amma ina akarshe saida akabarta da inna nan ne inna tayiya kwantar mata da hankali har tadan sake kadan..
Wannan Kennan......
Daga Alkalamin✍
NEERATLURV😍
Da
ABDUL MR SMILE😊