15

286 18 1
                                    

❣❣

*MAYA!🙍🏻‍♀*

❣❣

1⃣9⃣

Via O.H.W📚
neeratlurv.blogspot.com
Wattpad
@Neerat__lurv

**Speed yakara sai gudu yake xabgawa, Ba abinda Momi take sai kuka tana rike da Maya, Daddy kuma sai addu'a yake kar Allah yasa yarinyar nan mutuwa tayi.

Allah kadai yakaisu hospital din dan irin gudu da Nawaz yake xabgawa, suna isa tundaga gate yarinka zabga horn tiiit! Kake ji.

Nurse! Nurse!! Nawaz ne keta faman kwalla nurses kira da saurin su suka karaso da gadon tura marasa lpy.

A guje suke tura gadon direct A/E ward akayi da ita likitocin wajen ne suka dukufa kanta domin ceto ranta.

Daddy yakasa zama yakasa tsaye haka wajen Momi, Nawaz na ganin ikon Allah duk da dakakkiyar zuciya irin ta Nawaz saida yaji ba dadi ganin yadda iyayensa suka tada hankulansu.

Mintuna sunfi talatin likitoci suka d'iba kafin suka fito Maya na kwance gadon marasa lpy ana turata wani private room acikin hospital din aka kaita idan dakin ya hadu.

Doctor na fitowa yacewa su Dad ku biyoni.

Suna biye dashi har suka isa ofis din nasa zama yayi suma suka sami wajen zama,yad'an zare farin gilashin idonsa yayi yana share gumi, saida ya daidaita kansa before yafara cewa.

"Who are you to her?".

Daddy yayi saurin cewa "her parents and this ya nuna Nawaz yace"her brother you can feel free to talk."

Dan juyawa likitan yayi kan kujerarsa yasoma magana kamar haka.

Yace" a gaskiya yarinyar ku ta kasance daya daga cikin hallittun dan adam da sukeda karfin sha'awa kuma bugu da kari yanxun time na mensuration(jinin al'ada) shi zata fara shiya kawo ciwon ciki ya turniketa haka amma yanxu namata allura kuma zan yi mata prescribing magani da inta tashi sai a bata kafin jinin ya sauka insha Allah idan ta tashi xataji relief."

Ajiyan zuciya dukkansu suka sauke banda Nawaz daya tabe baki cikin ransa kuma yace dama kwaila ce yarinyar nan ashe yanxu ma zatafara jinin al'ada kuma wai takeda desire sosai tabdin.

Dan rubuce -rubuce Likita yayi a dan paper yabawa Daddy, godiya sosai Daddy yamasa suka fice.

Dakinda Maya take suka wuce Nawaz kam reception yawuce ya zauna yana tabe baki.

A kwance suka sameta tafada dan lokaci guda fuskarta tayi fayau tana baccin abinta, Momi ce takarasa tana shafa dogon gashin kanta dakuma fuskarta Daddy kuma ya tsaya yana kallonta dakuma tausayinta.

****

_2hrs later_

Maya ta farfado lpy jiki da sauki saidai dan ciwon ciki daya ke damunta kadan2.

Momi da Daddy sun fita dan sayaen magunguna dakuma su pant,da always.

Nawaz ne zaune ya zubamata manya kuma oily eyes dinsa masu rikitarwa kanta na a gefe bata kallonsa.

"Ke kawaila Nawaz yafada da dan karfi."

Shiru kake ji bata amsa saba.

Dake fa nake Kwaila ke dakike kwance.

Sai yanxu ta fahimci da ita yake dan haka ta juya ido biyu sukayi cikin ranta kuma maimaita kalmar *kawaila* da ya kirata dashi take.

"Kin zubamin na mujiya kina kallona karki cinyeni mana, dan naga alama likita yace kina daya daga jerin masu yawan sha'awa ko ta kaina zaki farane yayi tambayan yana kanne mata ido daya.

Taji zafin kawaila daya kirata dashi ga kuma sha'awa dayace tana da shi wata irin kunya ce ta rufeta take ta kauda idonta daga nasa ta juya baya.

Kafada ya dage alamar ko ajikinsa hakan da tayi.

Daidai nan Momi ta shigo leda hannunta bayanta kuma Daddy ne yashigo, gefen Maya Momi ta zauna tace.

"Sannu baby"

Gaida kai kawai Maya take.

"ina da ina ne ke miki ciwo yanxu Momi tasake tambayarta"

ido tadan rufe tana cize lips a hankali tace"babu amma cikina yana min kadan kuma inajin yunwa."

Oppss! sorry wlh na manta duk na rikice driver na hanya da shayin yanxu zai karaso kinji."

Kai tasake dagawa alamar "toh taji"

Matsawa Daddy yayi yana shafa kanta yace"Mamana jiki da sauki koh".

Tace"Alhamdullilah"

Yace"Allah yabaki lpy Mamana"

"Ameen ya rabbi ta amasa sa"

Shirune yabiyo baya nadan wasu lokuta, ana cikin haka driver yakawo brkfast daga gida da shayin nan Momi tahadamata tasha sosai.

Daddy yakula da Nawaz da bai ci abincin ba yace"Boy kai baka abincin bafa"

"Daddy bazan iya cin abinci a hospital dinba."

"Okay na gane."

mikewa Nawaz yayi yace i will be on my way zanje gida na dan huta narama baccin da ban samuba jiya am sleepy yafada cikin sanyin murya."

"Toh" Momi tafada, daga bisani kuma Daddy yace"baza mutafi tare nima inada meeting a government house by 10 na safe."

Sallama sukayi masu bayan Daddy ya tambayi Maya meye takeso yaxomata dashi tace"Ice cream" nan yace toh zai kawomata.

Sosai Momi ke kula da ita ana haka har jinin ya sauka Momi ta koyamata yadda ake amfani da pad sai kuma ta ajiyeta tana bata darusa kan tsabtace jiki da sauransu.

Nawaz sun isa gida ya wuce part dinsa wanka yayi yaci breakfast ya kawanta nan bacci ya daukesa.


*_Daga Alkalamin✍_*

*_NEERATLURV😍_*

*_DA_*

*_ABDUL MR SMILE😊_*

_Kuyi hakuri da wannan pls wollah ina busy ne but you guys should manage i will try to make d next page a bit long enjoy it, chill heart you❤_

#vote
#share
#comment
#Love

*_One love_*💞

MAYAWhere stories live. Discover now