❣❣
❣*_MAYA!🙍🏻♀_*
❣❣
❣1⃣5⃣
Via O.H.W📚
neeratlurv.blogspot.co.ke
Wattpad
@neerat_lurv
***Monday kamar yadda Nawaz yace haka akayi dan yau takama monday ɗin."Misalin 7:00am dot Maya tagama shiryawa cikin uniform ɗinta mai riga blue da tambarin rubutun sunan makarantar ɗauƙe a jiki sai skirt da yake iya guiwa kalar ruwan toka kafafunta sanye da white shocks da bakin takalmi dan karamin hijabi ne jikin ash colour iya kafaɗarta fuskarta fayau ba ƙwalliya sai ƙwalli data sanya a ido taɗan murxa hoda kadan da man leɓɓe.
' A dinning na falon Momi ta zauna tana karin kumallo har ta kusa idawa Nawaz ya shigo falon fuska ɗaure kamar hadari "ke ki tashi muje" abinda ya iya faɗa kenan.
"Suna shirin barin falon Momi ta sauƙo tace a'a har xaku tafi bamu yi sallamaba.
"Nawaz ne yayi saurin gaida,bayan sun gaisa yace eh Momi ai muna sauri kartayi letti kuma kinga nima i have somewhere to go shiyasa.
"ok allah yabaƙi sa'a ƴata yakuma kareki yabada abinda akaje nema kema kuma ki dage banda wasa pls Momi ce tayi dukka maganarnan."
"Toh Momi insha Allah zanyi.""Momi bye, ke kuma hurry up mu tafi karkisani letti yakara gaba."
A cikin mota ta samesa nan ta buɗe gidan baya da niyan zama tsawa yada dakamata yace"ni driver'n kine stupid come to the front seat."
A tsorace tadawo front seat yadda yafaɗa ɗin saidai tana shiga bayan ta xauna ya juya hade da jan kunnuwanta yace
"Stupid girl wlh kisake min abinda kikayimin koh hmmm... ya girgixa kansa hade da ciza leɓɓensa kaɗan yace sai na lahira yafiki jin daɗi cike da mugunta ya murɗa kunne da karfe before ya sake."
Idanu wanta sunyi ja ga ruwan da ya tara yana sakinta ta kauda kanta gefe tana murguɗa ɓaki leɓɓanta na motsawa kasa2 tace
"Allah ya isa mugu, azzalumi kawai mai kama da mage"
Meye kikace nine mugu ko kuma mai kama da mage ok fine xakiga mugunta kuwa.
Hanjinta saida suka kaɗa dan bata tsamman ya jitaba a hankali cikin ranta tace " banza dubesa yo ni ina ruwana ai shi mugun ne mutum kullum fuska a haɗe kamar yaga mala'ikan ɗauƙar rai mtsww taja karamar tsaki cikin ranta."
Sun fita gate na gidan yaja motan da karfin tsiya wanda har saida Maya ta buga kanta da dash boot na motan taji zafi sosai amma haka ta noƙe sabida tasan da gayya yayi hakan, gudu sosai yake zabgawa kan titin har suka isa makarantar.
Yana parking yafice yayi gaba ba yadda ta iya haka ta rinka binsa harsuka kai office na principal, hakimce kan kujerar sa yake yana ganin Nawaz ya soma murmushi, ɗaya daga cikin kujerun ofis ɗin Nawaz ya zauna ya mika masa hannu suka gaisa yace .
"Toh mr principal here is my sister ka ganta she is under your control idan tayi ba daidai ba flog sosai inkuma da bukatan wani abu here is my number written down ya ajiyemasa paper da number'n ke kai.Numfashi principal yaja kan ya dubi Maya yace.
"What is your name?"
Kallon gefe inda Nawaz yake tayi before ta maida dubanta kan principal tace.
"Fatima Umar Yusuf."
nice name inji principal ɗin kan yace "you are admitted into jss3 and yanxu kuna second term you should put more effort a karatunki next term zakuyu j.s.c.e yanxu zan kira class teacher ɗinku ya kai ki class kafin afara assembly, i hope u understand all what i said?.
Kai ta gaidamasa tace"yes sir i undersrand it."
Good of you yace, Nawaz is really impress bai tsamman Maya ta iya turanciba amma ta burgesa saidai yaki nunamata hakan saima harara daya bankamata.
Nan principal yakira class teacher ɗinsu ya masa bayani zasu fita Nawaz yace "hey stop".
Tsayawa tayi tana kallonsa zuciyarta na harɓawa, hannu yasa cikin aljihu yacire 1k yabata yace "Use it for your break".
Bayan ta karɓa tace "Tnx bros" bata jira mai zai ceba tayi gaba abinta.
Class teacher yanemi monitor ya damka Maya hannunta, yarinya ce sa'ar Maya ɗin tana da kyau daidai misali sunanta Halima amma ake cemata sadiya kusa da desk ɗinta ta ajewa Maya jakarta ta suka wuce assembly ground.....
_Kuyi hakuri da wannan insha allah am going to make 2 pages for guys 2morrow am less busy ne shiyasa_
#Vote
#Comment
#Share
#Love*_Daga Alkalamin✍_*
*_NEERATLURV😍_*
*DA*
*_ABDUL MR SMILE😊_*