14

422 22 0
                                    

❣❣

*_MAYA!🙍🏻‍♀_*

❣❣

1⃣8⃣

Via O.H.W📚
neeratlurv.blogspot.co.ke
Wattpad
@neerat__lurv


**Yau ta kasance weekend misalin 6:30am na safe Maya ta farka daga baccin da ta koma tun sallahn asuba.

Haka kawai take jin tana so ta dan yi exercise ko zaga gidanne tayi before Momi ta fito su shirya brkfst.

Dogon wando ne a jikinta na bacci da kayan iya guiwarta, kayan kalar pink ne mai laushi ya mutukar yimata kyau kanta sanye da hula ta mike ta fita daga dakin tafiya take har ta kai harbar gidan, zagewa ta soma tashiga garden can tafita da niyar komawa har ta wuce inda taga anrubuta _My game_ jikin wata daki ta koma.

Hangosa tayi cikin kayan game sai daga karfe yake yana hada gumi, dakin cike yake makil da kayan game iri iri.

Ta shagala da kallonsa ba karamin burgeta yayi ba yadda yake daga karfen, ta manta inda take kotakota.

Shikuma aje karfen yayi yaja karamin towel yana goge jikinsa, haka kawai jikinsa yabasa ana kallonsa juya warda zai yi yaci karo da cute face dinta tana xaune ta tallab'i kumatu sai kallon direction dinsa take she is not her self bcox she almost forget about everthing.

Fuska ya kwabe yace"look at how she is looking at me kamar zata cinyeni danye but zanyi maganinta she must tell me mai yakawota nan in this early morning.

Cike da kasaita yake tafi har ya isa inda take bata ji tsayiwarsa ba, shukuma hakan yamasa dadi ganin bata san inda take ba ya bude bottle water din hannunsa mai sanyi yashiga kawararamata.

Firgita tayi ta mike da sauri ido hudu sukayi yana watsa mata wani irriatated look.

Shirin barin wajen tayi sai ji tayi ya damko gashin kanta dake cikin hulan auchh tace tana lumshe ido alamar taji zafi.

Cikin lion voice dinsa yace"uban meye kike anan? And why are you staring at me kamar zaki cinyeni danye?"

Em..em.em..dama in ina tasoma takasa mai zata ce.

Tsawa ya dakamata yace" bazaki fadamin ba kenan ko saina soma dukanki tukun yayi maganar in a serious tongue."

Ganin yadda yayi maganar ta tsorata tace"dama fa ina wuce wane shine na ganka kuma tadan yi shiru tarasa nafada.

Sake damkar gashinta yayi yace" Ina jinki kuma mae?"

Hadiye miyau tayi tace" i dont know kawai i found my self staying and watching you am impress ne kawai yadda kake daga karfe takarasa maganar cike da tsoro."

Har ga Allah yayi niyan punishing dinta but jin tace he impress her yasasa sakinta yace"daga yau nasake kamaki kina kallona haka sai na cire idonki mai kama dana mayu get lost now yafada da dan daga murya.

Fewww! Ta wuce tana sauke ajiyar xuciya, a kitchen taga Momi nan ta gaidata tasoma aiki tana taya Momi hada brkfast sabida Daddy na gari yau.

_Some Few hours later_

Sungama cin brkfst its almost 10 na safe suna a zaune duka a falon Daddy yasoma tambayar Maya yace.

"Mamata ya karatu?"

Murmushi dauke kan fuskarta tace"Alhamdullilah mun ma kusa xanq junior waec"

A'a lalle mamana ta kusa zama yan mata yafada cikin zolaya.

fuska ta rufe da hannu ita a dole taji kunya.

Mikewa tayi tace" Momi zanje na shirya kinsa yau nafadamiki zanje gidansu sadiya koh."

MAYAWhere stories live. Discover now