Motar haya ta sauke Hindu a bakin hanya, ta fita ta nufi lungu.
Motar da ke bin bayansu ma ta nemi wuri ta tsaya. Sai da Hindu ta dan yi nisa sannan mai tuka motar ya fito ya bi ta a baya a hankali ta yadda ba za ta gane shi ba.
Ya kan dan tsaya a jikin wani bango ko ma ya shige zauren wani gida idan ya lura za ta gane wani ya na bin ta a baya. Baya son ta bace ma sa. Ya yi niyyar sanin gidan su ko ta halin kaka ne a yau din nan.
Wani gida ta shiga, wanda a gaskiya ba za a taba tsammanin da wani mahaluki a gidan ba. Daki daya ne, ginin katangar da ke gewaye da shi kusan duk ya rushe. Dakin ma kan sa gefe guda ya zube, an yi masa gwafa a ta ciki.
Gwafa sanda ce wanda a kan saka a tsakiyar daki wanda ke rike rufin kwanon da ke shirin zuba ya afka ko ruso. Duk da haka, ba matakin dindindin ba ne, don kuwa motsi kadan zai iya sanya shi ya zubo idan ba a yi hankali ba.
Bangaren dakin da ya zube an rufe shi da yagaggun kwalaye ne. Ga alama ma su shi sun tashi ne suka bari, su kuma a wadannan suka shiga.
Yana labe ya ga ta buga jikin langa-langar da ke sakale a matsayin kofar dakin. Wata budurwa ta bude mata kofar, dakin bay a wani haske sosai bayan na wata fitilar kalanzir. Ta mika ledar da ta ke rike wa wannan budurwa sannan su ka shige ciki tare.
Ya nisa, ya dudduba wurin sosai don ya gane, sannan ya sake kallon wannan gida da budurwar nan ta shiga ciki. Ya ciro kwalin sigari daga aljuhun rigar sa ta jamfa ya kunna daya da ‘lighter’, ya zuki hayakin ya busa cikin iska.
Murmushi ne cike da fuskar sa. A yau kam ya samu yadda ya ke so. Ya jira wannan rana ba tun yau ba, sai yau Allah ya cika masa burin sa. Ya shiga motar ya tayar, ya yi kwana ya koma hanyar cikin gari ta yadda ya fito.
Ya saka kaset din wakar Dan Anace a cikin rediyon da ke motar sa, wakar da ya yi wa ‘Shago’, shararren dan – damben nan a wancan zamani. Wakar da ya fi so ke nan, don haka ya riga ya haddace ta da kai. Ya na tuki ya na bin lafuzzan wakar a hankali tare da fidda gardin wakar kamar shi ya rera ta tun farko.
Jiya ya kashe…yau ya kashe….ko gobe na kashewa. Sai da maza a ke yi!
Ya na tafe ya na busa sigarin sa, zuciyar sa cike faal da nishadi, ya na jin kan sa kamar shi din ne ma Shagon. Lallai ya cancanci a yi masa waka kamar Shago domin ya yi kusa samun nasara a bisa burin da ya saka a gaban sa.
Kuma babu wacce za ta kai shi ga nasara irin yarinyar nan da ya gani tun shekaranjiya. Tun da Allah Ya sa ya gan ta, ya san kakar sa ta yanke saka.
Ya nisa a lokacin da wani murmushi ya rine fuskar sa. A wannan lokacin ne kuma ya shiga sha-tale-talen Dogon Yaro, ya dauke kan motar ta sa ya shiga hanyar Sindaba Hotel, ya mike hanyar sak. Sai da ya kai ga wani gida tukunna ya sa kan motar tare da latsa ham.
Mai gadi ya bude karamar kofar, tare da lekowa wajen mai tukin motar. Ko da ya lura da wanda ke cikin ta nan take ya yi sauri ya bude ma sa babbar kofar. Shi kuma ya shiga ciki, Mai gadin ya rusuna tare da yi ma sa barka.
Ya na tsayar da motar ya fita cikin sauri, ya nufi cikin gidan da ke girke a gaban sa. Babba ne, mai dauke da manyan falo guda biyu da dakina hudu. Ga furanni sun gewaye shi, ma su launi kala kala domin kawata wa. Kofar shiga cikin falon na gilas ne guda biu, irin wadan da akan tura ne gefe sannan a wuce.
Wa ta mace ta na zaune a falo ta na kallon talabijin mai kala inci 24. Da ganin sa ta mike ta na yi ma sa barka da dawowa. Ya amsa sannan ya shige cikin daya daga dakunan gidan, a yayin da ta bi bayan sa.
Ya cire hular sa a hankali sannan ya jefa kan gado tilo da ke garkame cikin fankacecen dakin. Sai kuma kujeru biyun da ke gefe na leda da jikin karfe. A ta bangaren hagu kuwa akwai ginannen wadurof mai kofa biyu.
YOU ARE READING
..... Tun Ran Zane
General FictionNo 1 in General Fiction on 21 September. A lokaci guda duniya ta yi mata juyi mai zafin gaske. A lokacin rayuwa ta kawo mata zabi mai cike da hatsari da nadama. Ta yi watsi da duk wata fata, ta dakatar da duk wani mafarki....tun da dama ai mafar...