Babi Na Sha Tara

1.9K 192 111
                                    

Malik ya ji ta na shakewa cikin kuka mai shiga jiki sannan a hankali. A nan ne ya kasa daurewa zuciyar sa, ya je gare ta ya ja ta zuwa jikin sa sannan ya rungume ta.

Da farko kamar za ta fice daga jikin na sa amma ya rike t ne gam, hancin san a shaker kamshin man gashin ta na dabur Amla hade kamshin turaren ta mai kamshin abarba da kwakwa.

Zuciyar sa ta sosu, jin yadda dumin hawayen ta ke jika gefen rigar sa. Bai damu ba, don zai iya yin komai don wannan radadin da ta ke ciki ya gushe ma ta.

Ya sake nadamar saka ta ba shi labarin ta. Ya san ba abu ne mai sauki ba, don ko da bai dandana irin waannan jafa’in ba, ya sha jin labarin yadda dubban mutane su ka salwanta ta dalilin wannan ruguntsimi.

Wadan da ke raye ma neman mutuwar su ke saboda rasa ‘yanuwan su da su ka yi. Tashi guda a ka mayar da yara marayu, mata zawarawa, sannan aka hallaka al’umma. Akwai matan da suka kubuta da kyar daga hannun wasu miyagu, wadanda suka mayar da su matan su na dole a matsayin ‘ganimar yaki.’

Daga yadda ta ba shi labarin Baba Alhaji, rashin sa babban gibi ne gare su baki daya. Sannan kuma a ce su na ji su na gani a ka hallaka shi?

Shi kan sa saukar ruwa ne kan kundukukin sa ya shaida ma sa hawaye ya ke yi tsabar tausayin ta. Ga rashin iyaye sannan ga wannan?

Numfashin sa a lokacin fita ya ke yi tare da na ta, a hankali, a natse kamar ma su bin wani yanayin tsafi.Ya ji ta dan ja hancin ta, sannan ta yi yunkurin fita daga rungumar

. Hakan ya sa shi sassauta rikon na ta da ya yi, ya kalli cikin idanun ta. Sun yi jawur kamar an shanya gauta, sannan sun kumbura. Zai iya nutsewa cikin su, ya mance da sunan sa da ma kudirin sa, har sai ya tabo cikin zuciyar ta.

Shin tausayi ne tsabar sa, ko kuma da wani abu ne? Shi kan sa ba ya da lokacin tunani ko nazarin amsar. Ya saka hannun sa ya na share hawayen ta, ya na danne zuciyar da ke ingiza shi kan ya sumbaci kumatun nata, ko za ta samu sauki.

Ta kura ma sa idanu ba ta ko kawar wa. Shi ma bai kawar da na sa ba, numfashin sa da kyar yake iya fita, a yayin da iskar da ke dakin ta tsaya cik a gewaye da su. Karo na farko ke nan da ta kalle shi, har ma yake iya ganin cikin ruhin ta ba tare da ta saka shamaki ba.

Cikin kunci take, ya lura da hakan. Ta na bukatar waraka ko da ba a lokaci daya ba ne. Sake maimaita labarin ya na matukar rugurguza ta. Ba tare da sanin dalili bay a ji ya na son taimaka mata wajen saamun sassaucin, in har za ta yarda da shi a hakan.

Don haka ya yanke shawarar ba ya son ci gaban, a kalla, a wannan lokacin. Ya yi yunkurin fada mata hakan. Amma kafin ya bude bakin sa duka, ta gyara zaman ta tare da share hawayen ta da kawar da kai, sannan ta ci gaba:

“Hakika mun yi rashi babba, don kuwa Allah shi ne gatan mu, Baba Alhaji ma gatan mu ne, jigon rayuwar mu ne. Sannan ga Gwaggo Kabo ita ma mun rasa ta. 

A lokacin da na yi rashin mahaifana, ya tsaya gare ni, ya nemo min tsari na rayuwa sannan ya kawo min farin ciki daidai ikon sa. Sai ga shi cikin wani yanayin da ba na da ikon taimaka ma sa  alhali ya na bukatar taimakon.

Ba zan taba mancewa da furucin Baba Alhaji ba, na cewar mu gudu don mu ceci rayukan mu; ko ma salatin da ya rika ambatawa a yayin da a ke ma sa wannan azaba. Tun ya na iya yi har ya yi shiru.

Mu hange shi ne a lokacin da muke gudu kamar yaddaa ya umurce mu. Duk da cewar cikin duhun dare ne, wutan gidajen da ke ci ta ba mu damar ganin komai, kamar cikin fim.

Ba mu san yadda a ka yi ba, kawai ganin Rufus mu ka yi ya ciccibo Gwaggo dauke a wuyan sa ya na jerantawa da mu cikin gudu. Gudun kawai muke yi ba tsayawa, koke-koken mutane da kaurin kuna suka cike kaina da kwanya ta, duhuwar dare da na hayaki suka cike idanuna, don haka babu abin da ke bani karfin gwiwar ci gaba sai muryar Rufus, wanda ke nu na mana hanyar da za mu bi.

..... Tun Ran Zane Where stories live. Discover now