Assalamu alaikum, barka da warhaka.
Yau Allah Ya yi, na samu yin update kasancewar asabar.
Hindu ce ke gayyatarku zuwa walima/liyafa /hafla/casun taya ta murnar auren ta.
Ummyasmeen ce jagora, mai fadakarwa. 😇
Xclusive_j ce babbar kawa ta da aminiya. 😎
UmmRa'eef, Kulthumuazu, babynmama, Umarfatima, Ummaty 123,AishatuYM ma su masaukin baki.
Saura da ba su ga sunan su ba sai ranar cin rengen 😋💃za ku gani.
Jazakumullah bi khair💗😘😍
Hindu ta na zaune a kan gungumen dake cikin zauren, dab da kofar dakin sa. Ta jiwo muryar sa a lokacin da ya doshi zauren, ya na gaisawa da makwabcin su Malam Salihu. Ba ta dai san ko karfe nawa ba ne, amma ta san dare ya yi sosai.
Da shigar sa ya hada ido da ita, kasancewar akwai wutar lantarki. Sanye yake cikin wando na velvet mai launin bula da rigar launin ruwan hoda. Jamfofi sun a karbar sa, amma idan ya saka kanana tamkar don shi a ka yi su. ga kamun kai ga natsuwa.
Ya dan yi murmushi tare da duban agogon hannun sa, “Ke kuma me ki ke yi a nan ba ki yi barci ba?” Muryar sa dauke da mamaki.
Ta mike ta tsaya, hasken wutar kwan lantarkin da ke azure ke kara nuna tsarin sa. Duk da cewar doguwa ce, ya dan dara ta kadan.
“Yaya Auwalu, yau kwanaki biyu ke nan, amma ban ji ka ce da ni komai ba.”
Ya fadada murmushin sa, amma bai kai idanun sa ba, “Je ki kwanta Hindu, dare ya yi sosai.”
Wani abu ya murda cikin zuciyar ta, ba ta san abin ba. “Ba zan tafi ba har sai na ji abin da za ka ce.”
Ya nade hannayen sa ya rungume, fuskar sa fayau, “To ni me ki ke son na ce? Abin da ya faru ya faru, wuri ya kure na neman shawara.”
Ta sadda kai a kasa, ta nisa. So ta ke ta san meye ra’ayin sa game da batun auren ta da ake shirin yi nan ba da jimawa ba. Ra’ayin sa muhimmi ne gare ta, don ko ba ta so, ya zama jigo a wajen ta.
Can ta dago ta dube shi, “Yaya ba na son ka dauke ni da wata manufa a ranka. Wannan abu na amince da shi ne saboda su Gwoggo…..”
Gwaggo. A lokacin da Hindu ta je da makudan kudi ba ta amince ta nuna mata ba, har sai da ta biya kudaden aikin na ta, a ka kuma tsara tafiyar ta su. Duk da hakan ma ba ta fayyace wa kowa yadda suka yi da Alhaji Bilya ba. Ta dai ce ma ta sun samu wanda ya amince zai dauki nauyin komai na su ne.
A cewar ta, jami’in gwamnati ne da ke duba mabukata sannan a dauke mu su nauyin jinyar su. Gwaggo har cikin zuciyar ta ta amince da hakan. A ka bar Hindu da tsarguwa cikin radadi da jin zafi. Ta rasa wanda take yaudara a tsakanin su din, da kuma ita kan ta.
Kowa ya yi ta farincikin jin wannan bayani kan yadda gwamnatin jiha ta yi hubbasa kan ‘yan gudun hijira don saukake mu su zafin rayuwa. Tsawon kwanaki biyu Hindu ta gagara sukuni da sakewa. Da kan ta ta iske Auwal ta fede ma sa daga biri har bindi.
Ba ta iya karantar komai a fuskar sa ba tun gilmawar kaduwar da ta gani tun farko. Ya dan yi shirun dakiku goma, kafin ya fice ba tare da ya ce uffan ba.
A lokacin da Balele ya ma sa maganar su je ganawar da suka shirya haduwa da likitan Gwaggo, ya kura ma sa idanu kamar wanda ba ya jin san a tsawon lokaci. Can sai ya dan yi firgigit sannan ya bi shi suka fita.
Tsawon kwanaki biyu bai yarda sun hada ko da hanya ba ce da ita. Kafin ta leko waje za a ce ya fita, abincin sa ma Balele ne kai ma sa ko daya daga cikin kannen sa mata. Shi yasa ta gaji, ta zauna a zauren jiran sa, don ta san komai dare zai dawo dakin sa.
YOU ARE READING
..... Tun Ran Zane
General FictionNo 1 in General Fiction on 21 September. A lokaci guda duniya ta yi mata juyi mai zafin gaske. A lokacin rayuwa ta kawo mata zabi mai cike da hatsari da nadama. Ta yi watsi da duk wata fata, ta dakatar da duk wani mafarki....tun da dama ai mafar...