Assalamu alaikum.
Barkan mu da sallah. Da fatan an ci nama sese sese.
Ni dai ban goron sallah ba, don haka ina jira daga gare ku.
Na gode da hakuri da jira. Don haka yau sau biyu zan yi.
Allah Ya kara zumunci da kauna😘😘
Baba Alhaji ya kira ni washegari zuwa cikin lambun san a ‘ya’yan itatuwa. Lambun yana can kuryar fiin gidan sa ne, kuma ya na dauke da itatuwan Ettile, lemun zaki, piya, mangoro da kuma na tufa, wanda yake kokarin ganin ya kama kasa sosai saboda bai dade da dasawa ba.
Da kan sa ya kawo irin ya shuka sannan yayi dashen, ya ba da dukkan hankalin sa gare shi dare da rana, a yayin da mu kuma jira mu ke ya fara ‘ya’ya mu ci.
Ya na zaune bisa kujerar sa ta karfe, hannun sa rike da jaridar Gaskiya Ta fi Kwabo. Ya kalle ni, sannan ya ci gaba da karatun sa, ya na jan tsaki.
Hakan a kullum dariya yakan bani, cewar ba makarantar boko yayi ba, amma har jaridar turanci ya kan karanta, tsabar gogewa da duniya.
Kamar kullum, so yake na tambaye shi abin da ke faruwa a duniya, wand aba lallai ne ya shafe nib a, amma sai ya fada min. yawanci babu komai a labaran da ya wuce karin farashin man fetur da gwamnati ke shirin yi; karancin man fetur din; yajin aikin malaman jami’a ko na NUPENG da PENGASSAN, wato ma’aikata masu hidimar man fetur din, ko kuma na wanda ya zame ma sa abin nazari ma fi girma, wato tarzomar tashin hankalin da ke faruwa a garin Jos.
“Wata sabuwar tarzomar addini ne ta barke a Bukuru, wannan karon.” Ya furta cikin jimami da motsin rai. Ya dan kalli wurin da nake, ya ci gaba, “Ban san yadda matasan yanzu su ka dauki duniya ba. Sun saka zafin rai ga rashin tunani cikin kan su.”
Ya rufe jaridar sannan ya kurbi ruwan shayin da ke gefen sa. Duk da yawan shekarun sa bai cika yarda ya karanta jarida da gilashin idanu ba. Mun sha yi ma sa tsiyar za mu canja ma sa idanuwan sa da na akuya idan ya karasa su da gangan.
Kayan jikin sa ma su nauyi ne, malun malun ne da ‘yar cikn ta da suwaita a kai. Kan sa da hula sannan ya yi lullubi da maka-wuya.
Ban san matsayin matasan zamani ba, kawai ni abin da ya dame ni daban, wanda ya hana ni barcin kirki daren jiya, yak e kuma neman hana ni sukuni. Wa ya ce tsoffin banan ma tayar baya ne?
Jin ban ce komai ba; don da kamar a da ne, da zan yi nawa irin tsokacin har ma daga nan tarihi da labaran zamanin sa daga wajen sa iri iri su biyo baya na lokaci mai tsawo, ya sa shi ci gaba da cewa, “Hindu, ba zan taba tilasta mi ki abin da ran ki ba ya so ba. Kin fi kowa sanin yadda na ke kaunar ku dukan ku…”
“To me ya sa ka ke neman nisantar da ni daga gare ku?” Na katse shi, kusan idanu da hawaye.
Ya gyara zaman sa da kyau, cikin natsuwa da kwantar da kai, ya amsa, “Waya ce da ke hakan nisantar da ke ne daga gare mu? Yin hakan ne zai kara kusanto da ke wajen mu.”
Na tsaya kallon sa kawai. Ta yaya zai ce wai hakan ne zai kara sa mu kusanta? “Bayan ka na neman tura ni wata duniyar?”Ya dan yi dariya, “Na isa? Ai nan duniyar ma ta ishe mu gaba dayan mu.”
Ban ce komai ba, na kawar da kaina ma. Ya kira sunan na, da na kalle shi, ya min alamar na je kusa da shi. Nan na durkusa dab da kujerar sa, na saka kaina kusa da kafar sa. Ya kai hannun sa ya na shafa kaina cikin lallami, ya ci gaba da cewa, “Ina yin komai don ke ne Hindatu.”
Na nisa tare da saka kaina jikin hannun kujerar da ya ke kai. Ba kasafai ya kan kirani da sunana haka ba. Zuciya ta ta ciko faal da girmama shi da kaunar. “In don ni ka ke yi, to ka bar ni nan, tare da ku.”
ESTÁS LEYENDO
..... Tun Ran Zane
Ficción GeneralNo 1 in General Fiction on 21 September. A lokaci guda duniya ta yi mata juyi mai zafin gaske. A lokacin rayuwa ta kawo mata zabi mai cike da hatsari da nadama. Ta yi watsi da duk wata fata, ta dakatar da duk wani mafarki....tun da dama ai mafar...