Babi Na Sha Biyu

2K 162 75
                                    

Sun dade a wannan hali, har sai da wata kila ta lura cewa mafarki ne kawai ta ke yi, ta fara sakewa. A hankali ta bar yin karkarwar, saurin bugun zuciyar ta ta ragu, amma ba ta bar yin kukan ba. Ganin haka ya sa ya dan ja daga rungumar ya kalli fuskar ta.

Nan take zuciyar sa ta kusa narkewa don wani abin da ya kasa fassara shi, sannan ya yamutse kamar an daure da igiya, duk a lokaci guda. A firgice ta ke, ko ma meye dalili ba karamin al’amari ba ne.

Cikin saukaken murya saboda gudun kara firgita ta, ya ce, “Ina son zan karanto addu’o’in neman tsari da wanda a kan yi idan mutum ya farka daga mummunar mafarki, sai ki karanta a baya na.”

Ta gyada masa kai a hankali idanun ta cike da rauni. Ba karamin dauriya ya yi ba, don kuwa na sa bugun zuciyar ya karu, ya na jin tamkar ya nutse cikin su ya na ninkaya.

Ya shiga karantawa ta na maimaitawa a hankali har ya idar. A lokacin ta sake fiye da dazu, ta samu natsuwa. Ya tashi zuwa gefen gadon sa, ya na jin kiraye-kirayen sallar farko. Ya zuba ruwa daga jug din gilashin da ke ajiye kan faranti cikin kofin gilas din, sannan ya koma gare ta ya mika ma ta ta karba.

Sai da koma ya kashe iyakwandishinan din da ke aiki tun farkon daren sannan ya koma kusa da ita ya sake zama, amma bai sake taba ta ba.  Sanyi ne ya dan buso shi, ga mamakin sa, ya ji ya fara kewar ta. Saboda tsaro, ya rungume hannayen sa, ya kuma tsare ta da idanu.

Ta dan kurbi ruwan kadan shi kuma ya kura mata idanu. Agogon bango ya nuna karfe hudu da kwata a lokacin. Kan ta a sunkuye ta na kokarin daidaita numfashin ta. Ya mike hannayen say a ja nata ciki ya rike su. wani abin da bai san shi ya wuce ta jijiyar hannayen sa zuwa bargo.

Ya daure ya tambaye ta, “Ya ya ki ke ji a yanzu?”

Ba ta daga ta kalle shi ba, ta amsa, “Ba bu damuwa.”

A hankali ya gyada na sa kan sannan ya mike ya shige bandaki ya dauro alwala. A lokacin kiraye kirayen sallar suna karuwa har da assalatu. Nan ya fice ya bar ta zuwa masallaci.

Ko da ya dawo ya tarar ta warware sosai kamar ba ita ba. ko kuma hakan take kokarin nuna ma sa. Don ya lura ba da kuzari take abubuwa ba. tabbas wani abu yana damun ta har a lokacin. Kamar wacce ta bace a wajen amma kuma ta na wajen.

Hakan ya saka ma sa yin nazari. Ya rika tunanin abin da ya kawo ma ta wannan yanayi. Shin wani abu ne da ke da nasaba da wanda ya faru da su a da? Me ye abin? Ya na nasaba da kawun sa ne?

Bai dai tambaye ta ba, ita ma ba ta kara ce da shi komai ba. Hasali ma ya lura da kara komawa cikin…cikin wata batta ko kuma kurtun da ta kulle kan ta. Kuma shi a yanzu abin da ya fi son sani shi ne tsakanin ta da Kawun sa, wannan karon ya sha alwashin zai bankado gaskiyar lamarin.

“Ina neman wata alfarma.”

Muryar ta ce ta kutsa cikin nazarin abubuwan da yake yi, wadda ke da illar watsa sanyin da ya fi naiyakwandishan din dakin. Ya kalli wurin da ta ke tsugune a hankali, zuciyar sa ta tsaya cik. Atamfa ce ta daura mai launin shudi da rawaya, sannan ta dora bakar abaya shar shar, mai sheki da adon duwatsu jajaye a surke da fari.

Ya hadiye yawu a yayin da kamshin ta ya fara buso shi, “Me nene?” Ya tsuke fuska sannan ya kawar da kai.

“Ina son idan ba zaka damu ba, Bature ya kai ni Jos?”

“Jos?” Duk wa ta kafa a jikin sa ta fara aiki.

“Eh.”

Bai sake tambayar ta ba, amma a bayyane yake, cewar ya na bukatar karin bayani. Da kan ta ta dago kadan, idanun ta suka kalli cikin na sa, sannan ta sunkuyar. Idan a da ya na tunanin illar muryar ta ne, to idanun sun ninka ta sau goma.

..... Tun Ran Zane Where stories live. Discover now