Unguwar gaba daya lullube take da duhu, babu motsi, karar sautin kukan kwadi ya cike ko ina. Ko kusa bas u yi kusa da karar bugun zuciyar sa ba a lokacin. Babu abin da bai kawo cikin zuciyar sa ba kafin isar sa.
A kofar gidan ya latsa ham na tsawon lokaci, ya na jin zuciyar sa ta na tsalle. Mai gadi ya leko, sannan ya fito waje don ya ga wanda ke cika musu kunnuwa da tsohon dare haka. Kallo daya yayi cikin motar, ya ci karo da idanun Malik ma su ci da wuta, ta ke muryar sa ta washe daga nauyin barcin da tun farko ya bayyana tare da shi.
“Ka yi hakuri Yallabai.” Ya furta tare da juyawa ciki, ya bude kofar.
Gidan shiru ba bu alamun motsi na ma su rai. Abubuwa suka kara wanzuwa cikin kan sa. ta na iya yiwuwa ya samu Hindu ciki, ta na kulle cikin daya daga cikin dakunan, ta yi ihu da kuka har karfin ta yak are, muryar ta ta dusashe, ko ma ta dunkule gefe guda cikin tashin hankali…Ya doshi kofar gidan, ya shiga bugawa tamkar zai balle ta, zuciyar sa kara tafasa take yi. Jin sa yake da akwai hali da ya ture bangon gidan lokaci guda don komai ya bayyana gare shi lokaci guda.
Bayan wani lokaci ya ji kukan yaro, a yayin da wutar falo ta haska ta ciki. Bayan an daga labulen daya daga cikin tagogin an leka shi, kofar ta bude a hankali.
Ya na jin ana murda makullin kofar ya kunna kai ya shige cikin falon kamar guguwa, ya kusa ture matar kawun sa Nafisa, wadda ta tsaya ta na kallon sa galala cikin mamaki da fargaba. Ba tare da ya jira ta yi magana ba, ya tambaye ta, “Ina Kawu? Ki kira min shi yanzun nan!” muryar sa kamar umarni ne wadda ke cakude da tsoro ko fargaba sannan da zallar fushi.
Saboda tsananin kaduwa ta gagara cewa komai. Ta rungume danta wanda ke da wata daya da haihuwar sa a duniya, a yayin da ya ke kara tsala ihu. A bayyane yake, cewar ya fahimci akwai yanayin tashin hankali a falon. Malik bai tsaya jiran amsar ba ya kunna kai cikin dakin Alhaji Bilya, ya hange shi kwance shame-shame ya na numfashi da kyar.
Ai kuwa sai ya fada kan sa, ya cukume wuyan rigar sa kamar yadda ya yi wa Auwal. Shi waye da zai hana ma sa sukuni da kwanciyar hankali sannan shi ya kwanta ya na hutawa?
“Ina Hindu? Ina ka boye min mata? Ba ka ji kunyar tura min matar ka ba ta fuskance ni? Idan ka na son kan ka da lafiya ka…”
A daidai lokacin ne Alhaji ya saki wani irin tari. Nafisa ta shiga dakin a guje, jaririn ta ya na kara ihun. Ko da ganin halin da su ke ciki, ta fadi kasa tare da dungurar da jaririn a gefen ta a kasa, ta rike wandon kafar Malik, ta fasa wani irin ihu ta na magiyar ya sake shi, “Wallahi Malam ba ya da lafiya Abdulmalik.”
Malik ya kara hasala, ya dunkule hannun sa ya rika wanke masa a fuska, ya na cewa,”Munafiki, ni za ka ke neman yaudara? Ka fito min da ita yanzun nan!”
Nafisa ta kara tsananta kukan da ta shiga yi. Mai gadin gidan ya shiga har cikin dakin da gudu. Maimakon dage Malik daga gefen Alhaji Bilya, sai ya bi sahun Nafisa ya shiga rokon Malik kan ya sake shi.
“Wallahi ba ya da lafiya,” Nafisa ta gaba da yin bayani cikin kuka, “Tun da rana ya dawo, ya ce min ba ya jin dadin jikin sa sannan kirjin say a na ciwo matuka. Nan ya kwanta ya ce min ba ya son yara su dame shi. Da zu da yamma kuma ya rika wani irin tari. Na dauko maganin tari na ba shi, amma jikin sai ma ya kara yin tsanani.”
Malik ya kura wa Alhaji Bilya idanu. Anya, gaskiya ne rashin lafiyar sa ko kuma karya? Sai da Hindu ta bata ne zai kwanta ciwo? Ko dai rainin wayon da yake ma sa ya kai har hakan ne?
Amma kuma ya lura numfashin da ke fita daga kirjin sa sama-sama ne. Idan har karya ya ke yi to lallai ya gwanance, ya zama kwararrare. Sannan kuma duk jijjiga shi da kuma marin sa da ya yi ta yi bai yi yunkurin kare kan sa ba. lallai ne, hakan ba yanayin Kawun sa bane, wanda yake tamkar kububuwa, ko da walkiya ce ta gilma sai ya kai sara balle a ce Dan Adam ya masa laifi.
CZYTASZ
..... Tun Ran Zane
General FictionNo 1 in General Fiction on 21 September. A lokaci guda duniya ta yi mata juyi mai zafin gaske. A lokacin rayuwa ta kawo mata zabi mai cike da hatsari da nadama. Ta yi watsi da duk wata fata, ta dakatar da duk wani mafarki....tun da dama ai mafar...