Babi Na Sha Uku

1.8K 178 93
                                    

Abdulmalik ya kyale Hindu ta yi mu su jagora zuwa cikin wannan ginin. A bayyane ne, cewar benen ya na daya daga cikin wadan da a ka kai wa hari a fadace-fadacen da a ka yi ta tabkawa a kasar ta Filato.

Ya na kudancin Afirka ya samu labarin wannan yakin, bai ziyarci garin ba sai yanzu. Zuciyar sa ta narke kan irin abin da idanun sa suka gane ma sa. Bai taba zama cikin garin ba, amma ya sha wucewa ta ciki idan zai yi tafiya. Hakika, fitina wutar daji ce.

Cikin ginin wata farfajiya suka samu, wata mace daluma, ta na sanye cikin riga da siket iya gwiwar ta, ta dan daure ribom a kan ta a tsaye.

Wasu mazaje ne a gefen ta, suna saka sabbin tagogin da aka rugurguza ne ta ciki. Ita kuma matar ta na duba aikin da suke yi. Wani farantin shayi ne a hannun ta mai dauke da manyan kofunan robar shayi a kan su.

Ganin Hindu ya sa ta dan yi shiru na dakika daya, ta kura ma ta idanu kamar wacce ta dirko daga sama. “Hindu?!” Ta furta kamar ta na tsoron kar ta tabka kuskure.

Ya lura Hindu ta yi murmushi, sannan ta amsa, “Na’am, Anty Lucy.”

“Yesu! Da gaske ke ce?” A lokacin Lucyn ta ajiye farantin a kan matsakaicin teburin da ke girke a wajen. Ta dafe hannayen ta duka biyu kan kirjin ta, idanun ta cike da mamaki.

“Ni ce.” Hindu ta sake ba da amsa. A bayyane yake, cewar wannan haduwa ta su mai muhimmanci ne gare su dukan su. Kamar rakumin mutum ne ya bace a Hamada daga baya ya same shi.

Lucy ta saki karar da zai kwatanta farincikin ta na ganin Hindu, “Hian! Jesu kristi!” Ta durkusa kan gwiwowin ta, sannan ta daga hannayen ta sama tare da muryar ta, ta na waka. “Praise the Lord! Halelluya!!” Daga baya ta mike ta daka rawa sosai, sannan ta rungumi Hindu, duka suna kuka.

Daga shi har ma su aikin kallon su kawai suke yi. Sai da ta sa zuciyar ta motsa, duk da dai neman amsa ce ta kawo shi nan din.

“Haba, shaitan karya yake! Ni Lucy Pam na ji a jikina ba ku mutu ba! Alhaji ma ya ji hakan, shi yasa ba mu bar neman ku ba. Alhaji ya yi ta neman ku a wurare da dama; nan Jos, Kaduna, Nassarawa. Ni ma kaina na je Bauchi wajen sansanin ‘yan gudun hijirar, amma ban samu labarin ku ba. Amma still, na ce ba zamu give up ba. Yes, the devil is a liar!” Ta sake tikar rawa ta na juyi ta na daga hannayen ta sama.

Sai a lokacin ta lura da Malik, sannan ta ba shi hankalin ta, “I am sorry, wa ka ke nema?”

Kafin ya ce wani abu, Hindu ta amsa, “Anty Lucy, tare mu ke da shi.”

“Eyya, sannu da zuwa.” Ta furta kusan a rusune. Ba ta bata lokaci ba ta ba su wuri suka zauna, sannan ta ba su abin sha.

Hindu ta tambaye ta, “Alhaji ya na nan kuwa?”

Kusan cikin zumudi ta yi tambayar. Ko ma wane ne Alhajin, Hindu na matukar fatan ganin sa. Hakan ya tsayar da hankalin sa. Wurin wa suka zo? Ofishin lauyoyi ne dai daga yadda allon gaban ya nuna.

Mene ne makasudin zuwan Hindu nan wajen? Shin ya na da alaka da Kawun sa? Ko duk shirin sa na neman ja da shi a kotu don hallaka kamfanin sa? Da zai iya tambayoyin wa Hindu, amma ba mamaki ita ma ba ta gama fahimtar abin da a ke ciki ba. don kuwa shi kadai ya san irin kwakwalwar sa.

Ta dauki wayar tarho daga ma’ajin sa, ta shiga juya lambobi, ta amsa, “Yes, my dear. Ya na Hillstation Hotel. Ya ce duk wanda ya zo, in dai akwai muhimmanci to na nemi shi a can. Kin san yadda garin ya zama….”

Ta dan dakata da maganar a lokacin da wata muryar ta kwararo daga daya bangaren. Ta yi bayanin ta na neman a hada ta da dakin Alhajin ne, a k ace ta kira bayan mintuna biyu, sannan ta ajiye.

“Ya na ganawa ne da wasu. Kin san yanzu Alhaji ya koma Abuja ne da aikin sa. Kawai nan din daga baya ne ya ce a gyara na rika zuwa ina zama saboda tsoffin abokan hulda, sannan kuma ya yi fatan Allah zai sa ku bullo. Saboda haka idan ya zo to layin mutane ke jiran sa don sau biyu ya ke zuwa a sati.”

..... Tun Ran Zane Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang