Babi Na Sha Shida

1.9K 165 92
                                    

Malik ya kura ma ta idanu a lokacin da ta kifar da kan ta, jikinta jijjiga cikin kuka take yi mai tsima jiki. Bai san abin da ya dace yayi a lokacin ba.

Ya dai san abu guda, cewar ta yi babban rashi a rayuwar ta. Shi mahaifin sa ne ya rasa, nan ba da jimawa sosai ba amma ya ke jin ciwon na zafin rashin sa har ranar, ballantana a ce na ta su biyun ne gaba daya?

Ta na bukatar kalamai a lokacin, wadan da ko ba su dauke ma ta radadadin da take ciki ba, za su saukaka ma ta shi. Amma ya gagara furta komai.

Ba kuma wai don rashin yarda da ita ba ne, a’a, ya yarda da labarin da ta ke ba shi. Amma ya na gudun kar ya je ya ja ta zuwa ga jikin sa da nufin rarrashi wani abu ya kai ga afkuwa, har su shagalta, daga baya kuma su zo su na nadama.

Maimakon hakan, ya ja hanayen sa ya nade cikin kirjin sa sannan ya matse zuciyar sa cikin jin zogi. Ya rasa abin da zai yi guda daya; ya na son ta ci gaba, kuma ya na son ya ce ma ta ta bari sai zuwa lokacin da ta ji natsuwa tukunna. Amma duka cikin su bai yi ko guda daya ba.

Kamar wacce ke iya jin muhawarar da ke zuciyar sa, ta dago ta kalle shi a lokacin, numfashin sa ya tsaya cikin huhun sa. Ya Allah! Idanun ta jawur, sun kara girma cikin shekin hawayen da ta zubar.
Ta dan ja hancin ta tare da goge fuskar ta da abin gogewar da ya ba ta.

Da kyar ya ke jin iya fitar muryar ta, “Za ka iya yin hakuri bayan sallar asuba na karasa ma ka?”

A lokacin iska cikin huhun sa ta fice gaba daya. Ya gyada ma ta kan sa cikin amincewa. Ya yi kyau da ta yanke ma sa abin da ya dace a lokacin.

Sannan a lokacin ne ya samu yi ma ta magana, “Allah Ya jikan su da rahama.”

Ta share sabbin hawayen da suka zubo ma ta, ya ji ya fara tsanar kan sa, na saka ta cikin wannan halin.

“Amin.” Su ka dan yi shiru kadan, kafin ta dora da, “Baba Alhaji ya sha fada min cewar mamaci ba ya bukatar kuka sai addu’a. A mma duk da hakan, a duk lokacin da na tuno da su….”

Ya ji yawu ya wuce ma sa, makogwaron sa da wani abin da ya cike ma sa shi. “I feel your pain. Na san yadda kike ji don rashin iyaye rashin wani babban ginshiki ne a rayuwa.”

Ta kara jan hancin ta, “Haka ne.”

Sun tsinkayi kiran assalatu daga masallatan unguwar su. Ya mike ya yiwo alwala, sannan ya fita zuwa masallaci, zuciyar sa cike da tunani. A gaskiya ya zarge ta, kan cewar irin ta ne matan da sukan amince su yi komai saboda da kudi. Har ma su sayar da ran su da ruhi.

Amma tun daga jiya ya fara musa hakan. Ya san ta karbi kudi, jazaman ne ma hakan saboda yadda ya ga kakarta na kwance, gidan da ta fito cikin talauci.

Ko kuma gidan da ta nuna wa duniya ta fito. Da ma shi tun farko ba yarda ya yi ba.

Tambayoyi da dama sun cike zuciyar sa fiye da lokacin da bata fara ba shi labarin ba. A bayyane ya ke, cewa da sauran labarin a baya.

Ta ba da labarin Baba Alhaji, amma bai gan shi ba. Ga kuma wani wai shi Sadiq, wanda ba sai an tona ba, akwai wata alakar da ta shiga tsakanin su tun da ya lura da lokacin da ta tambayi wannan Alhaji Maigarin wurin da yake.

Ya nisa a lokacin da kofar masallacin ya bayyana a gaban sa. Iskar asuba mai sanyi ta mamaye shi ta na dan hurawa. Ba zai yi saurin yanke komai ba. Zai saurare ta, don jin karashen.

Ko da yake, shi kan sa bai san yadda za ta kaya tsakanin su ba bayan ya gama jin labarin. Ya san dai ya na bukatar jagoranci daga wajen Allah…kamar kullum.
  
    *                    *             *                                              *       *          *

..... Tun Ran Zane Donde viven las historias. Descúbrelo ahora