Babi Na Daya

9K 455 51
                                    

Assalamu alaikum.

Na dawo tare da wannan dadadden labarin wanda a wancan zamanin da na rubuta shi na yi ne son saka yadda na ji a zuciyata a cikin takarda.

Za ku ga wurare da abubuwan da basu tafi daidai da zamanin da muke ciki ba. Amma na yi alkawari hakan ba zai shafi gundarin labarin ba ko kadan.

Kar dai na cika ku da surutu, ga ran zane na fitar zuwa gare ku.

Ku ci gaba da nuna wa labarin kaunar ku ta hanyar danna maballin tauraron nan sannan ku yi tsokaci a kan kowanne layi ko kalma ma in da hali.

Kar ku mance, a ko yaushe ku ne ke kara min kwarin gwiwar ci gaba da rubutu.





Babban asibitin Bauchi ya cike da jama’a a yammacin litinin, a kokarin da kowa ke yin a ziyartar ‘yan uwa da abokan arziki marasa lafiya.

Rike da takarda a hannunta, Hindu ta shiga shagon sayar da magani na Safara Pharm ltd da ke kusa da asibitin. Ta mika wa mutumin da ke bayan kanta takardar, ya duba da kyau.

Bayan yayi nazarin abin da ke kai, sai ya rubuta ma ta jimillan kudin magungunan ya mika ma ta. Ta dade ta na dubawa a yayin da kwalla su ka ciko mata idanu, zuciyarta ta shiga kuna. Ta yi wata irin nisawa sannan ta dubi mutumin, wanda a lokacin ya jera ma ta magungunan a gabanta, ya na jiran ta biya kudin su.

Ta tambaye shi kudin kowanne dai dai, ya yi ma ta bayani. Ta dubi kudin da ke hannun ta, bai kai ya saya ma ta daya daga cikin jerin magungunan ba ma. Ta sunkuyar da kai kasa hawaye suka zubo ma ta. Ta saka bayan hannun ta ta goge, ta juya za ta tafi.

Mutumin nan ya dakatar da ita, “Ji ma na ‘yan mata, dakata.”

Ta tsaya ta na sauraron abin da zai ce. Ya ci gaba, “Ya ya dai? Me ya faru ne?” Ba ta san shi ba, amma muryar sa ta nuna ban tausayi gare ta.

Ta girgiza kan ta, “Babu.”

Bai amince ba. Ya ce, “A’a, ga alamar damuwa a tare da ke.”

Ba ta sake cewa komai ba. Kan ta a sunkuye, ta ci gaba da share kwalla ta na jan hanci. Tausayin ta ya kama shi. Ya kara tambayar ta, “Ba kya da kudin sayen magungunan ne?”

Ta ajiye ma sa duk kudin da ke hannun ta a dunkule, ta amsa, “Duk abin da na mallaka ke nan.”

Ya dubi kudin ya dan yi murmushi, ya ce, “Ki koma gida ki ce a karo mi ki wasu, idan ya so sai ki dawo. Zan ajiye mi ki har sai lokacin.”

Hindu ta girgiza kan ta, “Ba ma da kowa a garin nan. Ba bu wanda mu ka sani.”  Kusan wa kan ta ta furta wa.

Ya dube ta da kyau, “Kun zo ne daga kauye yin jinya?”
“Ba ma da sauran dangi a ko ina.” Muryar ta cike da kunci.

Ya kura mata idanu, “To daga ina ki ke ne ‘yan mata?”

Ta dan daga kan ta ta kalle shi kadan. Saurayi ne da ba zai wuce shekaru ashirin da bakwai zuwa talatin ba idan ya yi nisa. Ta amsa, “Daga Pankshin mu ke, mu ‘yan gudun hijira ne.” A lokacin idanun ta su ka ciko fal da hawaye.

Ya dade ya na kallon ta, fuskar sa fayau. Ga alama ya na nazarin yarda ne da maganar ta ko a’a. Ya tambaye ta, “Wa ki ke jinya a nan?”

Ta goge hawayen da ya sauka kan kumatun ta, “Kaka ta ce.”

Ya dan yi shiru tare da jan numfashi, “Ya ya sunan ki?”
“Hindu.”

Ya saki murmushi, “Hindu, kin ce ba kya da kudi ko?” Ta gyada masa kai alamar eh. Ya ci gaba da cewa, “Zan ba ki wadan nan magungunan ki je da su, duk ranar da ki ka samu kudin sai ki kawo min.”

..... Tun Ran Zane Donde viven las historias. Descúbrelo ahora