Babi Na Talatin Da Tara

1.8K 160 102
                                    

01-09-Miladiyya
Zuwaira,

Hakika kin yi min halarci, kin nuna min kauna fiye da zatona sannan kin mallaka min zuciyar ki da kauna. Sai dai har ga Allah a lokacin da na hadu da Badiyya na ji na samu abin da na dade ina nema daga ‘ya mace. Ba wai ba na kaunar ki ba ne, amma na fi kaunar Badiyya.

Na san a lokacin da takardar nan za ta isa gare ki, za ki fahimci hakan. A gaskiya ba zan iya ci gaba da zama da ke ba ina tauye mi ki hakki. Shi ya sa na ga cewar gwara na sawwake mi ki in ya so idan kin samu mai kaunar ki, ki yi aure.

Don haka a yau, Lahadi, 01-09- Miladiyya, ni Muhammad Salihijo na sake ki Zuwaira diya ga marigayi Alhaji Sulaiman. Idan kin samu miji ki yi aure.

Zuwaira ta nisa tare da zukar numfashi a lokaci guda. Ta ce, “Alhamdulillah! Alhamdulillah! Allah Ka sa hakan shi ya fi alheri gare ni. Allah Ya hada kowa da rabon sa.”

Gambo kallon ta kawai take yi, ta na zubar da hawaye ita ma don tsananin tausayi da kaduwa. Ta san Zuwaira ta tafka wauta da ta ba da komai na ta ga Salihijo. Amma a gaskiya ba ta cancanci irin wannan zalunci da cin amanar da ya mata ba.

Ta saba yi mata ban baki kan halin da ta samu kan ta ciki. Amma a wannan lokaci kalamai suka ma ta karanci, ta gagara furta ko sauti. Ta kura wa Zuwaira idanu kirr, wacce ke kallon tagar dakin cikin zurfin tunani hawaye suna bin junan su a kan kumatun ta.

Gambo ta sake nisawa. A duk abubuwan da Zuwaira ta yi; wautar da ta tafka na mallaka ma sa kudaden ta ba tare da wata shaida ko rubutu ba, sannan ta sayi gidan da suka koma da sunan dan su Jamil, ba ta cancanci irin wannan cin amanar da tsohon mijin na ta ya mata ba. Don haka ba bu abin da wani zai iya yi ma ta. Ita ta bada makamin da a ka zalunce ta da shi.

Ba sai an kalli Zuwaira sau biyu ba a gane yanayin ba karamin jijjiga ta yayi ba. Ga danyen haihuwa ga kuma wannan. A lokacin ta rika jin da ta na da hali, da ta nemo Salihijo ta nuna ma sa ba za a zaluntar mace a zauna lafiya ba.

Zaman kuramen da suke ya dami Gambo matuka. Ta fi son Zuwaira ta furta wani abu, ko da ma zagi ne ko ma ta yi kuka. Don barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa.

“Zuwaira….”

Ta hadiye yawu da kyar sannan ta ce, “Kar ki ce komai Gambo, abin da ya faru, babu amfanin kuka a kan nonon da ya zube a kasa. Ni dai na gode wa Allah da Ya sa mu ka rabu ba tare da hakkin sa a kaina ba, kuma shi kan sa ya shaida cewa na rike shi tsakani da Allah.”

Zuwaira na magana cikin murya kasa-kasa mai jan hankali. Ta ci gaba da cewa, “Tsoro na daya ne Gambo, kar Allah Ya dauki raina ba tare da na nemi gafarar Hajiya ba. Ba na son na mutu da hakkin ‘yan uwana a kaina.”

Sai a lokacin hawaye suka zubo ma ta. Ta saka hannu ta share su, Ta yi nadamar sauraron Alhaji Bilya, wanda ya rika zuga ta, ya ingiza ta ta bata da ‘yan uwan ta. Shi kuma Salihijo ya kara ruruta wutar, wadda har ya sa ta karbi dukiyar ta ta danka ma sa a hannun sa.

Ta san duniya za ta dauka yin hakan wauta ce. Amma ta yi ne a dalilin so da kauna. Ta yi ne don na kara faranta ma sa rai, ya kara jin kaunar ta a zuciyar sa.

Ta sha jin a na cewa ba a yi iyaka wa mace hanyoyin da za ta bi don jan hankalin mijin ta zuwa gare ta ba. Babu abin da wasu ba za su iya yi ba kan hakan. Wasu matan malamai suke shiga, wasu kuma kissa da lakani iri iri.

A tunanin ta, don ta yi amfani da dukiyar ta ba aibu ba ne. A tun lokacin da ta san kauna na ke yin ta ga Salihijo. Ta ki amincewa da kowa, sannan ta yi kunnen uwar shegu wa wadan da suka ja mata kunne ko kashedi a kan hulda da shi ko auren sa saboda ganin da ta yi a wancan lokacin cewa duk wanda ya ke soyayya, ba zai yi bata ba. Sai ga shi nan, ta fadi a kasa, na zama tsummar goge kafa.

..... Tun Ran Zane Where stories live. Discover now