Babi Na Talatin Da Shida

1.7K 179 281
                                    

        *              *              *                   *                *             *
Hajiya Zuwaira ta saka kan motar ta cikin harabar makeken ginin da ya ke mazaunin ofishin mijinta. Bayan ta nemi wuri ta ajiye motar,sai ta fice,ta nufi ofishin sa gadan-gadan, ba ta ko amsa gaisuwar da sauran mutanen wurin ke mata. Ta hade girar sama da ta kasa. Ta na tafiya da kyar saboda kosasshen ciki.

Da isarta ofishin mijin ta ta bude kai tsaye ta shige ciki. A lokacin ya na rike da kan waya ya na magana. Ba ta tsaya saurara ma sa ba ta zuba wasu takardu a kan teburin da ke gaban sa ta tura ma sa, “Shin mene ne ma’anar wannan Salihijo?”

Salihijo ya dan yi wasu kalamai a waya, ya ajiye sannan ya dubi matar sa, “Ke me yasa wani lokaci ba kya da hankali ne? Ya ya za a yi ki shiga cikin ofis di na ba bu ko sallama sannan ki katse ni a waya?”

Hajiya Zuwaira ta yi kasake, a yayin da kalaman sa ke sauka kwanyar ta. Me take shirin ji? Kan ta abin ya juyo ke nan? Lallai ne, ma su magana sun ce yau da gobe, mai sa ango ya mari amarya.

Ta galla masa harara, fuskar ta na nuna karin fusata, “Abin da ke gabana ya fi wayar ka muhimmanci. Ya ya za a yi na zuba kudi naira miliyan biyar da hannuna satin da ya gabata, amma na je karbar kudi babu komai cikin account din da muka bude na hadin gwiwa?”

Salihijo ya dan yi murmushi, ya mike daga kan kujerar sa ta alfarma ya isa dab da ita. Yadin kaftani ya saka, dinkin kufta mai launin ruwan makuba, ya dofane jan dara a kan sa. Kamar ba ita ce ta saka ma sa hular da safiyar wannan rana ba, ta na neman izinin zuwa bankin daga gare shi.

Hakan ne ya kara bata ma ta rai, saboda ya san da zuwan ta bankin don karbar kudade amma kuma da zuwan ta a ka sanar da ita cewar an yashe komai kwanaki uku da suka gabata.

Ya rike hannayen ta tare da jan ta zuwa kujerun zaman baki da ke wangamemen ofishin sa ya zaunar da ita. Ya jefa mata kallon ita kadai ce sarauniyar zuciyar sa.

Ko da ya ga idanun ta na ci da wuta ne ya sa shi sake fadada murmushin sa, “Haba Zu-zu na, ke ma kin san ba zan taba yin wani abin da zai kawo cuta a gareki ba.” Muryar sa kasa kasa, ya na neman jan hankalin ta kan ta yarda da shi. “Kudaden da ki ka ajiye ni na kwashe su zuwa ma’ajiyata na bankin.”

Kallon ta ya koma irin na tuhuma, “Me ya sa?”

“Da farko dai kin cika kashe kudi da yawa kuma a karin banza, sannan ki na so ki mance da bashin da ke kanmu, wadan da mu ka karba daga bankuna don bunkasa wannan harka ta mu tun da dadewa. Idan na bar ki da kudin za ki yi facaka na da su kawai, ki dawo ki bar mu da jidali.”

Ta mike tsaye cikin fushi. Ita ba ta taba cin bashin banki ba, shi ne ya rika karba kudaden suna karyewa a kan sa. Ko da ya ga kudin ta ne ya nemi alfarmar ta bashi su yi kasuwancin hadin gwiwa don ya sauke nauyin da ke kan sa.

Tun da kayan Allah ai na Annabi ne, da kai da kaya kuwa duk mallakar wuya ne. Sai yanzu ta fara jin takaicin amince ma sa kan hakan.

“Ka mance cewa yarjejeniya ce mu ka yi da kai, kan cewa duk shekara za a rika ware min wasu kudaden kashin kaina?”

Salihijo ya ki sakin hannayen nata, ya ci gaba da magiya, “Zu-zu, jiya ba yau ba ne fa. Abubuwa sun fara canjawa. Ya kamata ki fi kowa sanin hakan.”

Ta kura ma sa idanu, ta na jin kamar ta kurma ihu har kololon muryar ta don duniya ta ji. Ta danne zuciyar ta, “Abubuwa sun canja, amma ba a aljihunka ba. Ina sane da yawan kudaden da ke fita daga account din ka kullum na kashewar ka. Sannan kuma a watannin da suka gabata tun farawar mu mun samu riba sosai a wannan kamfanin ta yadda za a iya biyan fiye da rabin basussukan da ka karba daga banki.”

Ya ja gwauron numfashi, shi ma ya mike sama, idanun san a nuna jin zafin sa bisa rashin yardar da ta fara nuna ma sa, “Ya kamata ki san cewar ni maigida ne. Nauyin da ke kaina ba ya kan ki. Zan fita waje tilas akwai abubuwan da sukan taso na yi su dole, wandan da ban shirya mu su ba. A zatona zan iya yin su ne ba tare da na sanar da ke ba.”

..... Tun Ran Zane Donde viven las historias. Descúbrelo ahora