Bai damu ba, ya ci gaba da raya wa kan sa. Babu wurin da zata je da ba zai sani ba. don haka ya ci gaba da hidimar sa, ya je ga mahaifiyar sa ya gaishe ta sannan ya je ofis.
Yammacin wannan rana ma da bai gan ta ba, bai bi ta kan ta ba, har sai da ya jera kwanaki biyu bas a ko da hada hanya tukunna abin ya fara damun sa, fiye da yadda yak e son nunawa.
Ya na kewar ta, yadda ta kan dunkule a kwance idan ta na barci, da kamshin ta idan ta na dakin, wanda baya tashi amma kuma ya na nan, sannan da gashin kan ta mai sheki da walwal idan ta taje ta baje shi a kan ta. Sau da dama ya kan ji tamkar ya zura hannun sa ta ciki ya tsefe tsawon su, ya ji ko yadda suke sheki ko za su taushi…
Ya salam! Wannan yarinya za ta saka shi cikin matsala idan bai yi hankali ba. A ce daga sumba daya kawai, ta saka shi jin abubuwa da dama, wadan da bai ma san suna nan ba? Sumba daya fa?
Ya na bukatar shayi. Ya dauki kofin shayin da ke gaban say a kora cikin makogwaron sa.
“Wannan shine kofi na uku da kake sha tun zama na a nan. Ka tabbata ba matsala?”
“Wannan mitin din ne ya dame ni Ibrahim.” Ya zuga karya. “Ba na son rasa wannan damar ne ta Mista Wilson.”
Ibrahim ya gyara zaman sa a kan kujerar da ke fuskantar dan uwan sa, sannan y ace, “Ka fa san kai a ka zaba, ko kuma in ce kamfanin ka. Komai ya na tafiya daidai, kawai hannu za a saka. Me zai saka tunani?”
Bai kalli Ibrahim ba, yayi kamar ayyuka sun ma sa yawa, “Ba zaka sani ba, you never know. Mutane su kan iya canjawa a ko yaushe.”
“Haka ne.” Ibrahim ya kishingida ya na kallon sa. Fari ne shi, ya na da tsawo, amma bai cika tsoka sosai ba. Mutum ne da yake da yawan murmushi da fara’a. Ba karamin abu ba ne ya ke saka shi fushi.
“Yaushe ka fara boye min abu Malik?”
Malik ya kalle shi wannan karon. Ba mamaki ko don jin yadda sautin muryar sa ta fito ne. Ya nuna damuwar sa a lokaci guda kuma da zolaya.
Me zai ce ma sa? Cewar mata ta ta bar kwana dakin kwananmu? Ko kuma ya damu da rashin ganin na ta? Amsar Ibrahim ta na daya daga cikin abubuwan da zuciyar sa ke kin nazarin su. Don haka sai ya kauce, kadan.
“Ban san me ye Alhaji Bilya yake shiryawa ba. Na samu labarin ya kai takarda Ma’aikatar Ma’adinai (Ministry of Solid minerals), tare da takardar kukan sa kaina.”
Ibrahim ya dan yi dariya, “Seriously? Hakan har damunka yayi? Ai ba wannan ne karon farko da hakan ke faruwa ba.”
Ya nisa, “Haka ne. Amma wannan karon ya kara karfi. Ya sayi bakin abokan hulda ta da yawa, kan su bayar da shaidar bogi ta harkar da mu ke da su ba kan doka ba ce. Ka kuwa san wannan gwamnatin ba zata kyale illegal minning ba.”
Ibrahim ya dan yi dariya, wanda ba hakan Malik ke bukata ba a wannan lokacin. “Look, wannan abu mai sauki ne. Tun da ka na da lasisi, kar wannan ya dame ka. Zan yi magana da Lawal Anchau, zamu sake kai ziyara wajen babban Yaya. Za mu ga abin da za mu iya yi ta hanyar dokar kasa.”
Malik ya gyada kan sa cikin amincewa. Bai taba shakka game da hazakar Ibrahm Danjuma, abokin sa kuma aminin sa sannan kuma lauyan sa.
“Hakan yayi kyau. Zan bar k aka yi abin kun a lauyoyi.”
Ibrahim yayi murmushi, “Sai dai na san ba wannan ne kadai ke damun ka ba.”
Ba tambaya ba ce, bayani ne, wanda ya san Ibrahim ba zai kyale shi ba cikin sauki.
“Ba wani abin da b azan iya warwarewa ba ne.”
“Batun matar ka fa? Shin ka taba zama da ita kun tattauna game da abubuwan da kake shakka?”
YOU ARE READING
..... Tun Ran Zane
General FictionNo 1 in General Fiction on 21 September. A lokaci guda duniya ta yi mata juyi mai zafin gaske. A lokacin rayuwa ta kawo mata zabi mai cike da hatsari da nadama. Ta yi watsi da duk wata fata, ta dakatar da duk wani mafarki....tun da dama ai mafar...