Assalamu alaikum da babbar murya.
Ya ya kuke? Yaya iyali? Yaya karatu? Yaya kujiba-kujiba?
Na san dai yanzu kun gano cewar ina kewaye kewayen baku hakuri ne. Ku yarda cewar abubuwa ne suka fi karfina ya sa kuka ji ni shiru.
Amma ga shi dai yau Allah Ya yi, na samu na kawo wannan. In shaa Allah gobe ma zan kara wani.
Na yi sadaukar da wannan shafi gare su masoyana, tare da godiya gare ku bisa soyayyar da kauna.
Na gode.
Xclusive_j ga naki nan😍😘. Idan kin karanta kya bani labari😂
Malik ya manne kan sa da jikin kujera kan san a kallon silin din ofishin sa, zuciyar sa ta na juya tunani daban daban. Fiye da awa guda ke nan babu abin da ya ke yi illa jan gwauron numfashi.
“Zuwaira ta dauko dala ba gammo. Ban zan yi mamaki ba idan da hannun mijin ta a ciki. Ya dade ya na saka ido a kan dukiyar ta. Yanzu kam yayi nasarar zuga ta, ta hau kai kuwa.”
Malik ya sake nisawa, “Ina fatan hakan ne Ibrahim. Don kwace goruba a hannun kuturu abu ne mai sauki. Ba zai dauke ni minti goma ba zan watsar da tsarin Salihijo. Amma a tunani na, wannan karon ko a ce da hannun sa, to kadan ne. Tilas mu bi a hankali don sanin girman al’amarin. Zuwaira ba ta sani ba, girman abin da ta shiga ya na da zurfi cike da hatsari.”
“Shi yasa bai dace ka biye mata ba.” Ibrahim ya jaddada.
Ya lumshe idanun sa, “Dole na yi yadda take so din, saboda Hajiya. Sannan na yi tunani tsawon daren jiya, cewa hakan shi ya fi. A ba ta hakkin ta kowa ya huta.”
“Ba hutu za ku yi ba Malik. Don nan ba da jimawa ba za ta koma gare ku cikin kuka da tashin hankali. Ku din ne za ku sake daukar wahalar.”
Malik ya gyara zaman sa, ya fuskanci Ibrahim da kyau, sannan ya nisa, “Na sani. Amma hakan zai kasance bayan ta koyi darasi mai tsaurin gaske.”
Fuskar Ibrahim cike da damuwa, “Kai ma darasin zai shafe ka matuka. Ina ka ke shirin samo makudan kudaden da za ka biya ta hakkin ta da su? Kudaden kamfanin da ke kasa wadan da a ke gudanar da harkokin yau da kullum ne. Mai tsoka mun saka shi a harkar da mu ka bude tare da su Mista Brown ne, sannan ga wannan harkar da mu ka samu na Abujan kwanan nan. So, ina kudin za su samu?”
Malik ya mike tsaye zuwa jikin tagar ofis din sa. Bangare guda ne, wanda ke rufe da gilas da kuma labule irin na ofis din da a ke sakawa kamar karare ne a daure a layi. Ya ja igiyar gefen da zai ba da damar bude wa da rufewa, ya ja suka zuge bude, sannan ya kura idanun sa waje.
“Ban sani ba.” Ya amsa cikin gaskiya. Sannan ya zuge labulayen suka rufu, ya koma ya sake zama, “Idan za a bani isasshen lokaci zan iya hada abin da ke hannuna na biya ta kawai.”
Ibrahim ya gwalo idanu, “Me kake cewa ne? Idan ka yi hakan, ta yaya za ka gudanar da kwangilar da mu ka samu na Abuja? Idan ka bari wani ne za a bawa, kuma babban kwangila ne Malik.”
Ya nade tafukan hannayen sa duka biyu ya dora bisa teburin da ke tsakanin sa da Ibrahim, sannan ya dora habar sa a kai, “Wane zabi ne gare ni, Ibrahim? Tun daren jiya na ke tunani na tsawon lokaci. Zuwaira ta shigo da abin da ya juya wa kowa kwakwalwar sa, ya jefa mu cikin bakon yanayi.”
“Ka yi kokarin fahimtar da kowa mana, halin da a ke ciki.”
Malik ya dan yi murmushin gefe, zuciyar sa na cikin halin da ya saba da hakan, ya ce, “Da ka ga yadda Alhaji karami ya yi ta fama jiya, da ba ka fadi hakan ba. Ya zare idon, har ma yayi yunkurin duka, amma Zuwairra ko gezau. A lokacin ne ma ta sanar da mu kan cewar ta yi wa Bilkisu mijin aure.”
ESTÁS LEYENDO
..... Tun Ran Zane
Ficción GeneralNo 1 in General Fiction on 21 September. A lokaci guda duniya ta yi mata juyi mai zafin gaske. A lokacin rayuwa ta kawo mata zabi mai cike da hatsari da nadama. Ta yi watsi da duk wata fata, ta dakatar da duk wani mafarki....tun da dama ai mafar...