Babi Na Tara

2.4K 205 125
                                    

“So, ya ya amarya?”
Abdulmalik ya nisa, “Kai wai ba zaka tambayi wani abu ba sai amarya? Tun shekaranjiya ka ke damuna.” Ya bata ran sa fiye da yadda ya dace. “Ka ga, Ibrahim ka rabu da ni na yi aiki na, ka ji ko?”

Ibrahim dan uwan sa ne, kuma aminin sa, shakiki. Tare suka tashi, tsarorin juna ne. Ya fashe da dariya, “Allah Ya shirye ka Malik. Waye ke zuwa wajen aiki kwanaki uku kacal da zuwa wajen amaryar sa?”

Amarya. Abin kamar ya ba wa Malik dariya. Bai ma fada ma sa cewar washe garin zuwan sa gidan ma sai da ya fita ofis, sannan ya bi ya fara aikin na sa ginin.

“Ba ka da matsalar komai ina ga alama.”

“Hmm, haka ne mutumina. Kai da a ka yi maka auren gata dole ka ce haka.”

Auren gata. Duniya za ta iya ganin auren sa a matsayin hakan. Amma shi ba hakan ya dauka ba. domin duk abin da a k ace Kawun sa ne a kai, to dole ya tsaya yayi nazari a kai tukunna.

Ba abu boyayye ba ne, Kawun sa ba son sa yake yi ba. shi ma kuma bai yarda da shi ba, don ya dade da sanin halayen da suka sa mahaifin sa ya kore shi daga kamfanin sa. Daga shi har mahaifin sa, ba sa kaunar ma su almundahana da rashawa, wanda hakan ne tsarin rayuwar Alhaji Bilya.

Suka yi sallama da Ibrahim, bayan sun dan tattauna kan wasu abubuwan. Bayan nan yayi kokarin yin aiki, amma sai fuskar matar da aka aura masa ta kutsa cikin kan sa. Kyakyawa ce fiye da zaton sa. Tsarin fuskar ta, tsarin siffar ta, maganar ta, murmushin ta…..

Malik ya yarfar da biron sa cikin takaici. A cikin kwanaki biyu da Allah Ya hada shi da wacce ke amsa suna matar sa…Hindu ko? Babu abin da yake iya tabukawa na a zo a gani, sai yawan tunanin ta.

Komai na ta a tsare ne kamar ita ta yi kanta. Ga shi kuma fuskar ta na nuna cewa ita mai gaskiya ce, kamar ba ta ma san ma’anar laifi ba.

Duk da cewa ya basar da ita tun dawowar sa, kuma ya na jin cewa zai iya ci gaba da hakan har zuwa lokacin da ya gamsu da komai game da ita, tunanin ta bai bar zuciyar sa ba. Duk danne-dannen komfutar da ya yi ta yi ba wai ya na bukata ba ne, sai don ya ci gaba da nuna mata halin ko-in-kula.

Ya na sane da idanun ta a kan sa. Idanun da suka hana ma sa jin sukuni har yanzu. Kallo ta rika zuba ma sa sai ka ce ita akuya ce shi kuma kura.

Duk da cewa ya kwanta ya yi kamar mai barci, idanun sa biyu, ya na kallon ta har barci ya dauke ta. Ita ce dai ba za ta gane hakan ba domin ita a haske ta ke, shi kuma ya kasance cikin duhu. Ko da dare ya yi sosai, garin juye-juye har ya fuskance ta.

Ya lura da yadda ta dunkule sanyin iyakwandishan din ya ratsa ta matuka. Ya so ya tashi ya rufe ta amma bai yi ba.  Sannan bai kashe sanyin ba. Ba ya son abin da zai sa shi ya matsa kusa da ita. Bai san tushen ta ba, bai ma san komai game da ita ba.

Ya mike tsaye, ya nufi tagar ofishin sa da ke hawa na shida a ginin NIDB, wurin da yake haya kafin ya kammalla ginin na sa, ya kalli waje. A matakin farko da ya ke shirin dauka, ya kunshi ba da dama don ya fahimci wace ce ita. In da hali ma, ya na son sanin cikakken tarihin kakannin ta, ba ma iyayen ta ba.

A cikin ran sa, ya na ganin ta na a wata manufa da auren sa, wanda wannan ne kuma ya dauki alwashin bincike ya tona. Shi ba yaro karami ba ne, balle a ce ya fada tarkon da Kawun sa ya dana, duk da cewar zai sara masa, saboda nemo mace kyakkyawa irin ta. Kyaun dan maciji, ya ayyana a ran sa.

Ya yanke shawarar ci gaba da nuna ma ta halin ko-in-kula. Ba abu ne mai yiwuwa ba a ce mace kamar ta, ta amince da auren wand aba ta taba haduwa da shi ba. Shin ta san ko shi mugu ne? Ko ma wane irin aiki ya ke yi?

Ya dai san cewa mace babu abin da ba za ta iya yi ba don kudi. To amma yawancin masu yin hakan sukan auri tsofi ne ma su nera, ba yara irin sa ba. Kuma fuskar ta sam ba taa nuna cewa ta na manufa boyayye. Duk da hakan, ba zai yarda da ita ba.

..... Tun Ran Zane Where stories live. Discover now