Babi Na Bakwai

2.2K 192 115
                                    

Assalamu alaikum.

I know, I have erred, terribly.  I am sorry for neglecting you all. It was unavoidable.

My younger sister got married yesterday, 5th August. I was the wedding planner. And being one isn't a joke.

But thank you for your patience and understanding.

Our story continues.  You are all awesome.

Did I mention that I love you?




A ranar Asabar, 22 ga watan Fabrairu, wanda ya zo daidai da uku ga Almuharram, a ka daura auren Hindu da Abdulmalik a kofar gidan su Auwal da misalin karfe sha daya da rabi na safe.

Mutanen unguwar ne hade da ‘yan uwa da abokan arziki su ka cika wajen daurin auren. ‘Yan uwan ango kadan ne suka zo.

Auwal ya zage yayi wa Hindu walimar bayan daurin auren na ta. Sannan duk da an ma ta kaya akwatina bakwai bai hana shi dinka ma ta kaya kalaa uku ba – hana-gori. Kayan ta saka su a lokacin hidimar.

Gaba daya a wannan lokaci kamar ba cikin hayyacin ta take ba. ta na da dalili, domin ta tuno da wata rana mai kama da wannan, amma sai dai waccan ta farinciki ce, wannan kuma ta rudani.

Shin me za ta tarar a wannan sabon gida, sabon yannayin da ta jefa kan ta ciki? Yay a zamanta cikin wannan gidan zai kasance bayan ta koma can da zama?

Ta lura cewar tun a ranar da kannen Malik mata biyu su ka je har gida suka dauke ta zuwa wajen mahaifiyar su, ta samu karbuwa matuka daga wajen ta. Haka su ma kannen na sa, ciki har da namiji guda daya, Mu’azzam.

Wadda ta ga za ta samu matsala da ita kuwa yayar sa ce, Hajiya Zuwaira. Ita ce babba duk gidan, ta na kuma auren wani Bafulatanin Yola ne.

A tun ranar da suka ziyarci gidan na ta, kallo daya ta yi wa Hindun, nan ma a wulakance, sannan ta shige cikin dakin ta kamar banza ta shanya a falon. Har dai kannen na ta suka gaji suka bi sawun ta. Nan ma ba ta fito ba. su din ne dai suka fito sannan suka ce ma ta su koma gida. Babu sallama daga wajen Zuwairan.

Ba sai an bayyana wa Hindu dalla dalla ba. Don daga yadda ta sa a kai mata ruwan sha cikin kofin roba, alhalin su Mashida a ka zuba mu su cikin abin zubawa na gilas hade da kofunan su, zuwa ga gayan tuwo da mai da gishirin da a ka sako ma ta cikin filet na roba duk sun nuna mata matsayin ta – matsiyaciya ‘yar talaka!

A yadda bayani ya zo mu su har gida bayan wannan ziyarar da ta kai ma ta, akwai wacce ta so a aura wa Malik. Sunan ta Badiyya, kanwar wata kawar ta ce.

A ire-iren ziyarar da Malik kan yi zuwa gida ta  hadasu hira. Har dai kamar abubuwa sun kan kama a dalilin yawan matsa ma sa da take yi kan ta. Hotuna iri da kala na Badiyyar duk ta aika ma sa har ma ta saka ta yi ma sa wasikar soyayya.

A gaskiya Badiyya ta kamu da son Abdulmalik, wasu ma sun ce fiye da yadda shi ke son ta ko nuna damuwa a kan ta. Saboda tsabar zumudi da yi wa kai, Hajiya Zuwaira har kaya ta kan saya da kudin ta ta ba wa Badiyya wai in ji Malik. Idan ya yi aika wa kannen sa ta rage a ciki ta kai wa Badiyya, duk dai wai in ji shi.

Ganin abu ya kan kama, mahaifin su ya nemi a tsayar da maganar aure a kan su. da kan sa ya samu kanin mahaifin Malik Alhaji Danjuma da zancen, shi kuma Alhajin ya yi alkawarin tuntunbar sa bayan ya gana da Hajiya Lauratu.

Ita kuma a lokacin Alhaji Bilya ya kai ma ta zancen Hindu. Ba ta bayar da kai wa Alhaji Danjuma ba, amma kuma ba ta ce a’a ba. ta shaida ma sa cewar za ta tuntubi Malik din da kan ta.

Hakan ya matukar bata wa Hajiya Zuwaira rai, ya kuma sa ta fuskanci Hajiyar da kan ta. Ta rasa abin da ta gani a jikin Hindu, ita da ba kowa ba ce, ba komai ba. Iyayen ta ma talakawan  kayau ne. Ba mamaki jahila ce.  A ce ita a ka aura wa Malik?

..... Tun Ran Zane Where stories live. Discover now